Abin da muka sani kan kwanton-ɓaunar da aka yi wa ƴansanda a Zamfara

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wasu ƴan bindiga sun kashe jami'an 'yan sanda takwas da aka tura domin samar da tsaro ga zaɓen fidda gwanin ɗan majalisar dattawan Zamfara ta Arewa a yankin arewaci maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalolin tsaro.

Ƴanbindigar sun yi motar da ƴansandan ke ciki kwanton ɓauna ne a ranar Litinin tare da buɗe musu wuta kamar yadda rahotonni suka ambato.

Harin na zuwa ne yayin da Najeriya, ƙasa mafi yawan jama'a a Afirka ke shirin gudanar da babban zaɓe a watan Janairu, a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarin tashe-tashen hankula daga ƙungiyoyin masu aikata laifuka a arewa maso yammaci da kuma tsakiyar Najeriya.

Waɗannan ƙungiyoyin na kai hare-hare a ƙauyuka, suna ƙaƙaba "haraji" kan manoma da masu haƙar ma'adanai, tare da yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa a yankunan karkara inda tasirin gwamnati ya yi rauni ko kuma babu shi gaba ɗaya.

A ina lamarin ya faru?

Harin ya faru ne a wajen ƙauyen Gidan Kano, a kan wata babbar hanyar karkara da ke haɗa jihar Zamfara da maƙwabciyarta, jihar Sokoto.

"Sun faɗa cikin kwanton ɓauna da 'yan bindiga suka shirya. 'Yan bindigar sun buɗe wa motar bas ɗin da 'yan sandan ke ciki wuta, suka kashe takwas daga cikinsu sannan suka tafi da sauran zuwa cikin daji," kamar yadda wani mazaunin ƙauyen Gidan Kano, Ibrahim Umar, ya shaida wa kamfanin diallancin labarai na AFP.

Sakataren ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, Adamu Kantu Gora, ya tabbatar wa AFP adadin waɗanda suka mutu, yana mai ƙara da cewa, "an kuma yi garkuwa da wasu biyar, yayin da wasu uku ke asibiti suna jinya saboda raunuka."

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya ce an turo jami'an ne daga jihar Sokoto domin samar da tsaro yayin zaɓen.

"An kai waɗanda abin ya shafa zuwa Sokoto," in ji shi, ba tare da bayar da ƙarin bayani ba.

'Lamarin ya faru ne a motar bas'

Bayanai sun nuna cewa jami'an ƴansandan na cikin motar bas, ba motar ƴansanda ba a lokacin da ƴanbindigar suka yi musu kwanton ɓauna.

Bidiyon da aka yaɗa bayan harin sun nuna motar bas ɗin mai ɗauke da sunan 'Zamfara State Transport', wadda aka fi sani da Bazamfara a yankin.

Wani abu da ya aza wasu ayoyin tambayoyin dalilin da ya sa ƴansandan suka zaɓi shiga motar bas maimakon motar ƴansanda.

Babu dai tabbaci ko ƴansandan ne zalla a motar ko har da fararen hula a lokacin aukuwar harin.

BBC ta tuntunɓi rundunar ƴansandan jihar amma ba ta mayar da martani ba.

Ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya

Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro daga ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi da ƴan bindiga da suka shafe 17 suka ƙaddamar da hare-hare a wurare da dama a ƙasar.

A gefe guda ga rikicin manoma da makiyaya da masu rajin ɓallewa da ke janyo janyo asarar rayuka da dukiyoyi a ƙasar.

Kodayake tashe-tashen hankulan Boko Haram sun ragu idan aka kwatanta da lokacin da suka kai kololuwa shekaru goma da suka gabata.

Amma kungiyar ACLED mai sa ido kan rikice-rikice da ke Amurka ta ce tashin hankali ya ƙaru tun daga shekarar 2024, sakamakon hare-haren ƴan bindiga da kuma na masu iƙirarin jihadi.

A wata hira da AFP a farkon wannan shekara, Sufeto Janar na Rundunar 'Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya ce za a gudanar da zaɓe cikin tsaro da kwanciyar hankali a faɗin ƙasar yayin babban zaɓen ranar 16 ga Janairu.

Ya kuma yi alƙawarin cewa ƴan Najeriya a arewacin ƙasar, waɗanda hare-haren 'yan bindiga da masu iƙirarin jihadi suka yi wa illa, "tabbas" za su samu damar kaɗa ƙuri'arsu.