Fitattun ƴan Najeriya da suka taɓa shiga ɗakin Ka'aba

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Hukumomin ƙasar Saudiyya sun buɗe wa shugaban Najeriya Bola Tinubu ɗakin Ka'aba, inda ya shiga ya gudanar da ibada.

Wannan na cikin wani ɓangare na aikin Umarah da shugaban ƙasar ya isa birnin Makka domin aiwatarwa.

A ranar 29 ga watan Oktoba ne Shugaba Tinubu da wasu muƙarrabansa suka isa ƙasar ta Saudiyya domin gudanar da aikin, wata tafiya da ta haifar da musayar kalamu tsakanin manyan ɓangarorin siyasa na ƙasar bayan da wasu ƴan adawa suka yi zargin cewa akwai wani dalilin daban game da tafiyar.

Sai dai tun bayan tafiyarsa, masu yaɗa labaran fadar shugaban Najeriya sun ci gaba da fitar da hotuna da bidiyo da ayyukan ibada da Tinubu ke yi a ƙasar ta Saudiyya.

A safiyar Litinin an wayi gari da hotuna da kuma bidiyon shugaban ƙasar lokacin da aka buɗe masa ɗakin Ka'aba.

Ka'aba ne wuri mafi tsarki a addinin Musulunci, wurin da ke karɓar baƙuncin miliyoyin Musulmai a kowace shekara waɗanda ke kai ziyara domin ayyukan ibada.

Shigar Tinubu ɗakin Ka'aba na nufin ya shiga jerin mashahuran ƴan Najeriya da aka taɓa buɗe wa ɗakin, wani lamari da ake yi wa kallon babbar karramawa daga masarautar Saudiyya.

Sai dai shigar da Bola Tinubu ya yi cikin ɗakin Ka'aba ta haifar da muhawara tsakanin al'ummar Najeriya, inda ake kallon cewa akwai mutane da dama da suka samu irin wannan karramawa.

Baya ga Tinubu, waɗanne mashahuran ƴan Najeriya ne suka samu damar shiga ɗakin na Ka'aba?

Tsohon shugaban hukumar alhazai ta Najeriya Abdullahi Mukhtar ya shaida wa BBC Hausa cewa akwai ƴan Najeriya da dama waɗanda suka samu damar shiga ɗakin Ka'aba.

"Akwai shugabanni da fitattun malamai da attajirai da jakadu na gwamnati waɗanda suka yi zama a Saudi Arabia da kuma shugabanni wadanda suka yi jagorancin aikin hajji waɗanda aka ba su dama bisa alfarmar sarki domin shiga ɗakin Ka'aba," in ji Abdullahi Mukhtar wanda shi ma ya taɓa shiga ɗakin na Ka'aba.

Sai dai yanzu ga jerin wasu daga cikin fitattun mutane da suka taɓa shiga ɗakin na Ka'aba daga Najeriya baya ga Shugaba Tinubu wanda ya shiga a baya-bayan nan.

Muhammadu Buhari

Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari na daga cikin mashahuran mutane na baya-bayan nan da suka shiga ɗakin na Ka'aba.

An buɗe wa Buhari ƙofar ɗakin Ka'aba har sau biyu. Na farko ranar 16 ga Nuwamban 1984 lokacin da yake mulkin soja.

Lokaci na biyu da aka taba buɗe masa shi ne a ranar Alhamis, 25 ga Fabrairu, 2016, lokacin da ya je ƙasar Saudiyya a hukumance.

A lokacin Buhari da tawagarsa sun samu damar yin sallar Juma'a a masallacin.

Shugaban na Najeriyar ya samu tarba ta musamman a wancan lokaci da ya kai ziyarar.

Sani Abacha

Daga cikin shugabannin Najeriya da suka shuga Ka'aba akwai Janar Sani Abacha, kamar yadda tsohon shugaban hukumar alhazai ta Najeriya Abdullahi Mukhtar ya tabbatar wa BBC.

Abacha ya mulki Najeriya ne daga shekarar 1993 zuwa 1998 inda a tsawon rayuwarsa ya sha zuwa Saudiyya domin gudanar da ibada.

Attahiru Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa ya samu shiga dakin Ka'aba a ranar 7 ga Fabrairun, 2017.

Ya samu damar ce bayan wata gayyata daga Babban limamin masallatan Harami, Sheikh Abdurrahman Sudais.

Lokacin ziyara cikin ɗakin na tsawon minti 15, Bafarawa ya yi sallar nafila, inda ya shiga tare da ɗansa Abubakar Bafarawa da kuma wasu malaman addini.

Rahotanni sun ce Bafarawa na daga cikin ƴan Najeriya waɗanda suka samu shiga ɗakin Ka'aba a lokuta da dama.

Malamai ƴan Najeriya da suka shiga Ka'aba

Baya ga shugabanni da wasu jagororin ƙasa, tsohon shugaban hukumar alhazai na Najeriya Abdullahi Mukhtar ya kuma ce akwai manyan malaman addini waɗanda su ma sun samu irin wannan "alfarmar".

"Daga cikin waɗanda zan iya tunawa a na nan kusa-kusa a cikin malamai akwai marigayi Malam Abubakar Mahmud Gumi," in ji Mukhtar.

A cikin littafinsa na 'Manufata', Gumi ya bayyana cewa ya shiga ɗakin Ka'aba tare da Firimiyan jihar Arewa Ahmadu Bello da kuma tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya Murtala Mohammed.

Wani babban malamin Musulunci a Najeriya Malam Abubakar Gumi ya shiga Ka'aba a lokuta da dama, kuma yana daga cikin "wadanda suka riƙa shiga Ka'aba akai-akai" a lokacin rayuwarsa.

A shekarar 1987 ne Sheikh Gumi ya lashe kyautar Sarki Faisal kan hidima ga addinin Muslunci.

A cewar Abdullahi Mukhtar sauran malaman Najeriya da suka samu damar shiga ɗakin Ka'aba sun haɗa da Sheikh Ahmed Lemu, sai kuma malamai waɗanda ke raka shugabanni, waɗanda su ma suke samun alfarmar shiga tare da shugabannin ƙasar.

Mene ne Ka'aba?

Ɗakin Ka'aba wanda ke a tsakiyar masallacin harami da ke birnin Makka shi ne wuri mafi tsarki ga Musulmi sannan kuma shi ne alƙiblar da Musulmin ke duba a lokacin da suke yin sallah.

Ziyarar ɗakin na Ka'aba aƙalla sau ɗaya a rayuwar Musulmi na daga cikin shika-shikan addinin Musulunci guda biyar, wani dalilin da ya sa suke yin dafifi domin gudanar da ibadar aikin Hajji.

Alƙaluma sun nuna cewa aƙalla a kowace shekara akwai mutum miliyan 13 zuwa 15 da ke ziyartar ɗakin, da suka haɗa da fiye da miliyan 11 da ke halartar Umra da kuma miliyan 2 zuwa 3 da ke zuwa aikin Hajji a kowace shekara.

A addinin Musulunci, Allah ya bayyana wurin a matsayin 'Ɗakin Farko' na bauta a duniya kamar yadda ya faɗi a cikin littafi mai girma wato Ƙur'ani.

"Haƙiƙa, ɗakin farko (na bauta) da aka samar ga ɗan'adam shi ne wanda ke Bakkah - mai albarka kuma shiriya ga duniya" (Al-Imran 3:96).

Malaman Musulunci da dama irin su Imam Baghwi sun fahimci cewa Ka'aba ce farkon gini, cewa ita ce wani gini da ya fara fitowa a kan ruwa lokacin da aka halicci sama da ƙasa shekaru 2000 kafin halittar duniya.

To amma wani ɓangare na malaman sun fi tafiya a kan cewar Ka'aba ce gini na farko na bauta a kan doron ƙasa da Annabi Adamu ya gina.

Bugu da ƙari akwai masu fahimtar cewa Mala'iku ne suka gina Ka'aba tun kafin Allah ya halicci Annabi Adamu.

Mene ne abin da ake la'akari da shi wajen buɗe wa mutum Ka'aba?

Shiga Ka'aba ba abu ne da ake bai wa kowa damar yin hakan ba, ko da kuwa mutum ne da ya je aikin hajji.

Akwai tsauraran matakai da ake da su wajen zaɓen waɗanda za su shiga ɗakin Ka'aba.

Saboda haka samun damar zuwa aikin Hajji ko Umara ba abu ba ne da zai iya bai wa mutum damar shiga ɗakin Ka'aba ba, sai dai mutum zai iya yin ibada a harabar masallacin harami da ke Makkah.

"Shi buɗe Ka'aba alfarma ce ta masarautar Saudiyya, kuma ba a iya buɗe ta sai da izinin sarki ko kuma yariman Saudiyya mai jiran gado.

"Babban abin da nake zaton ake la'akari shi ne irin ɗaukaka da Allah ya bai wa mutum a duniya, shi ya sa ake bai wa shugabannin ƙasashe da suka je aikin hajji ko umarah, amma ba kowa ba ne ake bai wa wannan damar.

"Alfarma ce wadda kuɗin mutum ko ikonsa ba sa iya yi masa, ko da an samu umarnin Sarki, dole ne sai da yarda ta ubangiji," a cewar Abdullahi Mukhtar.