Wane ne ya fara gina Ka'aba?

    • Marubuci, Usman MINJIBIR
    • Aiko rahoto daga, Abuja, Najeriya
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Ɗakin Ka'aba wanda ke a tsakiyar masallacin harami da ke birnin Makka shi ne wuri mafi tsarki ga Musulmi sannan kuma shi ne alƙiblar da Musulmin ke duba a lokacin da suke yin sallah.

Ziyarar ɗakin na Ka'aba aƙalla sau ɗaya a rayuwar Musulmi na daga cikin shika-shikan addinin Musulunci guda biyar, wani dalilin da ya sa suke yin dafifi domin gudanar da ibadar aikin Hajji.

Alƙaluma sun nuna cewa aƙalla a kowace shekara akwai mutum miliyan 13 zuwa 15 da ke ziyartar ɗakin, da suka haɗa da fiye da miliyan 11 da ke halartar Umra da kuma miliyan 2 zuwa 3 da ke zuwa aikin Hajji a kowace shekara.

Tuni dai miliyoyin alhazai daga sassan duniya suka fara yin bulaguro zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da ibadar aikin Hajji ta shekarar 2026.

Domin sanin asali da ma wanda ya fara gina wannan gini mai tsarki na Ka'aba ne ya sa BBC ta tuntuɓi Dakta Ibrahim Disina, Malamin addinin Musulunci a Najeriya wanda kuma ya yi karatun addini a ƙasar Saudiyya, wurin da Ka'abar take, inda malamin ya bai wa kafar wani shafi na musamman da aka rubuta kan tarihin ɗakin mai tsarki, domin rubuta wannan maƙala.

"Wannan bayanan duk gaskiya ne kuma tabbatattu ne, shafin Malamanmu ne daga ƙasar Qatar da Kuwait da Saudi," in ji Sheikh Disina.

Ka'aba shekaru 2000 kafin halittar duniya

A addinin Musulunci, Allah ya bayyana wurin a matsayin 'Ɗakin Farko' na bauta a duniya kamar yadda ya faɗi a cikin littafi mai girma wato Ƙur'ani.

"Haƙiƙa, ɗakin farko (na bauta) da aka samar ga ɗan'adam shi ne wanda ke Bakkah - mai albarka kuma shiriya ga duniya" (Al-Imran 3:96).

Malaman Musulunci da dama irin su Imam Baghwi sun fahimci cewa Ka'aba ce farkon gini, cewa ita ce wani gini da ya fara fitowa a kan ruwa lokacin da aka halicci sama da ƙasa shekaru 2000 kafin halittar duniya.

To amma wani ɓangare na malaman sun fi tafiya a kan cewar Ka'aba ce gini na farko na bauta a kan doron ƙasa da Annabi Adamu ya gina.

Bugu da ƙari akwai masu fahimtar cewa Mala'iku ne suka gina Ka'aba tun kafin Allah ya halicci Annabi Adamu.

Annabi Ibrahim AS

Malaman Musulunci sun yi ittifaƙin cewa daya daga cikin dalilan da Allah ubangiji ya nusar da Annabi Ibrahim zuwa Makka shi ne domin ya raya ginin Ka'aba da ya zagwanye.

Annabi Ibrahim tare da ɗansa Isma'il ne suka yi aikin sake gina ɗakin na Ka'aba, inda Isma'ila ke samar da duwatsu shi kuma Annabi Ibrahim yake ginawa kuma sun gina da tsawon da hannu ba zai iya kaiwa ba.

Bayan nan ne kuma Annabi Ibrahim ya nemi Isma'ila ya miƙa masa dutsen da zai iya takawa domin ya ƙarasa ginin - dutsen ne a yau ake kiran sa da 'Maqama Ibrahim', da ke kusa da Ka'aba.

Quraishawa

An samu ƙabilu da al'ummu da dama da suka riƙa kula da Ka'aba da suka haɗa da Amelekitawa da Jurhumawa da Khuza'awa da kuma Qurayshawa, inda suka rinƙa karɓeɓeniya wajen kula da wannan ɗaki.

Ƙabilar Larabawa ta Quraishawa ta yanke shawarar sake gina Ka'abar ta yadda malalar ruwa ba za ta sake zazaye ɗanba na ginin ba sakamakon ruwan sama.

Quraishawa sun kwashe shekaru biyar suna yin ginin tun kafin aiko Annabi Muhammad SAW a shekarar 605, inda suka ƙara tsayin ginin da kwas 9 ta yadda ginin ya zama mai kwas 18. Sun kuma toshe ƙofar ginin ta yamma inda suka bar ta gabas kawai domin hana shiga cikinsa.

A lokacin aikin na Quraishawa ne aka yi wa ginin rufi a karon farko. Sai dai kuma sakamakon rashin wadata ya sa dole suka bar wani ɓangare na ginin na asali da a yau ake kira 'Hijr Isma'il' a wajen Ka'abar.

Hadisai da dama sun nuna yadda Annabi Muhammad SAW yake raba gardama tsakanin ƙabilun Larabawa dangane da gini da kuma kula da Ka'aba.

Abdullahi bin Zubair 64 BH

A shekara ta 64 Bayan Hijra wato shekaru 31 bayan wafatin Annabi Muhammad, Abdullahi ibn Zubair ya rushe ginin Ka'abar har ƙasa inda ya sake sabon gini saboda ƙone ta da aka yi sakamakon harin da Yazid Ibn Mu'awiyya ya kai Makka.

A lokacin ne ya gina ta tare da sake shigar da wurin da Quraishawa ba su shigar ba wato 'Hijr Isma'il'. Ya kuma ƙara mata tsayi da zira'i 10 tare da ƙara mata kofofi guda biyu daga gabas da yamma a ƙasa da ginin.

Abdulmalik bin Marwan 73 BH

Bayan kashe Abdullahi bin Zubair da Abdul Malik bin Marwan ya yi tare da ƙwace iko da Makka, ya yi umarni da a sake gina Ka'aba kamar yadda take kafin Abdullahi bin Zubair ya gyara ta.

Hakan ya sa aka rushe kofar Ka'abar daga yamma, aka fito da 'Hijr Isma'il' waje, inda aka bar ƙofa ɗaya kawai wadda aka ɗaga ta sama. Sai dai kuma an bar tsayin ginin kamar yadda shi Abdullahi bin Zubair ya tsawaita da zira'i 10.

Masana tarihi sun ce ɗakin na Allah ya ci gaba da zama kamar yadda Abdulmalik bin Marwan ya bar shi har zuwa shekarun 1039 Bayan Hijra.

Sultan Murad Khan - 1039 BH

Masana tarihi sun ce Ka'aba ta fuskanci ambaliyar ruwa da ta lalata sassan ginin a ranar 19 ga watan Sha'aban na shekarar 1039 bayan Hijra, bayan da ambaliyar ta yi ɓarna a masallacin na Makka da ma ɗakin na Ka'aba.

Ruwan ya shiga ɗakin kuma ya lalata katangar arewaci da ta gabashi da kuma ta yammaci da kuma matattakalar da ke kai wa ga rufin ɗakin.

Hakan ne ya sa masu bayar da fatawa a lokacin suka amince da a rushe sassan da suka lalace domin sake ginawa wanda Sultan Murad Khan wanda shi ne Sarkin daular Usmaniyya ya kammala ginawa a ranar 2 ga watan Dhul al-Hijjah na shekarar 1040 Bayan Hijra.

Muhammad Ali Pasha - 1239 AH

A ƙarshen shekarun 1939 bayan hijra ne gwamnan ƙasar Misra mai suna Muhammad Ali Pasha ya bayar da umarnin tsaftace kewayen Ka'abar domin kwashe dukkan laka da yashi da ke damɓare sakamakon ambaliyar ruwa da aka fuskanta a lokacin.

Bayan nan ne kuma aka yi wa ginin ƴan gyare-gyare da suka fito masa da ƙimarsa.

Abdulaziz bin Abdul Rahman Al Saud - 1924

Sarkin Saudiyya na farko Abdul'aziz bin Abdul Rahman Al Saud shi ne wanda ya sake ƙawata ginin Ka'aba da suka hada da sake ƙofofin ginin bayan da ya shiga ɗakin.

Kuma ana ganin wannan ne babban aikin da aka yi na zamani a masallacin Makka da Ka'aba tun bayan da aka kafa masarautar Saudiyya a 1924.

A lokacin an gyara sama da ƙasan Ka'abar. An kuma gyara dukkan katangun ɗakin tare da ƙawata bulon da ke jikin katangun da ƙafar bene zuwa saman ɗakin.

Sarki Fahad - 1997

A zamanin Sarkin Saudiyya Fahad ne Ka'aba ta samu gyaran da har yau ake gani daga wajenta har cikinta da suka hada da rufi da turakunta uku da ƙofofin ciki da daɓe da kuma ƙafar benen.

Sauran gyare-gyaren sun haɗa da indararo da bangon Hijr Isma'il.

Sunaye 11 da ake kiran Ka'aba da su

Shafin na musamman kan tarihin Ka'aba a Musulunci ya bayyana cewa ɗakin Ka'aba na da sunaye masu dama kamar yadda yake a kundin tarihi na Al-Azraqi, kamar haka:

  • Kaaba
  • Bakkah
  • Al-Bayt al-Haram
  • Al-Bayt al-Atiq
  • Al-Baniyyah
  • Ad-Duwwar
  • Al-Masjid al-Haram
  • Qadis
  • Nadir
  • Al-Qariyah
  • al-Qadimah