Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Juma'a 15/05/2026

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, da Usman Minjibir da Aisha Babangida

  1. Kamfanin Honda ya tafka asara karon farko cikin shekara 70

    Kamfanin ƙera motoci, Honda ya tafka asara karon farko a shekara cikin shekaru 70 saboda hannun jarinsa na motoci masu amfani da lantarki ba su haifar da riba ba.

    Ba a cika neman motoci masu amfani da lantarki ba kamar yadda kamfanin ya yi hasashe inda kamfanin na Honda ya ce ya yi asarar dala biliyan 2.68 zuwa Maris ɗin 2026.

    Kamfanin ya ce zai soke wasu daga cikin muradansa na samar da motocin lantarki kuma zai nemi wasu kayan aiki daga China inda farashinsu suka fi sauƙi.

    Kamfanin ya ce tsare-tsaren Amurka suna da hannu wajen asarar da ya tafka ciki har da ƙaƙaba haraji.

    Honda, wanda ya shiga kasuwar hannun jari a 1957, ya bunƙasa cikin shekaru inda ya zama kamfanin motoci na biyu mafi girma a Japan.

  2. Jadawalin manyan jam'iyyun siyasar Najeriya na zaɓen fidda gwani

    Manyan jam'iyyu huɗu a Najeriya sun fitar da jadawalin da suke shirin bi wajen gudanar da zaɓen fitar da gwani kafin babban zaɓen 2027.

    Sabuwar jam'iyyar NDC ta fara bayyana shirinta na tantance da kuma zaɓar wanda zai wakilce ta a zaɓen 2027.

    A baya, jam'iyya mai mulki ta APC ta riga ta fitar da sabon jadawali da tsarin ayyukanta, inda ta yi gyare-gyare kan lokacin tantance 'yan takara da zaɓen fitar da gwani, da kuma sauraron ƙorafe-ƙorafe da sauran matakan cikin gida na jam'iyya.

    A cikin sanarwar, jam'iyyun sun kuma bayyana bayanan lambar asusun ajiya ta banki da masu sha'awar sayen fom ɗin tsayawa takara za su biya kuɗi domin samun fom ɗin shiga takara.

    Sun ce dalilin gyaran jadawalin ya haɗa da bukatar daidaitawa da hutun ranar ma'aikata ta duniya, wanda ya shafi lokacin gudanar da wasu ayyukan cikin tsarin jam'iyya

    A yayin da jam'iyyun adawa ke fuskantar rikice-rikicen kotu a 'yan kwanakin nan, jam'iyyar ADC ita ma ta fitar da jadawalin gudanar da zaɓen fidda gwani na shekarar nan.

    A cikin wata sanarwa da Kakakin Jam'iyyar na Kasa, Bolaji Abdullahi ya fitar, ADC ta ce jadawalin na su ya nuna ƙudirin jam'iyyar na tabbatar da dimokuradiyya ta cikin gida da bin doka da oda, da kuma cikakken bin ƙa'idojin hukumar zaɓe.

    Dangane da batun ko jam'iyyar za ta iya tsayar da 'yan takara a zaɓen 2027, ADC ta ce babu wani ɓangare na doka da ke hana ta shiga zaɓen. Ta kuma ƙara da cewa duk wani zance da ke nuna akasin haka "yunƙuri ne na ruɗa jama'a da kuma rage ƙwarin gwiwar 'ya'yan jam'iyyar."

  3. EFCC ta maka Blessing CEO a kotu kan zargin karɓar kuɗi ta hanyar ƙarya

    Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta'annati ta gurfanar da fitacciyar mai amfani da shafukan sada zumunta, Okoro Blessing Nkiruka da aka fi sani da Blessing CEO a gaban babbar kotun tarayya da ke Ikoyi a jihar Legas kan zargin badaƙalar naira miliyan 36.

    An gurfanar da Nkiruka kan tuhume-tuhume biyu da suka shafi zargin yin ƙaryar rashin lafiya don samun kuɗi da sace naira miliyan 36.

    A farkon zaman, lauyan wadda ake ƙara P.I Nwafor ya shaida wa kotu cewa wadda yake karewa ta mayar wa wanda ya shigar da ƙorafin kuɗinsa.

    Blessing ta musanta aikata tuhume-tuhumen.

    Lauyan wadda ake ƙara ya shaida cewa ana ƙoƙarin nema mata beli inda ya nemi kotu a tsare Blessing a komar EFCC zuwa lokacin da za a cika ƙa'idojin ba da ita beli.

    Alƙali Dipeolu ya amince da buƙatar tare da ba da umarnin a tsare ta a hannun EFCC.

    An ɗage zaman zuwa 5 ga watan Yuni domin ci gaba da shari'a.

  4. Wane ne ya fara gina Ka'aba?

    Ɗakin Ka'aba wanda ke a tsakiyar masallacin harami da ke birnin Makka shi ne wuri mafi tsarki ga Musulmi sannan kuma shi ne alƙiblar da Musulmin ke duba a lokacin da suke yin sallah.

    Ziyarar ɗakin na Ka'aba aƙalla sau ɗaya a rayuwar Musulmi na daga cikin shika-shikan addinin Musulunci guda biyar, wani dalilin da ya sa suke yin dafifi domin gudanar da ibadar aikin Hajji.

    Alƙaluma sun nuna cewa aƙalla a kowace shekara akwai mutum miliyan 13 zuwa 15 da ke ziyartar ɗakin, da suka haɗa da fiye da miliyan 11 da ke halartar Umra da kuma miliyan 2 zuwa 3 da ke zuwa aikin Hajji a kowace shekara.

    Tuni dai miliyoyin alhazai daga sassan duniya suka fara yin bulaguro zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da ibadar aikin Hajji ta shekarar 2026.

  5. Sojoji sun kashe mayaƙan Lakurawa biyu a Sokoto

    Sojoji da ke ƙarƙashin rundunar Fansan Yamma sun kashe wasu da ake zargi mayaƙan Lakurawa ne tare da ƙwato makamai yayin wani samamen yaƙi da ta'addanci da aka kai a ƙaramar hukumar Tangaza da ke jihar Sokoto.

    Sojojin sun kuma gano dabbobi 62 da ƴan bindigar suka sace a wani samame na daban da suka kai jihar Katsina.

    Cikin wata sanarwa da muƙaddashin mataimakin daraktan yaɗa labarai na rundunar Fansan Yamma, Lieutenant Colonel Olaniyi Osoba.

    A cewar sanarwar, samamen da aka kai ya faru ne bayan kiran gaggawa da aka yi game da wani yunƙurin hari kan ofishin hukumar shige da fice da ke ƙauyen Ruwa Wiri a Tangaza.

    Osoba ya ce sojoji sun isa wajen ba tare da ɓata lokaci ba inda suka fafata da maharan.

  6. Italiyawa biyar sun mutu sanadin wasan ninƙaya

    Ƴan Italiya biyar sun mutu a wani wasan ninƙaya a Maldives, kamar yadda ma'aiatar harkokin waje da ke Roma ta bayyana.

    Ana tunanin sun mutu ne a ƙoƙarinsu na shiga wani kogon dutse mai zurfin mita 50, in ji ma'aikatar.

    Huɗu daga cikin su, tawaga ce ta jami'ar Genoa har da wata farfrsa Monica Montefalcone da ƴarta da wasu masu bincike.

    Rundunar sojin Maldives ta ce an gano gawa ɗaya a cikin kogon kusan mita 60 ƙarƙashin ruwa sannan ana tunanin sauran huɗun ma suna wajen.

    A ranar Alhamis ne masu waan ninƙayar suka shiga ruwa kamar yadda kafafen yaɗa labarai na suka bayyana.

  7. Kenya ta ƙara farashin man fetur saboda yaƙin Iran

    Kenya ta ƙara farashin man fetur zuwa matakin da bai taɓa kai wa ba sakamakon tashin farashin mai a duniya da ke da alaƙa da yaƙin Iran.

    Farashin dizel ya ƙaru ɓagatatan da dala 0.35 sannan farashin mai ya ƙaru da dala 0.12 abin da ya janyo dogayen layuka a gidajen mai da dama musamman a Nairobi, babban birnin ƙasar.

    A sanarwar da aka fitar ranar Alhamis, hukumar kula da makamashi ta ƙasar ta ce an yi ƙarin ne saboda yadda farashin man fetur ya tashi a kasuwar duniya.

    Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai sun ce sa'oi bayan sanarwar, masu ababen hawa suka ƙara kuɗin mota a Kenya.

    Mutanen Kenya sun bayyana damuwa a shafukan sada zumunta saboda fargabar da suke cewa tashin farashin man zai shafi ɓangaren sufuri, wani abu da ka iya janyo hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.

    Sabon farashin da ya soma aiki yau, zai ci gaba da kasancewa har 14 ga watan Yuni.

  8. An kori ƴansanda biyar saboda zargin hannu a garkuwa da mutane a Rivers

    Rundunar ƴansanda a Najeriya ta kori jami'anta biyar masu muƙamin speta da ke aiki a Patakwal da ke jihar Rivers saboda zarginsu da hannu a ayyukan garkuwa da mutane da fashi da karɓar kuɗi a hannun mutane da kuma cin haci.

    Jami'in yaɗa labarai na rundunar ƴansanda, DCP Anthony Okon Placid, cikin sanarwar da ya wallafa a shafin rundunar ya ce ƴansandan da aka kora sun haɗa da Speta John Okoi da Speta Eyibo Asuquo da Speta Udo Ndipmong da Speta Bright Nwachukwu da Speta Anele Ikechukwu.

    Placid ya ce akwai wasu ƴansanda shida daga rundunar da aka samu da hannu wajen haɗa baki da fashi da garkuwa da mutane bayan zargin an sace wani a Patakwal a Fabarairun 2026 tare da cire sama da naira miliyan bakwai daga asusun wanda suka yi garkuwa da shi.

    Ya ce za a gabatar da ƴansanda uku da aka kama a gaban kotu yayin da jami'an tsaro suka bazama neman wasu uku da suka tsere.

  9. Ukraine ta kai harin jirgi mara matuƙi kan Rasha

    Ukraine ta kai hari da jiragen yaƙi mara matuƙa a birnin Ryazan na ƙasar Rasha.

    Kafofin yaɗa labaran Ukraine sun ce wuraren da aka kai harin sun haɗa da matatar mai, inda gobara ta tashi cikin dare.

    Gwamnan yankin ya ce mutum uku ne aka kashe.

    Harin na Ukraine dai ya biyo bayan harin da jiragen saman Rasha suka kai kan Kyiv a jiya Alhamis, inda aka kashe aƙalla mutum ashirin da ɗaya.

    Wannan dai na daga cikin abin da jami'an Ukraine suka ce shi ne hari mafi girma da suka fuskanta ta sama tun da Rasha ta fara mamayar ƙasarsu.

  10. Mutum 65 sun mutu bayan ɓarkewar cutar Ebola a Congo

    An tabbatar da ɓarkewar cutar Ebola a Lardin Ituri na Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo inda hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Afirka ta ce an samu rahoton mutum 246 da ake zargin sun kamu, wasu 65 kuma sun mutu, galibi a Mongwalu da Rwampara.

    Duka garuruwan sun dogara ne kan zinare a matsayin kafar samun kuɗaɗen shigarsu.

    Gwaje-gwajen da aka yi a Kinshasa su gano mutum 13 cikin 20 ɗauke da ƙwayar cutar sannan kuma ana ci gaba da nazarin waɗanda ake zargin suna ɗauke da cutar.

    Mutane huɗu da suka mutu na cikin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar.

    Har yanzu gwamnatin ƙasar ba ta ayyana ɓullar cutar a matsayin ɓarkewa ba sai dai ana sa ran hukumomi su yi taron manema labarai nan gaba.

  11. APC ta ɗage zaɓen fitar da gwani na ƴanmajalisar wakilai

    Jam'iyya mai mulki a Najeriya, APC ta ɗage zaɓen fitar da ƴantakara na ƴanmajalisar wakilai da aka tsara yi a yau zuwa gobe Asabar.

    Wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na jam'iyyar, Felix Morka, ya fitar, ta ce sauyin bai shafi zaɓen fitar da gwani da sanatoci da majalisun dokoki na jihohi da na gwamnoni da kuma shugaban ƙasa ba.

    Ya ce a yanzu zaɓen fitar da gwani na sanatoci zai gudana ranar Litinin 18 ga watan Mayu, na ƴanmajalisar jiha kuma za a yi shi a ranar Laraba 20 ga watan Mayu sai na gwamnoni da aka tsara yi ranar Alhamis 21 ga watan Mayu.

    Sanarwar ta ƙara da cewa zaɓen fitar da ɗantakarar shugaban ƙasa a jam'iyyar zai gudana kamar yadda aka tsara wato a ranar 23 ga watan Mayu sai dai Morka bai faɗi dalilin ɗagewar ba.

    Ya ce matakin ya shafi tsarin jigila musamman ga jami'an da aka tsara za su je sa ido a zaɓen.

  12. Trump ya bar China bayan ƙarƙare tattaunawa da Xi Jinping a Beijing

    Shugaba Donald Trump na Amurka ya bar ƙasar China bayan tattaunawar da ya yi da takwaransa Xi Jinping a Beijing kan yauƙaƙa alaƙa tsakanin ƙasashen masu ƙarfin tattalin arziki.

    Mista Trump ya ce sun ƙulla yarjeniyoyin kasuwanci masu ban sha'awa, kodayake bai bayar da cikakken bayani ba.

    Wakilin BBC ya ce yayin wata ganawa da suka yi a babban ɗakin taron jama'a shugaba Xi ya gargaɗi Donald Trump kan cewa batun Taiwan na iya janyo matsala tsakanin ƙasashen biyu idan har ba a tafiyar da shi yadda ya kamata ba.

    Tun da farko Mista Trump ya shaida wa gidan talabijin na Fox News cewa China ta amince ta sayi mai daga Amurka, za ta kuma daina bai wa Iran kayan aikin soji.

    Kan batun yaƙin na Iran dai, wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen China ya shaida wa manema labarai cewa tun farko bai kamata ma a fara yaƙin ba kuma yanzu babu dalilin ci gaba da shi.

  13. Barka da Juma'a

    Shafin Kai Tsaye na BBC Hausa na yi wa ɗumbin masu kasancewa da mu barka da wannan lokaci.

    Da fatan an wayi gari cikin ƙoshin lafiya. Kamar kodayaushe, a yau ma za mu ci gaba da kawo maku rahotanni na abubuwan da suka shafi yaƙin Iran da labaran da suka danganci Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labarai da ma kallon bidiyo.