Aston Villa ta janye barazanar da ta yi na ɗaukar matakin shari'a a kan mai sharhin Sky Sports, Jamie Carragher.
A ranar Juma'a, Villa ta bayyana cewa za ta ɗauki matakin shari'a kan tsohon mai tsaron bayan tawagar Ingila, saboda abin da ta bayyana a matsayin "kalamai da ba za ta amince da su ba" da Carragher ya yi a shirin tattaunawa ta Stick to Football.
Tsohon dan wasan Liverpool ɗin ya danganta kocin Villa, Unai Emery da cewar watakila shi ne zai maye gurbin Michal Carrick a Manchester United, sannan ya shaida wa magoya bayan Villa da su "yi shiru" bayan da suka soki kalamansa.
Carragher ya nemi afuwa a ranar Asabar saboda amfani da kalaman da ya bayyana a matsayin "kuskure kuma ba su dace ba", yana mai cewa ya yi su ne cikin barkwanci.
Ko da yake Villa ba ta kai ƙarar Carragher kotu ba, yanzu ta daina barazanar yin hakan bayan afuwar da ya bayar.
Tun bayan da ya karɓi ragamar Villa a shekarar 2022, Emery ya sauya alkiblar kungiyar sosai. Kocin ɗan asalin Sifaniya ya taimaka wa Villa ta kauce daga matakin fafutukar kaucewa daga faɗuwa zuwa ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke buga Champions League akai-akai, sannan ya jagorance ta zuwa lashe Europa League a 2026.