An ceto wasu mutum takwas da aka yi garkuwa da su a Kaduna
Jami'an tsaro sun tabbatar da ceto wata mata mai juna biyu, Jamila Muhammad da wasu mutum bakwai da 'yan bindiga suka sace a jihar Kaduna bayan shafe makonni a hannun masu garkuwar.
An kuɓutar da mutanen ne a wani samame na haɗin gwiwa da ya haɗa da Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS da rundunar ƴansandan Najeriya da sojoji tare kuma da haɗin gwiwar gwamnatin Kaduna.
Kwamishinan ƴansanda a jihar, Muhammad Rabiu shi ya tabbatar da ceto mutanen a wani taron manema labarai a hedkwatar DSS da ke Kaduna.
Rabiu ya ce samamen na cikin wani ɓangare na ƙoƙari da jami'an tsaro ke yi wajen kakkaɓe ayyukan masu garkuwa a anguwar Millenium City da ƙewaye.
Ya ce anguwar ta fuskanci ayyukan masu garkuwa a baya-bayan nan, abin da ya saka fargaba tsakanin mazauna yankin da kuma masu ruwa da tsaki kan tsaron lafiyar mutane.
An sace Jamila mai shekara 27 ranar 6 ga Oktoba lokacin da ƴanbindiga suka kai hari anguwar Millenium City da ke karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna, inda kuma a lokacin ne aka yi garkuwa da Ahmad Zakka da matarsa da kuma ƴarsu ƴar kimanin watanni shida.
Sai dai an saki Zakka da matarsa ranar 15 ga Oktoba, kwanaki kaɗan bayan bidiyonsu ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda aka ci gaba da riƙe Jamila har sai da jami'an tsaro suka kai farmaki.
Rahotanni sun bayyana cewa ta yi ɓarin cikinta lokacin da take hannun ƴanbindigar.