Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Abinda aka yi a Gombe ya saɓawa dokar zaɓe'
Tsohon Ministan Sadarwar Najeriya kana mai neman tsayawa takarar gwamna a jihar Gombe a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC, Farfesa Isa Ali Pantami, ya sha alwashin ɗaukar duk wani mataki da ke bisa doka wajen ƙalubalantar yadda aka fitar da ɗan takarar gwamnan jihar na zaɓen baɗi, da ya ce ya saba wa ƙa'ida.
Wannan ya biyo bayan da gwamnan jihar ya sanar da Dr. Jamilu Isiyaku a zaman ɗan takarar gwamnan jam'iyyar na maslaha.
Sakamakon ƙorafinsa dai Jam'iyyar ta APC a jihar Gomben ta ce za ta iya sake zaɓen ta hanyar ƴar tinke,
Sai dai Farfesa Pantami ya shaidawa BBC cewa a shirye yake ya tunkari zaɓen fitar gwanin ta hanyar ƴar tinke:
''Gaskiya ta Allah, a babin adalci ba consensus aka yi a jihar Gombe ba, in an ce consensus shi ne kowa da kowa ya amince'' in ji shi.
A cewarsa akwai abubuwa da dama da ake buƙata a kiyayesu idan tsarin maslaha ake son ayi amfani da shi.
''Na farko duk wani wanda ya ke cikin harkar, sai ya amince da cewa da ƙashin ƙansa ya amince da abinda aka yi a wurin, na biyu ya zama dukkan wani mutum ko da ba ya wurin sai an turo da wani wakilinsa da zai wakilce shi''
''Na uku akwai yarjejeniyar da ake cimmawa a kan abinda aka yi ya dace da doka kuma dukkanin guda ukun nan ba bu guda ɗaya da aka cika bare ya zama an samu maslaha''
Tsohon ministan ya yi iƙirarin cewa abinda aka yi ya saɓawa dokar zaɓe ta 2026 kuma sau ɗaya gwamnan jihar Gombe ya taɓa zama da masu anniyar tsayawa takarar gwamna
''Sau ɗaya aka taɓa zama da mu, aka tara mu cewa wani tsari mu ka ɗauka, sai gwamna Muhammed Inuwa Yahaya ya ce ya yi alƙawarin zai yi adalci in zai yiwu a yi amfani da tsarin maslaha''
''Na biyu in bai yiwu ba sai ayi zaɓen ƴar tinke kuma a tsarin masalaha sai aka ce a je a fitar da ƙa'idojin da za a bi kuma ba bu wanda ya ga ƙa'idojin a cikinmu''
''Idan za ka yi consensus sai a nemi kwamiti mai zaman kansa wanda ba su da wani karkata ga wani ɗan takara sai a basu wuka da nama''
Dr Pantami ya kuma ce akwai waɗanda aka aika wa goron gayyata yayin da akwai wasu da ba a gayyacesu ba
''An ba mu notice ɗan takaitacce ne, na ƙasa da awa 20, a lokacin da mu ka gani mun kama hanyar tafiya, tafiyar ba ta yiwu ba, ga saƙo a rubuce cewa in dai zaman da za a yi, ci gaba ne na zaman da aka fara ƙwaya ɗaya da aka yi na consensus mu na roƙon a ƙara mana lokaci don nu halarci zaman mu tabbatar an yi''
''Aka mai da zaman Lahadi , ba bu wanda ya gaya mana za a yanke hukunci ranar Lahadi''
Ɗan takarar ya sha alwashin ɗaukar duk wani mataki da ke bisa doka wajen ƙalubalantar yadda aka fitar da ɗan takarar gwamnan jihar na zaɓen baɗi, da ya ce ya saɓa wa ƙa'ida.
''Ai waɗanda su ke tsoron zaɓen ƴar tinke a Najeriya duk suna tsoro ne saboda ba su da magoya baya a wurin talakawa amma duk wanda ya shirya, ya san talaka na tare da shi, da ke da katin jam'iyya ai ba ya jin tsoro ya shiga''
Abinda muke buƙata a yi shi ne a yi adalci, in an yi zalunci har ga Allah za mu yaƙi zalunci, za ka ga yaƙin da ba ka taɓa ganin irinsa na zalunci a Najeriya ba
Ya dai ce yaƙin na zalunci za a yi shi ne bisa la'akari da tanadin da dokar ƙasa ta shimfida.