Dalilan da suka sa PDP ta naɗa shugabanin riƙon ƙwarya

Lokacin karatu: Minti 2

Ɓangaren Kwamitin Zartarwa na PDP na ƙasa wanda ke samun goyon bayan Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da naɗin kwamitin riƙon ƙwarya mai mambobi 13, ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki, a matsayin shugaba.

An ɗauki wannan mataki ne a taron kwamitin da aka yi a Abuja, bayan wani hukuncin da kotu ta yanke na rushe babban taron jama'iyyar na kasa da aka gudanar a birnin Ibadan kwanakin baya, abun da ya rushe shugabancin jama'iyyar ƙarƙashin Tanimu Turakin.

Yayin wani zama da ƴan kwamitin zartarwar jama'iyyar suka gudanar a Abuja, sun ce ɗaukar wannan mataki ya zama dole don kaucewa ganin jama'iyyar ta PDP ta zauna babu shugabanci.

Sanata Umar Ibrahim Tsauri, ɗan kwamitin amintattu na jama'iyyar ta PDP ya shaidawa BBC cewa a tasu fahimtar, hukuncin kotun ƙolin bai ba wa kowanne ɓangare ciki har da na Wike nasara ba.

''Kotun ƙoli ta ce babban taron da mu ka yi wanda ya zaɓi Tanimu Turaki haramttace ne, watau Tanimu Turaki da waɗanda aka zaɓesu da shi, ba za su riƙe muƙami ba'' In ji shi.

Sanatan ya kuma ce a fahimtar su kotun ƙolin ta kuma tabbatar da korar da aka yi wa sakataren Jam'iyya, Samuel Anyanwu

''Kotun ta kuma ce korar da aka yi wa sakataren jam'iyya da mai ba jam'iyya shawara kan harkokin sharia ta tabbata''

Sanatan ya ce tsarin mulkin jam'iyyar PDP ya ce idan an sami matsayi irin wannan sai kwamitin amintattu ya ɗauki jamiyya

To sai dai a cewar Muhammad Jungudo, kakakin jama'iyyar ta PDP ɓangaren Wike, matakin da ɗayan ɓangaren suka ɗauka na jeka na yi ka ne kawai:

''Waɗannan mutane a kwanakin baya lokacin da jam'iyyar PDP ta kafa kwamiti na riƙon ƙwarya sun fito su na suka suna cewa kundin tsarin mulkin jam'iyya bai ba da damar kafa wani abu mai suna kwamitin riƙo ba''

''Sai ga shi yau rana tsaka sun kafa kwamitin irin wannan saboda son rai''

''Idan har kwamitin yana da inganci kuma har su ke iƙirarin za su sayar da fom na ƴan takara me ya hana gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad tsayawa su yi takara a ciki?'' in ji shi.

Duka wannan dai na faruwa ne yayin da zaɓen 2027 ke ci gaba da karatowa lamarin da ya sa mutane da dama ke shakkun iya warware rikicin jama'iyyar ta PDP har ma ta tsayar da ƴan takara ballantana a yi batun yaƙin neman zaɓe a kuma kai ga samun nasara.