Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Amurka ke da sansanonin soji a Jamus?
Amurka ta jibge sojojinta a Jamus ne tun bayan kammala yaƙin duniya na biyu a shekarar 1945.
Bayan miƙa wuya da gwamnatin ƴan Nazi ta yi, adadin sojojin Amurka a ƙasar ya kai kimanin sojoji miliyan 1.6, kafin a rage yawansu zuwa ƙasa da 300,000 cikin shekara guda, ida yawanci waɗannan sojojin suka karɓe ragamar mulkin yankin da Amurka ta mamaye.
An ci gaba da rage yawansu har zuwa lokacin da aka fara samun cacar baka, bayan da aka fara ganin kamar an samu sauyin manufa daga kawar da ƴan Nazi zuwa sake gina ƙasar Jamus don ta zama wata kariya daga Tarayyar Soviet.
Bayan da aka kafa NATO da Jamus ta Yamma a 1949, an kafa wasu sansanonin sojan Amurka a yankin na dindindin a matsayin ɗaya daga cikin tsare-tsaren.
A lokacin yaƙin na cacar baka, Amurka ta yi aiki da manyan sansanonin soji kusan 50 da kuma wurare sama da 800 a Jamus, wadanda suka haɗa da manya-manyan filayen saukar jiragen sama na soja zuwa bariki, da wuraren sanya ido.
An rufe yawancin waɗannan wuraren tun bayan rugujewar katangar Berlin a shekarar 1989 da rushe Tarayyar Soviet bayan shekaru biyu.
A cikin shekarun 1960, 1970 da 1980, yawan sojojin Amurka a Jamus ya zarce 250,000, yayin da dubban ɗaruruwan danginsu ke zaune a ciki ko kuma a kusa da sansanonin, inda ya zama wani birni mai cin gashin kansa na Amurkawa da ke da makarantu, shaguna da gidajen wasan da wuraren shaƙatawa.
A cewar Cibiyar Bayanan Jami'an Tsaron Amurka, adadin sojojin ƙasar da ke aiki na dindindin a sansanoninta da ke ƙasashen Turai ya kai kusan 68,000 a ƙarshen shekarar da ta gabata, yayin da fiye da rabin su, kusan 36,400, ke Jamus.
Ana tuttura waɗannan jami'an a tsakanin sansanonin soja 20 zuwa 40 (ya danganta da muhimmancin "sansanin"), ciki har da hedikwatar Stuttgart na Rundunar Turai da Afirka, wanda ke kula ayyukan sojojin Amurka a nahiyoyin biyu.
Biyar daga cikin rundunonin sojin Amurka bakwai a Turai suna Jamus ne (sauran biyun kuma a Belgium da Italiya suke).
Bayan Stuttgart, wani sansanin Amurka mai muhimmanci shi ne na Ramstein, hedikwatar sojojin saman Amurka a Turai, wadda ke da kusan ma'aikatan sojan sama fiye da 8,500.
Sansanonin Grafenweir, Welseck, da Hohenfels, waɗanda rundunar Bavarian ke kula da su, na daga cikin manyan wuraren horar da sojojin Amurka a Turai, yayin da Wiesbaden Garrison ke zama hedikwatar Rundunar Sojojin Amurka ta Turai da Afirka, kuma Cibiyar Kiwon Lafiya ta Landstuhl ita ce babbar asibitin sojojin Amurka a wajen ƙasar.
Saboda muhimmancin waɗannan sansanonin, sun sha sauye-sauye sosai tun bayan kawo ƙarshen yaƙin cacar baka, domin su ne manyan wuraren gudanar da ayyukan ci gaba, inda ake amfani da su wajen tallafawa ayyukan sojin Amurka, ciki har da Iraƙi, Afghanistan, da kuma na baya-bayan nan Iran.
Dole ne Turai ta ƙara yawan kuɗaɗen da take kashewa a fannin tsaro - Nato
Ƙungiyar tsaro ta NATO ta bayyana cewa ta tuntuɓi Amurka domin samun fahimtar juna kan matakinta na janye dakarunta 5,000 daga Jamus, bayan samun saɓani tsakanin ƙasashen biyu.
Kakakin ƙungiyar ta NATO, Alison Hart ta bayyana a shafinta na X cewa ''muna tattaunawa da Amurka don samun fahimtar juna kan matakinta na janye sojojinta daga Jamus''.
Ta ƙara da cewa, wannan sauyin da aka samu "yana nuna buƙatar ƙasashen Turai su ci gaba da ƙara zuba kuɗaɗe a fannin tsaro da kuma daukar nauyin tsaronta," ganin irin ci gaban da aka samu tun bayan da ƙasashen ƙawancen suka amince da ware kashi 5 cikin 100 na tattalin arzikinsu ga harkokin tsaro.
Matakin na Amurka dai ya zo ne bayan da shugaba Donald Trump ya ci gaba da sukar sa ga shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz, wanda a ranar Litinin ɗin da ta gabata ya ce Iran na "wulaƙanta" Amurkar game da tattaunawar da ake yi domin kawo ƙarshen yaƙin Gabas ta Tsakiya.
A ranar Juma'a ne ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta bayyana cewa sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth ya bayar da umarnin janye dakarun ƙasar 5,000 daga Jamus cikin shekara ɗaya.
Adadin ya kai kashi 15 cikin 100 na sojojin Amurka da ke Jamus, wadda mamba ce a ƙungiyar tsaro ta NATO.