Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yadda gwamnatin Iran ta ƙara ƙarfi sakamakon yaƙi da Amurka'
- Marubuci, Fergal Keane
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Special correspondent
- Lokacin karatu: Minti 4
Har yanzu suna nan, duk inda ka shiga, duk akwatin talbijin da ka buɗe ba abin da ake gani sai fuskokin jagororin ƙasar da aka kashe, da kuma sabbin da aka naɗa, hotunansu sun cika wuraren taron jama'a.
An yi zanga-zanga an ƙare, yaƙi ya zo ya wuce, yanzu kuma ana lokacin tsagaita wuta, amma har yanzu gwamnatin Musulunci na da ƙarfinta.
A cewar wasu Iraniyawa da ke cikin ƙasar da BBC ta zanta da su, maimakon durƙusar da gwamnatin Musuluncin, ƙarfi ma ta ƙara sakamakon yaƙin, kuma yanzu tana cikin yanayin murƙushe waɗanda suka adawa da ita.
Sana da Diako - ba sunansu na gaskiya ba - matasan ma'aurata ne da ke zaune a Tehran, babban birnin ƙasar.
Ma'aurata ne masu ilimi da ke da matsakaicin samu, waɗanda ke fatan ganin ƙarshen gwamnatin masu tsattsauran ra'ayi.
Domin bayar da labaransu, mun cire wasu abubuwan da za su sa a gane su a labarin domin ba su kariya.
Dan jaridar da ke taimakon BBC wajen haɗa labarin, ya gana da Sana da Diako a kusa da wani wurin shaƙatawa, inda iyalai ke zuwa da yaransu, musamman a wannan lokaci da ake cikin yarjejeniyar dakatar da wuta.
Diako na fatan cewa rayuwa za ta inganta "abubuwa za su sauya, a shirye muke mu samu chanji," in ji shi.
Sana ta yi dariya yayin da yake bayyana haka.
"Chanji?" ta tambaya cikin mamaki. "Kasa na faɗawa hannun dakarun juyin juya hali , kana maganar chanji. Ai ƙasa ta rikici." Sana ta bayyana yadda ta ji tun bayan da Amurka da Isra'ila suka fara kai wa Iran hare-hare.
"Da fari ban so a yi yaƙin ba... [amma] yayin da aka fara, ake kuma kashe jiga-jigan gwamnatin, na riƙa jin daɗin hakan'', in ji ta.
Amma yayin da yaƙin ya ɗauki lokaci, sai fatan Sana ya fara daƙushewa, kamar dai yadda hakan ya faru ga Fadar White House, domin kuwa kisan Jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei da wasu manyan ƙusoshin gwamnatin ƙasar, bai haifar da wani sabon sauyin gwamnati ba.
"Saboda har yanzu mutanen gwamnatin ne ke mulki. Abinda nake fata bai faru ba. Komai ya taɓarɓare. An kuma bar mu da gwamnatin Musulunci. Ina matuƙar baƙin cikin nasarar da suka yi a yaƙin''.
Gwamnatin Musuluncin na da matuƙar gagarumin goyon baya a cikin ƙasar.
Ana yawan samun gangamin goyon bayan gwamnatin a faɗin Iran, yayin da kuma ake haramta gangamin adawa da ita.
Majiyoyinmu sun tattauna da ƴan gwagwarmaya, da masu rajin kare haƙƙin bil'adama da lauyoyi da ƴan jarida masu zaman kansu, waɗanda suka bayyana rashin gamsuwarsu da gwamnatin.
Akwai kuma fargabar da ake yi cewa ida yaƙin ya ƙare, gwamnatin za ta faɗaɗa gangaminta na muzguna wa ƴan ƙasar da suka nuna adawa da ita, musamman a lokacin yaƙin.
Kamfanin dillancin labaran HRANA na masu raji kare haƙƙin bil'adama da ke Amurka, ya ce fiye da mutum 53,000 aka kama lokacin zanga-zangar adawa da gwamnatin a watan Janairun da ya gabata, da kuma kafin ɓarkewar yaƙin.
Kuma tun bayan fara yaƙin an yi imanin kama wasu ƙarin dubbai tare da tsare su.
Akwai kuma bayanan da ke cewa an kashe fursunonin siyasa kusan 21 ta hanyar rataya a lokacin yaƙin, adadi mafi yawa a ɗan ƙanƙanin lokaci cikin fiye da shekara 30.
Tara daga cikin waɗanda aka kashe na da alaƙa da zanga-zangar watan Janairu, 10 kuma an zarge su da zama mambobin ƙungiyoyin adawa da gwamnati, yayin da aka zargi biyu da leƙen asiri.
Susan - wadda muka sauya sunanta - lauya ce da ke aiki da waɗanda aka tsaren, ta ce yanayin inda aka tsare mutanen na da matuƙar muni.
"Kafin yaƙin, akan tsanantawa waɗanda suka jagoranci zanga-zangar, da waɗanda ke riƙe da makamai. Amma a lokacin yaƙin an tsananta wa kowa cikin waɗanda ake tsaren da su,'' kamar yadda ta bayyana.
Labarinta ya nuna yadda yaƙin ya raba iyalai daban-daban. Iyayenta sun kasance masu goyon bayan gwamnatin, sai ta riƙa fargabar cewa za su fuskanci matsala idan aka hamɓarar da gwamnatin.
A lokacin da ta bayyana wa wani ɗan'uwanta - wanda shi ma mai adawa da gwamnatin ne - fargabar tata, sai ya nuna bai damu ba.
''Tunda suna son zama shahidai, wa zai hana su''?
Susan na fatan ƙarewar yaƙin, amma tana fargabar mutane irinta za su fuskanci mummunan matsin lamba.
Kuma tana fargabar halin da mutanen da ake tsare da su za su shiga. ''Ina tunanin idan aka gama yaƙin, akwai yiwuwar gwamnatin za ta sauke fushinta kan waɗanda take tsare da su. Ina ganin kamar lokaci ya ƙure mana''.
Masu gwagwarmayar kare haƙƙin bil'adama sun bayar da rahoton cewar an kashe mutum huɗu a wannan shekara zuwa yanzu, da aka zarga da alaƙa da hukumar leƙen asirin Isra'ila, Mossad.
Ƴan jarida masu zaman kansu na daga cikin mutanen da ake fargabar kama su kan zarge-zargen taimaka wa Amurka ko Isra'ila.
Akwai rahotonnin kama mutane da dama da aka zarga da aika bayanai ga kafofin yaɗa labaran ƙetare da ake ganin kamar cutar da ƙasar ne.
Ɗaya daga cikin ƴan jaridar - mun kira shi da Armin - wanda ya yi magana da abokin aikinmu a Tehran, ya bayyana yadda bayar da rahoton gaskiya kan yaƙin ya sa aka kama shi.
"Da fari ana zargin mu da laifukan siyasa. Amma a wannan yanayin yaƙin, idan muka bayar da rahoto za a iya zarginmu da laifin cin amanar ƙasa.''
Laifin cin amanar ƙasa ka iya ɗaukar hukuncin ɗaurin rai da rai a kotunan da ke ƙarƙashin gwmanatin Iran.
"A baya muna koƙarin gano yawan mutanen da aka cutar ko illar da zanga-zangar kan haifar, amma a yanzu batun ya sauya, muna mayar da hankali ne yanzu don kasancewa a raye, mu da iyalanmu'', in ji Armin.
Yayin da iyalansa ke ƙoƙarin barci, Armin ba ya iya barci.
"Nakan yi barci a zaune, ina ta mamakin makomarmu, kuma rashin tabbas ɗin na haifar da damuwa.''
Abin mamaki shi ne ƴan adawa da gwamnati sun ɓace daga titunan ƙasar, gwamnatin ƙasar ta kasance mai wuƙa da nama, ta kashe wanda ta ga dama, ta bar wanda take so.
Ƙarin rahoto daga Alice Doyard