Shin maslaha wajen fitar da ƴantakara alheri ne a siyasar Najeriya?

Lokacin karatu: Minti 5

Ƴansiyasa da dama a Najeriya, musamman waɗanda suka so tsayawa takara a kujeru daban-daban na ci gaba da bayyana damuwarsu kan hanyar da ake bi wajen fitar da ƴantakara.

A baya-bayan nan tsoffin ministoci biyu daga jihar Gombe da suka so tsayawa takarar gwamnan jihar ƙarƙashin jam'iyyar APC, Farfesa Ali Isa Pantami da Said Ahmed Alƙali, da kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Danjuma Goje sun yi watsi da hanyar da aka bi wajen fitar da ƴantakara a jihar Gombe.

Ƴansiyasar uku sun ce hanyar da aka bi wajen fitar da ƴantakara a jihar ta saɓa wa dokokin hukumar zaɓe da tsarin dimokraɗiyya.

Haka ma rahotonni sun ce an samu ƙorafin ƴansiyasa a jihohin Katsina da Adamawa da Ogun da Kogi da Nassarawa kan batun fitar da ƴantakara a jihohin nasu, musamman a jam'iyyar APC mai mulki.

Me dokar zaɓe ta ce kan fitar da ƴantakara?

Sabuwar dokar zaɓen Najeriya da aka yi wa gyaran fuska a 2025 ta tanadi hanyoyi biyu na fitar da ƴantakara a kowace jam'i'yya.

Hanyoyin su ne maslaha da kuma ƙato-bayan-ƙato, inda kuma dokar ta soke tsarin daliget da a baya aka fi amfani da shi.

  • Hanyar Maslaha: Ɗantakara zai samu tsaya wa jam'iyyarsa ne idan duka ƴantakarar suka sanar a rubuce cewa sun janye masa. Idan wannan wannan hanyar ba samu ba, to jam'iyya za ta je hanya ta biyu, wato ƙato-bayan ƙato.
  • Ƙato bayan ƙato: A wannan hanya kowane mutum mai rajistar katin jam'iyya zai shiga a dama da shi, in da zai zaɓi ɗantakarar da yake so, daga nan sai a ga wanda ya fi magoya baya, sai ya zama dantakara.

A baya akan yi amfani da tsarin daliget, waɗanda aka zaɓa daga matakin akwati zuwa mazaɓa da ƙaramar hukuma har zuwa jiha.

Tasirin gwamnoni a siyasar jihohi

Galibi tsarin da jam'iyyun siyasar Najeriya ke bi shi ne gwamna ne jagoran kowace jam'iyya a jiharsa, lamarin da ya sa yake da wuƙa da nama wajen fitar da ƴantakara a faɗin jihar tasa.

Ana ganin cewa hakan na bai wa gwamnoni damar tsayar da waɗanda suke so, su kuma hana wanda ba su so, wani abu da ya ƙara musu kwarjini a siyasar jihohinsu.

Rahotanni sun ce da dama cikin fitattun ƴanmajalisa sun nemi Shugaba Tinubu ya sanya baki a ba su tikitin takara kai-tsaye, amma hakan bai samu ba.

A wannan karon an ɗauki dogon lokaci ana tattaunawa, da kai ruwa rana a jihohin kafin sanar da ƴantakara, inda ake shiga ganawa daban-daban, domin cimma matsaya.

Ko hanyar sulhun alheri ne?

Daga cikin hanyoyin biyu na fitar da ƴantakara, sulhun ne kawai ba ya buƙatar kashe kuɗi da yawa, don haka ne mafi yawan jam'iyyun suka fi amfani da hanyar wajen fitar da ƴantakara.

Sai dai wasu ƴansiyasar na sukar hanyar da cewa ta saɓa wa tsarin dimokuraɗiyya, inda suke bayyana hanyar da ɗauki-ɗora.

Yusha'u Abdulhamid Shu'aiba Editan Jaridar PR Nigeria, kuma mai sharhi kan lamurran yau da kullum ya ce wannan hanya ta sulhu da ake amfani da ita wajen fitar da ƴantakara ba alheri ba ce a siyasar ƙasar.

''Domin abin da muke gani shi ne wasu tsiraru da ake cewa gwamnoni su ne ke fayyace waɗanda za su tsaya takarar muƙamai daban-daban a jihohin, wanda kuma hakan ya saɓa wa dimokraɗiyya'', in ji shi.

Yusha'u ya ce a idan ana maganar dimokraɗiyya mutane da yawa ne suke ɗaukar mataki, ba mutum ɗaya ba.

''Amma kawai sai mutum ya tashi daga ɗakinsa, kawai ya ce wane ne zai tsaya takarar muƙami kaza, ciki har da na gwamna, wai shi nan jagoran siyasar jiha, wannan ba dimokraɗiyya ba ne'', in ji editan na PR Nigeria.

'Tsayar da waɗanda ba su cancanta ba'

Mai bibiyar harkokin siyasar ya ce ɗaya daga cikin illar hakan shi ne tsayar da mutanen da ba su cancanta ba, don kawai wani dalili na ƙashin kai da gwamnonin ke da shi.

''Wani ma bai taɓa aiki a kamfani ba ma ballantana na gwamnati, ba shi da kowace irin ƙwarewa, amma saboda wani nasa, misali mahaifinsa sai a ɗauki takara a ba shi'', in ji shi.

Ya kuma ce wata illar ita ce asarar miliyoyin kuɗaɗe da ƴantakarar ke yi wajen sayen fom.

''Ta yaya za ka kashe miliyoyin kuɗi irin wannan, sannan kawai wani mutum guda ya je ya ce ba za ka yi takara ba, ba tare da amincewar duka sauran masu ruwa da tsaki na jihar ba'', in ji shi.

Sai dai masu mabambancin ra'ayi na ganin cewa hanyar masalaha na rage husuma tsakanin masu neman takara, kuma yana rage ɗawainiya da ake sha idan aka ce za a yi zaɓen fitar da gwani.

Mene ne alfanun maslaha?

Dakta Kabir Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a jihar Kano ya ce babbar matsalar da ake fama da ita game da maslaha ita ce "rashin bin ƙa'idojin da doka ta tsara".

"Doka ta ce wajibi ne a nemi amincewar duk wani ɗan takara, amma za ka ga yanzu ba a yin hakan," in ji Sufi.

Sai dai ya ce wasu daga cikin alfanun yin sulhu sun haɗa da:

  • Rage kashe kuɗi
  • Taƙaita rigingimu
  • Rage ficewar waɗanda ba su ji daɗin zaɓen fitar da ɗan takara ba

Me ya kamata a yi?

Editan na PR Nigeria ya ce ya kamata a yi abin da ya dace wajen fitar da ƴantakara, a tuntuɓi duka masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a jihar, domin samun shawararsu da amincewarsu.

"Ka nemo duka masu ruwa da tsaki na jam'iyya a jiharka, sannan ka fito da sunayen mutanen da ke neman takarar kowace kujera, ka tambayi ra'ayin duka masu ruwa da tsakin su bayyana maka ra'ayinsu a kansu, daga nan sai a haɗu a yanke hukunci''.

Dangane ta waɗanda suke da ƙorafi, Yusha'u ya ce su je wurin uwar jam'iyya ta ƙasa su kai ƙara, su kuma ce ba su yarda ba.

Sannan ya ce ita ma uwar jam'iyyar ya kamata ta yi adalci, idan an kai mata ƙorafi ta tsaya ta tantance da kuma yi adalci.

Idan wannan hanya ta gagara, ƴantakarar da ba su amince ba, suna iya zuwa kotu, domin ƙalubalantar matakin.