Hare-haren Isra'ila sun yi ajalin aƙalla mutum 17 a Lebanon
Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta ce akalla mutum 17 ne suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila a cikin awa 24 da suka gabata, duk da tsagaita wuta da ake sa ran tana aiki tsakanin Isra’ila da Beirut da kuma kungiyar Hezbollah. Sojojin Isra’ila sun kuma fitar da sabbin gargadin kwashe jama’a daga wasu ƙauyuka da ke wajen yankin kudancin Lebanon da suke iko da shi. Kungiyar Hezbollah ta ce mayaƙanta sun kai hare-hare kan sojojin Isra’ila a yankin. Shugaban ƙasar Lebanon, Joseph Aoun ya sake jaddada cewa ba zai gana da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ba, sai an kawo ƙarshen hare-haren Isra’ila.