Yawan fasinjojin da ke bi ta filin jirgin saman Dubai ya ragu matuƙa saboda yaƙin Iran

Asalin hoton, Getty Images
Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce yawan fasinjojin da suke bi ta filin jirgin saman Dubai ya ragu matuka, da kusan kashi biyu bisa 3 a watan Maris, sakamakon ɓarkewar yakin Iran.
Adadin matafiya a filin jirgin saman kasa da kasa na Dubai, wanda yawanci shi ne mafi hada-hadar zirga-zirga a duniya, ya ragu zuwa kusan miliyan biyu da rabi.
An dai kai hare-hare kan filin jirgin sau da dama, yayin da ƙasar mai arzikin mai ta fuskanci martanin Iran kan hare-haren Amurka da Isra’ila.
Hukumomi na fatan ayyukan filin jirgin za su dawo da tagomashin su, yayin da aka sake buɗe sararin samaniyar ƙasar baki ɗaya.











