Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Laraba 06/05/2026

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar da Nabeela Mukhtar Uba

  1. Ghana ta soma kwaso ƴan ƙasar daga Afirka ta kudu saboda rikicin ƙin jinin baƙi

    Gwamnatin Ghana ta mayar da ɗaya daga cikin ƴan ƙasarta, Emmanuel Asamoah, wanda ke Afirka ta Kudu gida, bayan da aka ganshi a wani bidiyo a yayin da wasu ƴan Afrika ta Kudu suka tsare shi suna ce mishi 'ya koma gida ya gyara ƙasar sa'.

    Lamarin ya fusata ƴan Ghana da dama, wanda ya kai har gwamnatin ƙasar ta gayyaci jami'an ofishin diflomasiyyar Afirka ta Kudu da ke Accra.

    A yanzu haka ƙasar ta Ghana na tayin dawo da ƴan ƙasar da ke son dawowa, a yayin da ake gudanar da zanga zangar nuna ƙin jinin baƙi a Afirka ta kudun.

    ''Duk ɗan Ghana da ke son komawa gida ya tuntuɓi ofishin jakadancin ƙasar domin a dawo da shi a cikin aljihun gwamnati,'' a cewar ministan harkokin wajen Ghana Okudzato Ablakwah.

    Wannan lamari na ƙin jinin baƙi dai ba sabon abu bane a Afirka ta kudu, inda ƴan ƙasar ke zargin baƙi da aikata laifuka da kuma ƙwace musu ayyuka.

    Hukumomi Afirka ta kudun sun ce suna duba lamarin shigar baƙi ƙasar, sai dai mutane da dama na ganin akwai buƙatar Afirka ta kudu ta tuna da tarihin goyon bayan da ƙasashen da lamarin ya shafa suka bata, maimakon kai wa baƙi hari.

  2. Ukraine ta zargi Rasha da karya tsagaita wutar ƙashin kai da Zelensky ya sanar

    Ukraine ta zargi Rasha da karya tsagaita wutar ƙashin kai da Shugaba Zelensky ya sanar, bayan da ta ƙaddamar da hare hare da jirage marasa matuƙa a birane da dama.

    Hukumomi a ƙasar sun ce harin ya kashe wata mata da ke tafiya cikin mota a yankin Sumy, yayin da hare haren suka lalata gidaje da dama a birnin Kharkiv.

    Tun da farko Ukraine ta ce tsagaita wutar za ta soma aiki ne a daren Laraba, sai dai Rasha ba ta amsa cewa za ta yi hakan ba.

    Moscow ta ce tana shirin tsagaita wuta na ƙashin kanta na kwanaki biyu a ranar Juma'a, saboda faretin bikin nasara na yaƙin duniya da za a yi a babban birnin ƙasar.

  3. An tsinci gawar alkalin da ke shari'ar uwargidan tsohon shugaban Koriya ta Kudu

    An tsinci gawar alkalin da ke shari'ar da ake yi wa uwargidan tsohon shugaban Koriya ta Kudu Kim Keon Hee a birnin Seoul.

    Ƴan sanda sun ce an gano gawar Shin Jong-o ne a cikin furanni da ke harabar babbar kotun a safiyar ranar Laraba.

    Rahotanni sun ce an samu takardar da ya rubuta kafin kashe kansa a aljihun sa, wanda ke nuna alamar yana neman gafara, amma bai ambaci shari’ar ba.

    Ƴan sanda sun ce basu gao wani shaida da ke nuna kashe shi aka yi ba.

    A watan da ya gabata alkali Shin ya ninka hukuncin daurin Miss Kim - matar tsohon shugaban kasar Yoon Suk Yeol - zuwa shekaru hudu bisa zarginta da laifin cin hanci da rashawa da kuma yin maguɗi a kasuwannin hannun jari.

  4. NiMet ta yi gargaɗin samun tsananin zafi a wasu jihohin arewacin Najeriya

    Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMET) ta yi gargaɗin cewa za a samu matsanancin yanayin zafi a ƙasar, inda ta ce hakan zai iya kai wasu ga shiga yanayin galabaita saboda zafin a wasu sassan ƙasar.

    A wata sanarwa da ta fitar a shafukanta, NiMet ta ce yanayin zafin zai fi shafar jihohin arewacin ƙasar da suka haɗa da jihohin Neja da Kebbi da Kano da Sokoto da Zamfara da Katsina da Yobe da Jigawa da Bauchi da Gombe da Borno da kuma Adamawa.

    A cewar sanarwar, akwai yiwuwar wasu jihohin ma da ba a ambata ba su samu ƙaruwar yanayin na zafi.

    A hasashen ta, yanayin zafin zai iya kai wa maki 40 zuwa 45 a ma'aunin salshiyas a arewacin ƙasar, yayin da tsakiyar ƙasar kuma zai kai tsakanin maki 35 zuwa 38 a ma'aunin salshiyas, a Kudancin ƙasar kuma yanayin na iya kai wa maki 33 zuwa 35.

    Hukumar yanayin ta buƙaci alumma su riƙa shan ruwa sosai, sannan su kasance a wuri mai iska sosai tare da kaucewa wurare masu cinkoson alumma, kuma su rage zama ƙarƙashin rana.

    Ta kuma shawarce su da su sanya hula da gilashi idan za su fita, kuma su sanya kaya marasa nauyi.

  5. Isra'ila ta gargaɗi mazauna kudancin Lebanon su gaggauta ficewa

    Rundunar sojin Isra'ila ta fitar da gargaɗi a safiyar yau Laraba, inda ta buƙaci mazauna birane da ƙauyuka 12 da ke kudancin Lebanon su gaggauta barin gidajensu.

    Gargaɗin kai hari ta sama da Isra'ila ta bayar ya shafi har da yankunan da ke arewacin Kogin Litani.

    Saƙon gargaɗin ya bayyana cewa Hezbollah ta saɓawa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.

    Sojojin Isra'ilar sun kuma ce fararen hula da ke kusa da inda ƴan ƙungiyar Hezbollah suke na iya kasancewa cikin barazana.

  6. Ministan harkokin wajen Iran ya gana da takwaransa na China a Beijing

    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya gana da takwaransa na kasar China Wang Yi a birnin Beijing.

    China wadda babbar kawar Iran ce tana yin biris da takunkuman da Amurka ta kakaba, ta hanyar ci gaba da shigo da danyen mai daga Iran zuwa matatunta.

    Tafiyar Mista Araghchi na zuwa ne gabanin ziyarar da shugaba Trump zai kai China a mako mai zuwa, inda zai gana da shugaba Xi Jinping.

    Mista Trump ya jinkirta ziyarar tasa ne bayan da gwamnatinsa da Isra'ila suka kai wa Iran hari a karshen watan Fabrairu.

  7. Trump ya dakatar da shirinsa na taimaka wa jiragen ruwa ratsawa ta Mashigar Hormuz

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya dakatar da wani shiri na taimaka wa jiragen ruwa ratsawa ta Mashigar Hormuz da ake taƙaddama a kai.

    Shugaban ya yi nuni da cewa, an yi hakan ne domin ganin ko za a iya cimma cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya da Iran.

    A wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta Mista Trump ya ce ya ɗauki matakin ne bisa buƙatar Pakistan wadda ke shiga tsakani a tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da Iran.

    Pakistan dai na ƙokarin tabbatar da an ƙulla yarjejeniya, amma ya zuwa yanzu sau ɗaya kacal aka yi tattaunawar kai tsaye, wadda ta ƙare ba tare da cimma matsaya ba.

    Mista Trump ya kuma yi nuni da cewa Amurka za ta ci gaba da datse tashoshin jiragen ruwan Iran.

  8. Buɗewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar yau Laraba.

    A yau ma, za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a duniya, kama daga yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran, da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance tare da mu.