KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Laraba 06/05/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar da Nabeela Mukhtar Uba

  1. China ta yi kiran a sake buɗe Mashigar Hormuz cikin gaggawa

    Wang Yi da Abbas Araqchi

    Asalin hoton, TASNIM

    Ministan harkokin wajen China Wang Yi ya yi kiran da a buɗe Mashigar Hormuz ''ba tare da ɓata lokaci ba'' a yayin da yake tattunawa da takwaransa na Iran.

    Ministocin sun gana ne a Beijing a yau Laraba, a ziyarar Ministan harkokin wajen Iran Abba Araqchi na farko zuwa China tun bayan soma yaƙin.

    Wang Yi ya kuma shaidawa Araqchi cewa cimma tsagaita wuta mai ɗorewa abu ne mai ''matuƙar muhimmanci'', inda ya ce akwai buƙatar a ci gaba da tattaunawa.

    Ya kuma ce a shirye Beijing take ta taimaka wajen shawo kan lamarin.

    Ganawar na zuwa ne mako guda kafin wata ganawa ta daban da Shugaba Trump ya tsara yi da shugaban China Xi Jingping, wanda ake hasashen shugabannin biyu za su tattauna kan yaƙin Iran da sake buɗe Mashigar.

  2. An tabbatar da mutum na takwas da ya kamu da cutar HantaVirus

    Hukumar Lafiya ta duniya, WHO ta tabbatar da mutum na takwas da ya kamu da cutar Hantavirus a cikin wani jirgin ruwan alfarma, a yayin da aka samu ɓarkewar cutar.

    Ta kuma tabbatar cewa za a iya yaɗa cutar tsakanin mutane.

    Mutum na takwas ɗin, wanda ɗan asalin Switzerland ne, yana karɓar magani a Zurich.

    Saura kuma na hanyar zuwa Netherlands.

    Zuwa yanzu fasinjoji uku sun mutu sakamakon cutar.

    Gwamnatin Sipaniya ta ce sauran fasinjojin da suka rage a jirgin ruwan ba sa nuna alamar kamuwa da cutar ta HantaVirus.

    Ta kuma amince jirgin ya tsaya a Tsibirin Canary domin yi wa mutanen gwaje gwaje.

    Daga nan za a kai ƴan Sipaniya birnin Madrid, sauran kuma za a mayar da su ƙasashen su.

    Sai dai shugaban Tsibirin Canary ya ce ba zai yarda jirgin ya tsaya a Tsibirin ba.

  3. An haramta wa waɗanda aka ba digirin girmamawa kiran kansu 'dafta'

    Gwamnatin Najeriya ta haramta wa mutanen da aka bai wa digirin girmamawa sanya 'Dr" a sunayensu.

    Ministan Ilimi na ƙasar Tunji Alausa, wanda ya bayyana hakan a fadar shugaban ƙasar da ke babban birnin ƙasar Abuja a yau Laraba, ya ce an cimma matsayar ne a taron majalisar zartaswa ta ƙasar da aka yi ranar 30 ga watan Afrilu.

    Alausa ya ce an ɗauki matakin ne domin kawo ƙarshen shekarun da aka shafe ana amfani da damar bayar da digirin ta yadda bai kamata ba, domin siyasa ko kuma saboda samun kuɗi.

    Ya ce wasu jami'oin da ba su kai matakin yin karatu na digirin digirgir ba, su ma sukan bayar da digirin girmamawa, ko kuma waɗanda ba su kai ko shekaru biyar da kafuwa ba, a cewar sa, kuma '' hakan bai dace ba''.

    Ya kuma ƙara da cewa nan gaba, wajibi ne jami'oi su nemi amincewa daga hukumar kula da jami'oi ta ƙasar NUC, kafin su bai wa mutum digirin girmamawa.

    Ministan ilimin ya kuma ce za a hukunta duk wata jami'a da ta saɓa umurnin, inda ya ƙara da cewa an bai wa shugabannin jami'oi umurnin su sake nazari kan yadda suke zaƙulo waɗanda ake bai wa digirin.

  4. Hare haren da za mu kai kan Iran za su fi na baya ƙazancewa -Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi karin bayani game da halin da ake ciki kan tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce yaƙin Iran da kuma toshe tashohin jiragen ruwan Iran na iya zuwa ƙarshe idan aka cimma yarjejeniya, amma kuma Amurka za ta iya ci gaba da yi wa Iran ruwan bama-bamai idan Iran ta ƙi cimma yarjejeniya.

    Idan Iran ''ta miƙa wuya kan duk abin da aka buƙata, to yaƙin zai ƙare'' in ji shi.

    Shugaban Trump ya kuma yi barazanar ci gaba da luguden wuta a Iran idan basu cimma yarjejeniya ba, ''kuma abin takaici zai fi hare haren da muka kai a baya ƙazancewa''.

  5. Farashin ɗanyan mai ya faɗi a kasuwannin duniya

    mutum a gaban gangunan mai

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin ɗanyan mai ya faɗi, yayin da hannayen jari a kasuwannin duniya suka tashi bayan rahotannin da ke cewa Amurka da Iran na gab da cimma kawo ƙarshen yaƙin.

    Farashin mai nau'in Brent ya faɗi zuwa ƙasa da dala 100 duk ganga.

    Farashin ɗanyan man na ta hawa da tashi tun soma yaƙin AMurka da Isra'ila kan Iran, bayan da Amurka da Iran suka taƙaita zirga zirga ta Mashigar Hormuz.

    A gefe guda kuma, kamfanonin jiragen sama sun rage tashin jirage 13,000 a faɗin duniya cikin watannan, a yayin da farashin man jirgin ke ta hauhawa.

    Masu sharhi sun ce lamarin ya shafi kusan fasinjoji miliyan biyu.

  6. Najeriya za ta aika tawaga ta biyu Afirka ta Kudu domin kawo ƙarshen kai hari kan ƴan ƙasarta

    Majalisar dattawan Najeriya ta ce za ta aika wata tawagar ƴan majalisar ƙasar zuwa Afirka ta Kudu, a wani ɓangare na ƙoƙarin samun maslahar diflomasiyya game da hare hare da kashe ƴan Najeriya a ƙasar.

    Hakan ya biyu bayan amincewa da wani ƙuduri da aka gabatar na yin tir da hare haren ƙin jinin baƙi da ake yi a Afirka ta Kudu, wanda sanatan yankin Akwa Ibon North East, Aniekan Bassey ya gabatar.

    Majaliar dattjian ta amince cewa tawagar za ta kasance wani kwamitin haɗin gwiwa da majalisar wakilai, wanda shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio zai jagoranta.

    Ana sa ran tawagar za ta gana da gwamnatin Afirka ta kudu da kuma shugabannin majalisar ƙasar domin lalubo hanyoyin kawo ƙarshen kai hari kan ƴan Najeriya.

    Wannan ce za ta kasance tawaga ta biyu daga Najeriya da za ta je Afirka ta Kudu tun bayan hare haren baya bayan nan, sai dai zuwa yanzu ba a sanya ranar da za ta tafi ba.

    A yanzu haka ministan harkokin wajen Najeriya Bianca Odumegwu Ojukwu na ƙasar da tawagarta domin tattaunawa da gwamnatin Afirka ta kudu.

  7. Ana samun ci gaba a tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Iran - Pakistan

    Trump da Shehbaz Sharif na Pakistan

    Asalin hoton, Reuters

    Fira Ministan Pakistan, wanda shi ne babban mai shiga tsakanin Iran da Amurka, ya ce ana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi na cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shehbaz Sharif ya jinjinawa Donald Trump kan dakatar da shirinsa na yi wa jiragen kasuwanci da suka maƙale a mashigar Hormuz rakiya da sojoji, wanda aka soma a ranar Litinin da ta gabata.

    Tun da farko Mista Trump ya ce ya dakatar da shirin ne domin ganin ko za a iya cimma yarjejeniya da Iran.

    Pakistan ta shafe watanni tana kai wa da komowa da sharuɗɗan ƙasashen biyu.

  8. Ghana ta soma kwaso ƴan ƙasar daga Afirka ta kudu saboda rikicin ƙin jinin baƙi

    masu zanga zanga a Afrika ta kudu

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Gwamnatin Ghana ta mayar da ɗaya daga cikin ƴan ƙasarta, Emmanuel Asamoah, wanda ke Afirka ta Kudu gida, bayan da aka ganshi a wani bidiyo a yayin da wasu ƴan Afrika ta Kudu suka tsare shi suna ce mishi 'ya koma gida ya gyara ƙasar sa'.

    Lamarin ya fusata ƴan Ghana da dama, wanda ya kai har gwamnatin ƙasar ta gayyaci jami'an ofishin diflomasiyyar Afirka ta Kudu da ke Accra.

    A yanzu haka ƙasar ta Ghana na tayin dawo da ƴan ƙasar da ke son dawowa, a yayin da ake gudanar da zanga zangar nuna ƙin jinin baƙi a Afirka ta kudun.

    ''Duk ɗan Ghana da ke son komawa gida ya tuntuɓi ofishin jakadancin ƙasar domin a dawo da shi a cikin aljihun gwamnati,'' a cewar ministan harkokin wajen Ghana Okudzato Ablakwah.

    Wannan lamari na ƙin jinin baƙi dai ba sabon abu bane a Afirka ta kudu, inda ƴan ƙasar ke zargin baƙi da aikata laifuka da kuma ƙwace musu ayyuka.

    Hukumomi Afirka ta kudun sun ce suna duba lamarin shigar baƙi ƙasar, sai dai mutane da dama na ganin akwai buƙatar Afirka ta kudu ta tuna da tarihin goyon bayan da ƙasashen da lamarin ya shafa suka bata, maimakon kai wa baƙi hari.

  9. Ukraine ta zargi Rasha da karya tsagaita wutar ƙashin kai da Zelensky ya sanar

    Zelensky

    Asalin hoton, EPA

    Ukraine ta zargi Rasha da karya tsagaita wutar ƙashin kai da Shugaba Zelensky ya sanar, bayan da ta ƙaddamar da hare hare da jirage marasa matuƙa a birane da dama.

    Hukumomi a ƙasar sun ce harin ya kashe wata mata da ke tafiya cikin mota a yankin Sumy, yayin da hare haren suka lalata gidaje da dama a birnin Kharkiv.

    Tun da farko Ukraine ta ce tsagaita wutar za ta soma aiki ne a daren Laraba, sai dai Rasha ba ta amsa cewa za ta yi hakan ba.

    Moscow ta ce tana shirin tsagaita wuta na ƙashin kanta na kwanaki biyu a ranar Juma'a, saboda faretin bikin nasara na yaƙin duniya da za a yi a babban birnin ƙasar.

  10. An tsinci gawar alkalin da ke shari'ar uwargidan tsohon shugaban Koriya ta Kudu

    An tsinci gawar alkalin da ke shari'ar da ake yi wa uwargidan tsohon shugaban Koriya ta Kudu Kim Keon Hee a birnin Seoul.

    Ƴan sanda sun ce an gano gawar Shin Jong-o ne a cikin furanni da ke harabar babbar kotun a safiyar ranar Laraba.

    Rahotanni sun ce an samu takardar da ya rubuta kafin kashe kansa a aljihun sa, wanda ke nuna alamar yana neman gafara, amma bai ambaci shari’ar ba.

    Ƴan sanda sun ce basu gao wani shaida da ke nuna kashe shi aka yi ba.

    A watan da ya gabata alkali Shin ya ninka hukuncin daurin Miss Kim - matar tsohon shugaban kasar Yoon Suk Yeol - zuwa shekaru hudu bisa zarginta da laifin cin hanci da rashawa da kuma yin maguɗi a kasuwannin hannun jari.

  11. NiMet ta yi gargaɗin samun tsananin zafi a wasu jihohin arewacin Najeriya

    NIMET

    Asalin hoton, Google

    Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMET) ta yi gargaɗin cewa za a samu matsanancin yanayin zafi a ƙasar, inda ta ce hakan zai iya kai wasu ga shiga yanayin galabaita saboda zafin a wasu sassan ƙasar.

    A wata sanarwa da ta fitar a shafukanta, NiMet ta ce yanayin zafin zai fi shafar jihohin arewacin ƙasar da suka haɗa da jihohin Neja da Kebbi da Kano da Sokoto da Zamfara da Katsina da Yobe da Jigawa da Bauchi da Gombe da Borno da kuma Adamawa.

    A cewar sanarwar, akwai yiwuwar wasu jihohin ma da ba a ambata ba su samu ƙaruwar yanayin na zafi.

    A hasashen ta, yanayin zafin zai iya kai wa maki 40 zuwa 45 a ma'aunin salshiyas a arewacin ƙasar, yayin da tsakiyar ƙasar kuma zai kai tsakanin maki 35 zuwa 38 a ma'aunin salshiyas, a Kudancin ƙasar kuma yanayin na iya kai wa maki 33 zuwa 35.

    Hukumar yanayin ta buƙaci alumma su riƙa shan ruwa sosai, sannan su kasance a wuri mai iska sosai tare da kaucewa wurare masu cinkoson alumma, kuma su rage zama ƙarƙashin rana.

    Ta kuma shawarce su da su sanya hula da gilashi idan za su fita, kuma su sanya kaya marasa nauyi.

  12. Isra'ila ta gargaɗi mazauna kudancin Lebanon su gaggauta ficewa

    sojoji

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojin Isra'ila ta fitar da gargaɗi a safiyar yau Laraba, inda ta buƙaci mazauna birane da ƙauyuka 12 da ke kudancin Lebanon su gaggauta barin gidajensu.

    Gargaɗin kai hari ta sama da Isra'ila ta bayar ya shafi har da yankunan da ke arewacin Kogin Litani.

    Saƙon gargaɗin ya bayyana cewa Hezbollah ta saɓawa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.

    Sojojin Isra'ilar sun kuma ce fararen hula da ke kusa da inda ƴan ƙungiyar Hezbollah suke na iya kasancewa cikin barazana.

  13. Ministan harkokin wajen Iran ya gana da takwaransa na China a Beijing

    ..

    Asalin hoton, TASNIM

    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya gana da takwaransa na kasar China Wang Yi a birnin Beijing.

    China wadda babbar kawar Iran ce tana yin biris da takunkuman da Amurka ta kakaba, ta hanyar ci gaba da shigo da danyen mai daga Iran zuwa matatunta.

    Tafiyar Mista Araghchi na zuwa ne gabanin ziyarar da shugaba Trump zai kai China a mako mai zuwa, inda zai gana da shugaba Xi Jinping.

    Mista Trump ya jinkirta ziyarar tasa ne bayan da gwamnatinsa da Isra'ila suka kai wa Iran hari a karshen watan Fabrairu.

  14. Trump ya dakatar da shirinsa na taimaka wa jiragen ruwa ratsawa ta Mashigar Hormuz

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya dakatar da wani shiri na taimaka wa jiragen ruwa ratsawa ta Mashigar Hormuz da ake taƙaddama a kai.

    Shugaban ya yi nuni da cewa, an yi hakan ne domin ganin ko za a iya cimma cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya da Iran.

    A wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta Mista Trump ya ce ya ɗauki matakin ne bisa buƙatar Pakistan wadda ke shiga tsakani a tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da Iran.

    Pakistan dai na ƙokarin tabbatar da an ƙulla yarjejeniya, amma ya zuwa yanzu sau ɗaya kacal aka yi tattaunawar kai tsaye, wadda ta ƙare ba tare da cimma matsaya ba.

    Mista Trump ya kuma yi nuni da cewa Amurka za ta ci gaba da datse tashoshin jiragen ruwan Iran.

  15. Buɗewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar yau Laraba.

    A yau ma, za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a duniya, kama daga yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran, da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance tare da mu.