Yaushe za a rufe ƙofar sauya sheƙa a Najeriya?

Tun bayan da aka fitar da sabon jadawalin hukumar zaɓe ta Najeriya game da shirye-shiryen babban ƙasar da kuma garambawul da aka yi wa dokokin zaɓen, sai ya kasance jam'iyyu na ta ƙoƙarin tabbatar da kiyaye dokokin.
Sauye-sauyen da ake gani a jam'iyyun ƙasar ba sa rasa nasaba da ƙoƙarin ganin an kammala tsare-tsare domin tsayar da ƴantakara.
A sabon jadawalin zaɓen, za a yi zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisun tarayya ne a ranar 16 ga watan Janairun shekarar 2027 bayan an rage wasu kwanaki saboda ƙorafin da aka yi na yiwuwar faɗawar zaɓen a cikin azumi.
Haka kuma za a yi zaɓen gwamnoni na ƴan majalisun jiha a ranar 6 ga watan Fabrailun 2027.
Da farko INEC ta shirya gudanar da babban zaɓen shugaban ƙasa ne a ranar 20 ga watan Fabrailu, sai na gwamnoni a ranar 6 ga watan Maris kafin ta sauya ta hanyar mayar da su baya.
Sai dai duk wani sauyi da aka samu a jadawalin, dole sai ya taɓa tsare-tsaren dokokin zaɓen ƙasar, lamarin da ke ƙara hargitsi ƴan siyasar ƙasar domin sun san akwai aiki a gaba.
Jadawalin zaɓukan 2027 da INEC ta fitar ya nuna cewa za a gudanar da zaɓen fitar da gwani, da kuma warware duk wata taƙaddama da za ta taso a lokacin zaɓukan, daga ranar 22 ga watan Afrilun 2026 zuwa 30 ga watan Mayun 2026.
Za a fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokokin tarayya daga ranar 19 ga watan Agusta 2026.
Sai kuma yaƙin neman zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi, da za a fara daga ranar 9 ga watan Satumban 2026.
Me doka ta ce kan sauya sheƙa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Abba Hikima, lauya ne mai zaman kansa a Najeriya, ya bayyanawa BBC cewa dole akwai tanada-tanaden da suka kamata a yi la'akari da su wajen shiga da fita daga wata jam'iyya zuwa wata.
Ya ce sauya sheƙa musamman ga wanda yake so ya yi takara, "daga jadawalin da INEC ta fitar, ta bayyana cewa daga ranar 23 zuwa 30 ga watan Mayu ne aka ƙayyade wa kowace jam'iyya ta kammala zaɓukan fitar da ƴantakara," in ji Barista Abba.
Lauyan ya ce duk wanda yake so ya koma wata jam'iyya ya kamata ne ya koma kafin ranar 30 ga watan na Mayu.
Sai dai ya ƙara da cewa suma jam'iyyu kowacce na da tanade-tanaden da suke amfani da su a matsayin ɗoriya da na INEC.
"Akwai jam'iyyun da suka tsara cewa mutum ba zai shiga jam'iyyar, sannan ya tsaya takara ba sai ya kai wani lokaci mai tsawo a cikinta. Amma wasu jam'iyyun suna da tanadin ɗaga ƙafa da ake kira 'waiver' inda ake yafe wa mutum wannan buƙatar, a ba mutum damar shiga takara," in ji Hikima.
A game da abin da doka ta ce game da zaɓin da ƴantakara suke da shi bayan kammala zaɓukan fitar da ƴantakara, Barista Abba ya ce idan har ɗantakara ya tsaya har aka miƙa ɗantakara, to akwai ƙura.
"Yanzu ka ga daga cikin wajibcin INEC ma akwai cewa dole kowace jam'iyya ta miƙa sunan ƴaƴanta," in ji shi, inda ya ƙara da cewa, "amma a jadawalin na INEC ba ta bayyana yaushe ne za ta kulle amsar sunan ƴaƴan ba."
Lauyan ya ce duba da yanayin dokar, idan an riga an miƙa sunan ƴaƴan jam'iyya, ba zai yi mutumin da ba ya cikin ƴaƴan da aka miƙa wa INEC ya shiga ya tsaya mata takara.
"Amma INEC ta bayar da wata dama ta janyewa da musanya ɗantakara. Misali mutum ya shiga takara an kusa zaɓe sai ya sanar da INEC cewa ya janye takara, to a wannan yanayi jam'iyya za ta iya maye gurbinsa da wani," in ji shi.
Sai dai ya ce wannan damar ma tana da wa'adi, domin ita ma za a rufe na shugaban ƙasa da majalisun tarayya a ranar 22 ga watan Agusta, sai na gwamnoni da majalisar jihohi a ranar 19 ga Satumba.
Babban zaɓen 2027
Hukumar zaɓen ƙasar, INEC ta saka ranar Asabar, 16 ga watan Janairun 2027 a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.
Tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuraɗiyya a 1999, an zaɓi shugabannin ƙasa guda biyar da suka ja ragamar ƙasar.
Biyu daga cikin shugabannin (Obasanjo da Buhari) sun yi shekara takwas kowanne, yayin da Yar' Adua ya yi shekara uku, Jonathan ya yi shekara biyar, sai kuma Tinubu da ke shekarar mulkinsa ta uku zuwa yanzu, kuma yake hanƙoron samun wa'adi na biyu.
Kamar yadda aka saba za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasar ne tare da na ƴan majalisar dattawa da na wakilan ƙasar.
Najeriya dai na da sanatoci 109 - uku daga kowace jiha - sai ɗaya daga birnin Abuja, yayin da take da ƴanmajalisar wakilai 360, waɗanda ake zaɓa gwargwadon yawan al'ummar yankunan da suka fito.
Kamar yadda jadawalin hukumar zaɓen ya nuna za a gudanar da zaɓen gwamnoni bayan na shugaban ƙasa da mako biyu.
INEC ta ce za a gudanar da zaɓen gwamnonin ranar Asabar, 6 ga watan Fabrairun 2027.
Za a gudanar da zaɓukan gwamnonin a jihohi 28 na ƙasar, yayin da sauran jihohin takwas na ƙasar za a yi zaɓukan gwamanan daga baya.
Haka kuma za a gudanar da zaɓukan gwamnonin tare da na ƴanmajalisar dokoki na jihohi.
Akwai jihohin ƙasar takwas da ba za a yi zaɓukan gwamna a watan Fabrairun 2027 ba, sakamakon wasu matsaloli da suka janyo tsaiko a zaɓukan jihohin.
Jihohin takwas sun haɗa da: Kogi da Bayelsa da Imo da Anambra da Edo da Ekiti da Osun da kuma Ondo.
Ana gudanar da zaɓukan waɗannan jihohi ne daga baya.











