Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Messi, Neymar, Mbappe, Sancho, Alli da Hakimi
Kocin Barcelona Ronald Koeman ya ce yana "fata amma ba ni da kwarin gwiwar" cewa dan wasan Argentina mai shekara 33 Lionel Messi zai zauna a kungiyar a bazara. (Athletic - subscription required)
Kwangilar Messi wadda ta kai £492m a Barcelona, wadda za ta kare a wannan bazarar, ta kunshi wani sakin layi da ya amince dan wasan ya bar kungiyar ba tare da bayar da ko sisi ba da zarar yankin Catalonia ya samu 'yancin kasa. (El Mundo, via Mail)
Dan wasan Brazil Neymar, mai shekara 28, na shirin sanya hannu kan sabuwar kwangilar shekara hudu a Paris St-Germain. (Goal)
PSG na sha'awar sake hada Neymar da abokinsa na Barcelona Messi a Parc des Princes. (Metro)
Sai dai shi ma dan wasan Faransa mai shekara 22, Kylian Mbappe, wanda kwangilarsa za ta kare a PSG a 2022, har yanzu bai yanke shawara kan makomarsa ba. (ESPN)
Wai yiwuwaManchester United ta daina zawarcin dan wasanBorussia Dortmund dan kasar Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, bayan da dan wasan Ivory Coast mai shekara 18 Amad Diallo ya burge ta tun lokacin da ya isa kungiyar daga Atalanta. Dan wasan Dortmund dan kasar Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20, da dan wasan Sevilla dan kasar Faransa Jules Kounde, mai shekara 22, su ne yanzu kungiyar ta fi so ta dauka. (Express)
Shugaban Tottenham Daniel Levy ya dakile yunkurin PSG na daukar dan wasan Ingila Dele Alli, mai shekara 24, saboda matsalar da 'yan wasan Spurs suke fama da ita ta yawan jin rauni da kuma rashin katabus. (Telegraph).
Arsenal, Chelsea da Manchester City suna son daukar dan wasan Inter Milan mai shekara 22 dan kasar Morocco Achraf Hakimi a bazara. (Calciomercato - in Italian)
Mai yiwuwa dan wasan Arsenal mai shekara 19 dan kasar Ingila Folarin Balogun zaibar kungiyar a karshen kakar wasan nan. (Express)
Kocin Leicester City Brendan Rodgers zai nemi daukar dan wasan gaba idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwalllo ta bazara. (Independent)
Real Madrid za ta sayar da dan wasan Brazil mai shekara 20 Vinicius Junior a bazarar nan. (AS - in Spanish)