Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Chalobah, Maitland-Niles, Eriksen, Ramos, Upamecano, Ndombele

Leicester City na son daukar dan wasan Watford da Ingila Nathaniel Chalobah, mai shekara 26, ranar da za a rufe kasuwar 'yan kwallo. (Leicester Mercury)

Liverpool ta tuntubi Marseille domin daukar dan wasan Croatia Duje Caleta Car, mai shekara 24. (Mail)

Leicester ta shirya karbar aron dan wasan Arsenal da Ingila Ainsley Maitland-Niles. Southampton, West Brom da Newcastle su ma suna son daukar dan wasan mai shekara 23. (Mirror)

Dan wasan tsakiyar Denmark Christian Eriksen, mai shekara 28, wanda aka alakanta da komawaTottenham, yana iya zama a Inter Milan bayan wa'adin rufe kasuwar musayar 'yan kwallo kuma zai taka muhimmiyar rawa a kungiyar, a cewar babban jami'in kungiyar Giuseppe Marotta. (Sky Sports)

Tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino yana son daukar dan wasan Sifaniya daReal Madrid Sergio Ramos, mai shekara 34, zuwa Paris St-Germain a bazara. (Independent)

Dan wasan RB Leipzig da Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 22, zai iya tafiya kungiyar da ke buga Premier League a wannan shekarar a yayin da wakilinsa ya ce dan wasan zai yi zabi tsakanin "babbar kungiyar" da ke Turai da kuma Bayern Munich "nan ba da jimawa" ba. (Mail)

Dan wasan Tottenham Tanguy Ndombele, mai shekara 24, ya bayyana cewa abokinsa dan kasar Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, ya yi yunkurin jan hankalinsa ya bi shi Paris St-Germain. (Goal)

West Brom na son daukar 'yan wasa biyu a ranar da za a rufe kasuwar musayar 'yan kwallo - inda take son daukar dan wasan Turkiyya Okay Yokuslu, mai shekara 26, daga Celta Vigo da dan wasan Ingila Japhet Tanganga, mai shekara 21, dagaTottenham. (Express and Star)

Birmingham City ta mika £3m domin daukar dan wasan Hibernian mai shekara 23 dan yankin Scotland Kevin Nisbet. (Scottish Sun)

Newcastle United na son daukar aron dan wasan Leicester City dan kasar Ingila Hamza Choudhury, mai shekara 23, zuwa karshen kakar wasan bana. (Chronicle)

Burnley na son daukar dan wasan Bournemouth da Norway Josh King, mai shekara 29, ranar da za a rufe kasuwar musayar 'yan kwallo, kodayake za ta iya fuskantar matsala game da alawus-alawus dinsa. (Lancashire Telegraph)

Manchester City tana tattaunawa da Fluminense domin daukar 'yan wasa Brazil masu shekara 17 Kayky da Metinho, sai dai kungiyar kwallon kafar tasu tana bukatar fiye da £15m da aka yi mata tayi. (Mail)