KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Laraba 13/05/2026

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir da Aisha Babangida

  1. Tinubu ya isa Kigali domin halartar taron ƴan kasuwa da masu zuba jari na Afrika

    ....

    Asalin hoton, Bayo Onanuga

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya isa birnin Kigali na ƙasar Rwanda domin halartar taron ƴan kasuwa da masu zuba jari na Afrika da ake kira da Africa CEO Forum karo na 13, wanda zai fara a ranar Alhamis.

    An tarɓi Shugaba Tinubu a filin jirgin saman Kigali inda Ministan Harkokin Waje, Ambasada Bianca Ojukwu da Ministan Tsaron Rwanda, Juvenal Marizamunda suka tarbe shi.

    Sauran da suka halarci tarbar sun haɗa da ministar masana’antu, kasuwanci da Zuba Jari, Dr Jumoke Oduwole da daraktan hukumar tsaron ƙasa (NIA) da Ambasada Mohammed Mohammed, da kuma wakilin Najeriya a Rwanda, Ambasada Ibrahim Zanna.

    Taron wanda aka kafa a shekarar 2012 shi ne babban taron shekara-shekara da ke tattaro shugabannin kamfanoni, masu zuba jari da masu tsara manufofi a Afrika.

    Taron na mayar da hankali ne kan inganta ci gaban tattalin arziki ta hanyar haɗin gwiwa, haɗa kasuwanni da ƙarfafa zuba jari tsakanin ƙasashe.

    A yayin taron, Shugaba Tinubu zai gabatar da jawabi inda zai bayyana nasarorin da ake samu daga sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya.

    Haka kuma, ana sa ran Tinubu zai gudanar da tarurruka da manyan shugabannin kasuwanci daga Afrika da sauran sassan duniya.

  2. An killace fiye da fasinjojin jirgin ruwa 1,700 saboda cutar norovirus

    Jirgin Ruwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Faransa sun keɓe fiye da mutum 700 cikin wani jirgin ruwa a Bordeaux bayan da ɗaya daga cikin fasinjojin ya mutu sakamakon zargin da ake ya kamu da ƙwayar cutar norovirus.

    Kusan wasu mutum 50 da ke cikin jirgin mai suna Ambassador Cruise Line suna nuna alamun sun kamu da cutar mai saurin yaɗuwa da ke janyo amai da gudawa.

    Jirgin wanda ke ɗauke da ƴan ƙasar Birtaniya da Ireland, ya bar tsibirin Shetlands a farkon watan nan inda kuma aka tsara zai ci gaba da tafiyarsa daga Faransa zuwa Sifaniya.

  3. Batun yaƙin Iran zai iya mamaye taron ministocin harkokin wajen BRICS a New Delhi

    Ana tsammanin cewa batun yaƙin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran zai mamaye batutuwa a taron ministocin harkokin wajen ƙungiyar BRICS na kwanaki biyu da zai fara gobe Alhamis a birnin New Delhi.

    Rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce taron zai gwada yadda ƙasashen ƙungiyar za su iya cimma matsaya guda tare da fitar da sanarwar haɗin gwiwa duk da saɓanin ra’ayoyi da ake da su.

    Ƙungiyar BRICS ta fara ne da ƙasashen Brazil da Rasha da Indiya da China da kuma Afirka ta Kudu, amma daga baya ta faɗaɗa tare da shigar ƙasashe irin su Masar da Habasha da Indonesia da Iran da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

    Iran ta buƙaci mambobin BRICS su yi Allah wadai da matakan da Amurka da Isra’ila suka ɗauka, sai dai an bayyana cewa akwai saɓani tsakanin Iran da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa kan lamarin.

    Duk da tashin hankalin da ake ciki, Indiya na ƙoƙarin ganin an cimma sanarwar bai ɗaya a taron ministocin harkokin wajen BRICS.

    Ƙasashen BRICS na kuma fuskantar matsin tattalin arziki sakamakon tashin farashin makamashi bayan barkewar yaƙin.

    Ana sa ran ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, zai isa New Delhi a daren yau domin halartar taron.

    Haka kuma ana tsammanin ministan harkokin wajen Rasha, Sergey Lavrov, zai halarci taron.

  4. NAPTIP ta ceto mutum 15 daga hannun 'masu safarar mutane' a Nasarawa

    Binta Adamu Bello

    Asalin hoton, @naptipnigeria

    Hukumar yaƙi da safarar mutane a Najeriya NAPTIP ta kuɓutar da mutum 15 har da baƙi bayan da ta bankaɗo wata ƙungiyar masu safarar mutane da ake zargi tana aiki a matsayin kamfanin tallata kayayyaki ta intanet a jihar Nasarawa.

    NAPTIP ta kuɓutar da mutanen ne bayan samamen da jami'anta suka kai ƙananan hukumomin Karu da Keffi sakamakon sahihan bayanan da suka samu a kan kamfanin.

    NAPTIP ta sanar da haka ne cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba.

    Ta ce an kai samamen ne a ranar 7 ga watan Mayu inda ta ce cikin mutanen da aka kuɓutar akwai mata huɗu da maza 11. Cikin mazan, uku ƴan Najeriya ne sai sauran da suka fito daga wasu ƙasashen.

  5. Trump ya isa Beijing don ganawa da Xi Jinping

    Yadda aka tarbi Shugaba Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya isa birnin Beijing da ke China don halartar wani babban tsaro da shugaba Xi Jinping.

    Wannan ce ziyararsa ta farko cikin shekara 10 tun 2017.

    A yayin ziyarar ta yini biyu, Trump zai tattauna da Shugaba Jinping kan batutuwa da dama kuma shugabannin biyu na fatan ziyarar za ta yauƙaƙa dangantaka tsakanin su.

    Tun da farko an tsara Trump zai je Beijing ranar 31 ga watan Maris sai dai yaƙin Iran ya haifar da tsaiko na wata biyu.

    A tsakiyar watan Maris, ƴan makonni kafin yaƙin ya ɓarke, Trump ya ɗage ganawar inda ya ce ya zama dole ya kasance a Amurka saboda yaƙin.

    China - ɗaya daga cikin manyan magoya bayan Iran ta yi ta yin baya baya da batun ganawar sai dai a farkon makon nan, ƙasar ta tabbatar da cewa za a yi taron.

    ..

    Asalin hoton, Reuters

  6. Kotu ta ɗaure Saleh Mamman shekara 75 kan badaƙalar kuɗi

    Tsohon Ministan Lantarki a Najeriya, Saleh Mamman

    Asalin hoton, @EngrSMamman

    Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yanke wa tsohon ministan lantarki a Najeriya shekara 75 a gidan yari kan almundahanar fiye da naira biliyan 33.

    Alƙalin James Omotosho ya yanke hukuncin bayan ya samu Mamman da laifin aikata laifuka 12 da hukumar yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta'annati EFCC ta tuhume shi da su masu alaƙa da haɗa baki da almundahana.

    EFCC ta tabbatar da hukuncin kotun a saƙon da ta wallafa a shafinta na Fesbuk.

    Alƙali Omotosho ya ce ya kamata hukuncin zaman gidan yarin ya soma aiki daga ranar da aka kama mai laifin kasancewar an yanke hukuncin ne ba ya harabar kotun.

    Kotun ta kuma umarci hukumomin tsaro da su kamo tsohon ministan a duk inda yake sannan kuma a miƙa wa gwamnati kuɗaɗe da dukiyoyin da aka ƙwato daga hannunsa.

    Kotun ta kuma nemi Mamman da ya mayar da naira biliyan 22 na kuɗaɗen aikin samar da cibiyoyin lantarki na Mambila da Zungeru.

    An gabatar da Mamman gaban babbar kotun tarayya a Abuja cikin Yulin 2024 bisa tuhume-tuhume 12 da ke da alaƙa da haɗin baki da almundahana. Ya musanta aikata zarge-zargen.

    Sai dai a lokacin shari'ar, EFCC ta gabatar da shaidu 17 tare da miƙa wasu bayanai gaban kotun.

    Hukuncin da aka yanke a yanzu ya kawo ƙarshen wata babbar shari'ar cin hanci da rashawa da ta fara tun bayan kama tare da tsare Mamman da EFCC ta yi a ranar 10 ga Mayun 2021.

  7. A yi bincike kan rahoton kisan farar hula a Najeriya da Chadi - Volker Türk

    Volker Türk

    Asalin hoton, Reuters

    Babban jami'in kare haƙƙin bil adama a Majalisar Ɗinkin Duniya, Volker Türk ya buƙaci a gudanar da bincike kan rahotannin kisan gomman farar hula a wasu hare-hare ta sama da sojojin Najeriya da Chadi suka kai lokuta daban daban a ƙarshen makon da ya wuce.

    Mista Turk ya ce ya kaɗu da zarge-zargen da ke cewa aƙalla farar hula 100 ne suka mutu a hare-haren da aka kai a wata kasuwa da ke jihar Zamfara a arewa maso gabashin Najeriya da kuma wanda aka kai kan masunta a yankin tafkin Chadi.

    Hukumomin soji dai sun musanta kisan farar hula a samamen da suka kai inda suka ce an kai hare-haren ne kan masu iƙirarin Jihadi kuma an kai su ne bisa tsarin dokokin kare haƙƙin bil adama na ƙasa da ƙasa.

    Hukumomin Chadi sun ce hare-haren an kai su ne kan mayaƙan Boko Haram.

    Tuni dai Ƙungiyar Amnesty International ita ma ta nemi a gudanar da zurfaffan bincike kan lamarin.

    Daraktan ƙungiyar Amnesty International a Najeriya, Malam Isa Sanusi, ya ce bisa bayanan da suka tattara, kusan duka waɗanda abin ya shafa farar hula ne.

    Ya ƙara da cewa a makon da ya gabata ma an samu irin wannan lamari a jihar Neja, inda mutane aƙalla 12 suka rasa ransu - yawancinsu ƙananan yara.

    A cewarsa, tun daga shekarar 2017 ake samun irin wannan lamari a arewa maso gabashin Najeriya musamman a jihar Borno inda a cewarsa,ana kai hare-hare da sunan yaƙi da Boko Haram.

  8. Sudan ta yi fatali da kiraye-kirayen yin bincike kan zargin aikata laifukan yaƙi

    Gwamnatin soji a Sudan ta yi watsi da kiran da Majalisar Ɗinkin Duniya haɗin gwiwa da Ƙungiyar Tarayyar Afirka suka yi kan a yi bincike kan zarge-zargen laifukan yaƙi da cin zarafi.

    Jami'ai sun ce Majalisar Ɗinkin Duniya da hukumar kare haƙƙin bil'adama ta AU ba su da hurumin gudanar da irin wannan binciken.

    Ba ya ga kiran a yi bincike, MDD da AU sun buƙaci a tsagaita wuta a kuma samar da hanyoyin kai jin ƙai zuwa Sudan ba tare da shamaki ba.

    Sai dai hukumomi a Khartoum sun yi watsi da sakamakon binciken tare da sukar AU kan haɗa kai da wasu hukumomin ƙasar waje da Sudan ba ta yi na'am da su ba.

    Ta ƙi bai wa tawagar MDD haɗin kai kasancewar an samar da tawagar ne shekaru uku da suka gabata.

    Binciken zai duba zarge-zargen cin zarafin da sojojin Sudan da dakarun RSF suka aikata a tsawon shekara huɗu na yaƙin.

  9. APC za ta fitar da sunayen ƴantakarar da za su fafata a zaɓen fitar da gwani

    Nentawe Yilwatda

    Asalin hoton, X/Nentawe Yilwatda

    Yau ake sa ran jam'iyyar APC mai mulki ta fitar da jadawalin sunayen mutanen da ta amince su tsaya takara a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar a wani ɓangare na cika ƙa'idar lokacin da Hukumar zaɓe INEC ta ware a gudanar da zaɓen.

    Hakan na nufin yau ne gwamnoni 30 zuwa 31 da sanatoci 88 da ƴanmajalisar wakilai 242 da babban mai ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu, Osifo Stanley da wasu 2,620 za su san makomarsu kan ko za su samu damar yin takara a zaɓen 2027 ƙarƙashin inuwar jam'iyya mai mulki ta APC.

    Shi ma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu da Sanata mai wakiltar Ogun ta gabas, Gbenga Daniel da tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo na daga cikin waɗanda jam'iyyar ta tantance.

    Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa jam'iyyar ta tantance ƴantakara 2,980 da ke neman kujerar shugaban ƙasa sai gwamnoni 28 da sanatoci 109 da ƴanmajalisar wakilai 360 da kuma ƴanmajalisar jiha 991.

  10. Trump ya soki yadda ake ba da rahoton yaƙin Amurka da Iran

    Shugaba Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kakkausar suka kan yadda kafafen yaɗa labarai ke bayar da rahotannin da suka shafi yaƙin Amurka da Iran, inda ya bayyana rahoton da ke cewa Iran na da ƙarfin soji a matsayin "cin amanar ƙasa".

    Saƙon da ya wallafa a shafinsa na dandalin Truth social ya zo ne sakamakon rahoton da jaridar New York Times ta wallafa cewa har yanzu Iran tana riƙe da kashi biyu bisa uku na makamanta masu linzami, kuma ta sake samun damar yin amfani da yawancin cibiyoyinta na ƙarƙashin ƙasa.

    Jaridar ta ce rahotannin da gwamnatin Trump ke fitarwa da ke nuna ta ɗaiɗaita sojojin Iran ya yi hannun riga da abin da hukumomin leƙen asirin Amurkan ke fada a bayan fage.

  11. Trump zai kai ziyara China karon farko cikin shekara 10

    Donald Trump da Xi Jinping

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump na hanyar tafiya birnin Beijing, a ziyarar farko da wani shugaban Amurka ya kai ƙasar China tun bayan da shi Trump ya je a shekarar 2017.

    Babban abin da zai fi mayar da hankali a tattaunawarsa da Xi Jinping shi ne taɓarɓarewar dangantakar kasuwanci tsakanin manyan ƙasashen biyu mafi ƙarfin tattalin arziki a duniya.

    Amma kafin ya bar birnin Washington, Mista Trump ya ce za su kuma tattauna kan Iran -- ko da yake ya dage cewa ba ya buƙatar taimakon China wurin kawo ƙarshen rikicin.

    Ya ce Muna da abubuwa da dama da za mu tattauna, mun riga mun gama da batun Iran, ko su yarda a cimma yarjejeniya ko kuma mu yi kaca-kaca da su, duk ta hanyar da aka bi za mu yi nasara.

    Ana tunanin mai yiwuwa shugaba Xi ya matsa wa Mista Trump lamba kan ya takaita sayar da makaman Amurka ga Taiwan.

  12. Barka da Safiya

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa na Kai Tsaye, barka da warhaka. Da fatan mun wayi gari lafiya.

    Shafin kamar yadda aka saba, zai kawo muku labaran da suka shafi yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi kan Iran da abubuwan da suka shafi Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

    Kuna iya zuwa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu rahotannin da ma kallon bidiyo.