Me ya sa Faransa ke son ƙulla sabuwar alaƙa da shugabannin Afirka a Kenya?

Asalin hoton, AFP via Getty Images
- Marubuci, Akisa Wandera
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
- Aiko rahoto daga, Nairobi
- Marubuci, Hafsa Khalil
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Bayan zarge-zargen da ake yi wa Faransa na tsoma baki irin na mulkin mallaka a wasu ƙasashen Afirka da take da doguwar alaƙa da su, ƙasar na ƙoƙarin faɗaɗa hulɗarta ta hanyar shirya taron shugabannin Afirka karo na farko a ƙasar Kenya, mai amfani da turancin Ingilishi.
Da yake jawabi a taron cigaban Afrika a Nairobi ranar Litinin, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da zuba jarin dala biliyan 27 a Afirka a fannonin inganta makamashi da fasahar zamani da AI da tattalin arziƙin teku da kuma noma.
Macron ya ce: "Afirka na samun ci gaba. Ita ce nahiyar da ta fi kowacce yawan matasa a duniya, kuma tana buƙatar jari domin ta dogara da kanta." Ya ƙara da cewa wannan zai samar da ayyukan yi kusan 250,000 a Afirka da kuma Faransa.
Ya kuma bayyana cewa Faransa ba wai kawai tana zuwa Afirka ne domin saka jari ba, har ma tana son manyan 'yan kasuwar Afirka su ma su zuba jari a Faransa.
Taron na kwanaki biyu yana da nufin faɗaɗa haɗin gwiwar Paris da ƙasashen Afirka tare da ƙulla yarjejeniyoyin saka jari, a lokacin da ake ganin ƙiyayya ga Faransa na ƙaruwa a ƙasashen da ta yi wa mulkin mallaka, musamman a Yammacin Afirka.
Tun bayan samun 'yancin kai a shekarun 1960, Faransa ta ci gaba da riƙe dangantaka ta tattalin arziki da siyasa da tsaro a da dama daga cikin ƙasashen da ta yi wa mulkin mallaka, lamarin da ya sa ake zargin ta da zame musu ƙarfen ƙafa.
Masanin siyasa daga Senegal, Gilles Yabi, ya shaida wa BBC cewa sabon ƙarni na 'yan Afirka na son "juya shafin mulkin mallaka da tasirin bayan mulkin mallaka."
Shi ma ministan harkokin wajen Kenya, Musalia Mudavadi, ya ce taron wata dama ce ga Afirka ta fara magana da murya ɗaya.
Ya ƙara da cewa gudanar da taron a ƙasar Afirka da ba ta amfani da Faransanci babban saƙo ne cewa bai kamata hulɗa tsakanin ƙasashe ta ta'allaka kawai kan harshen da ake amfani da shi ba.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ministan harkokin wajen Kenya, Mudavadi ya ce wannan wata "dama ce mai muhimmanci" ga Kenya da Faransa su kauce wa abin da ya kira matsalar bambacin harshe, waɗanda suka samo asali daga rarraba ƙasashen Afirka a matsayin masu amfani da Turanci, Faransanci ko Fotigalanci, lamarin da ya ce yana hana cikakkiyar haɗin kai a nahiyar.
Ya ƙara da cewa Kenya ta kasance muhimmiyar ƙasa wajen harkokin diflomasiyya da tarurruka na ƙasa da ƙasa. A cewarsa, taron zai tattauna batutuwan zaman lafiya da tsaro, sannan ya fi mayar da hankali kan haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin Afirka da sauran ƙasashen duniya ciki har da Faransa.
A makon da ya gabata ma, babban sakataren harkokin wajen Kenya, Korir Sing'oei, ya bayyana Kenya a matsayin ƙasar da ke taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kai da sasanta ƙasashen Afirka.
Ya shaida wa BBC cewa dangantakar Kenya da Faransa ta bambanta da ta wasu ƙasashen Yammacin Afirka saboda Kenya ƙasa ce da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka, don haka ba ta da irin tarihin mulkin mallakar Faransa da waɗancan ƙasashe suka fuskanta.
Shugabannin mulkin sojin da suka karɓe iko a Burkina Faso da Mali da Niger, waɗanda duk ƙasashe ne da Faransa ta yi wa mulkin mallaka, sun kori sojojin Faransa da ke taimaka wa yaƙi da masu tayar da ƙayar baya da masu iƙirarin jihadi a yankin, sannan suka karkata zuwa Rasha domin neman tallafin tsaro.
Kafin taron, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kare matakin rage yawan sojojin Faransa a Afirka, yana cewa ficewar sojojin ba "wulakanci ba ne" illa martani ne da ya dace da halin da ake ciki.
Macron ya ce: "Lokacin da muka gane cewa ba a buƙatar kasancewarmu bayan juyin mulki, sai muka fice."
Ya ƙara da cewa ya yi imanin cewa dole ne a bar waɗannan ƙasashe da shugabanninsu, har ma da masu juyin mulki, su zaɓi hanyar da suke son bi.
Babu ɗaya daga cikin shugabannin ƙasashen uku da ya halarci taron.
A yanzu ƙasar Djibouti ce kaɗai ke ɗauke da sansanin soja na dindindin na Faransa da ya rage a nahiyar Afirka, wanda ke bakin Bahar Maliya.
Masanin siyasa Gilles Yabi ya ce gudanar da taron a Kenya wata alama ce ta sauyin da ke faruwa a dangantakar tsakanin ƙasashen Afirka da Faransa.
Ya shaida wa shirin Newsday na BBC cewa wannan ba wai kawai martanin Faransa ba ne kan taɓarɓarewar dangantakarta da wasu ƙasashen Yammacin Afirka, amma wata hanya ce da ta daɗe tana ƙoƙarin samarwa.
A cewarsa, Faransa ta fahimci cewa dole ne ta nemi sababbin wuraren zuba jari da suka zarce tsoffin ƙasashen mulkin mallakarta da ke Yammaci da Tsakiyar Afirka.
Yayin da Kenya da Faransa duka ke neman ribar tattalin arziki daga haɗa kai wajen shirya taron, Paris na kuma ƙoƙarin nuna cewa har yanzu tana da muhimmanci a Afirka, a daidai lokacin da ƙasashe kamar China, Rasha da Turkiyya ke ƙara faɗaɗa tasirinsu a nahiyar.
Da yake jawabi a jami'ar Nairobi ranar Litinin, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Afirka na buƙatar zuba jari domin ta samu cikakken ƴanci da ikon dogaro da kanta.
Ya bayyana cewa nahiyar "ba ta buƙatar ci gaba da son jin shugabannin Turai suna faɗa mata abin da take buƙata."
Macron ya kuma ce ba ya son Faransa ta ci gaba da kallon Afirka a matsayin wani fili na musamman da take da cikakken iko a kai, inda 'yan kasuwanta ke ganin suna da damar samun kwangiloli kai tsaye kawai saboda ƙasashen na amfani da Faransanci.
Fiye da shugabannin ƙasashen Afirka 30 ake sa ran za su halarci taron, tare da attajirin Afirka, Aliko Dangote daga Najeriya, da sauran manyan 'yan kasuwa na Afirka, da kuma wakilan manyan kamfanonin Faransa.
Jakadan Faransa a Kenya, Arnaud Suquet, ya ce duniya na ƙara rikicewa da rarrabuwa, don haka ana buƙatar ƙarin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe.
Ya kuma ce ba wai yanzu ne Faransa ta fara sanin Kenya ba, yana mai nuni da cewa Faransa ta riga ta zama ta huɗu a jerin ƙasashen da ke zuba jari a Kenya.
A birnin Nairobi, manyan shagunan Carrefour suna nuna irin tasirin Faransa, inda ake sayar da kayan abinci da suka haɗa da kayayyaki na Faransa da giya da kayan kwalliya da kayan burodi tare da kayayyakin gida na Kenya.
Ga yawancin matasan Kenya, Faransa tana bayyana a matsayin ƙasa mai alaƙa da kasuwanci da abinci fiye da siyasa, abin da ya bambanta da yadda ake kallon ta a wasu tsoffin yankunanta na mulkin mallaka.

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Beverly Ochieng, wata babbar mai nazari a cibiyar da ake kira Control Risks, ta ce Faransa na sake tsara yadda take bayyana kanta a Afirka, tana kuma rage tsaurin nuna karfi da ta saba da shi a baya.
Ta ce maimakon dogaro da soja kaɗai, Faransa na ƙara amfani da kasuwanci, zuba jari da tafiya sannu a hankali domin ci gaba da kasancewa mai tasiri a nahiyar.
A cewarta, Faransa na amfani da sanannun kamfanoni da tasirin al'adu, da kuma matsayinta a Tarayyar Turai wajen inganta dangantakar tattalin arziki da ƙasashen Afirka.
A gefe ɗaya, gwamnatin Kenya na neman zuba jari a fannoni kamar gine-gine da makamashi da fasaha. Kamfanonin Faransa sun riga sun fara aiki a harkokin sufuri, kasuwanci da makamashi a ƙasar.
Akwai kuma tattaunawa kan haɗin gwiwa a fannin makamashin nukiliya, yayin da Kenya ke neman hanyoyin da za su ƙara ƙarfin makamashinta a nan gaba.
A watan da ya gabata, Nairobi ta amince da sabuwar yarjejeniyar tsaro ta shekaru biyar da Faransa, wadda ta haɗa da musayar bayanan sirri da tsaron teku a Tekun Indiya da kuma agajin gaggawa lokacin bala'i.
Ministan Harkokin Wajen Kenya, Mudavadi, ya ce ƙasashen biyu na kuma tattauna sabbin fannoni na haɗin gwiwa, yana mai cewa taron da ake kira "Africa Forward Summit" yana nuni ne da hasashen abin da zai faru a gaba, ba wai waiwayen baya ba.









