Me ya janyo cacar-baki tsakanin magoya bayan Atiku da Obi?

Asalin hoton, facebook/Atiku Abubakar, Peter Obi
A Najeriya cacar-baki ce ta kaure tsakanin ɓangaren tsohon mataimakin shugaban ƙasar Alhaji Atiku Abubakar da kuma ɓangaren tsohon ɗantakarar shugaban ƙasar Peter Obi kan batun shiyyar da ɗan takarar shugaban ƙasa zai fito daga jam'iyyun adawar ƙasar.
A baya baya nan ne, jam'iyyar hamayya ta NDC ta yanke shawarar tsayar da ɗan takararta na shugaban ƙasa daga shiyyar kudancin Najeriya a zaɓen 2027, abin da ɓangaren Atiku Abubakar ya yi zargin cewa dabara ce kawai ta tabbatar da nasara ga shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki.
Batun tsarin siyasar karɓa-karɓa a Najeriya, ba sabon abu ba ne, kuma duk lokacinda zaɓe ya ƙarato, sai an samu ce-ce-ku-ce tsakanin ƴan siyasar ƙasar musaman shiyyar da ɗan takarar shugaban ƙasa zai fito.
Kuma jiga-jigan ƴan adawa ne da suka kasa dunƙulewa waje ɗaya a yanzu ke musayar yawu bayan sabuwar jam'iyyar Peter Obi ta NDC ta yanke shawarar fito da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 daga shiyyar Kudu,
'Matakin NDC ya saɓa wa manufar adawa'
Sai dai wannan mataki ga dukan alamu bai yi wa ɓangaren tsohon mataimakin shugaban Najeriya daɗi ba inda ya ce ya saɓa wa manufar ƴan adawa ta ƙoƙarin kayar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Abdulrasheed Shehu Sharaɗa, ɗaya daga cikin masu magana da yawun tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ya shadai wa BBC cewa tsarin karɓa-karɓa ya fi tasiri ne a jam'iyya mai Mulki.
''Batun karɓa-karɓa ba za ka iya yin shi a cikin jam'iyya ba, sai idan kana da gwamnatin ne a hannunka, a ce wannan shiyya ta yi sai wata shiyya sai tayi'', in ji shi.
''Kuma babu inda ya zama cewa tsarin da jam'iyyar APC ta ke bi na shiya-shiya misali a ce wasu jam'iyyu shi ma wannan tsari za su bi'' in ji shi
Ya ƙara da cewa ya kamata a ba jam'iyyu damar amfani da tsarin da za su karɓi mulki.
''Duk jam'iyyu tsarin da ya kamata su bi, shi ne tsarin da za su karɓi mulki, tsarin da za su sami nasara, tsarin da za su kifar da gwamnati kuma shi ne tsari ingantacce''
Ya yi iƙirarin cewa wasu daga cikin jam'iyyun suna haɗa baki da gwamnati'
''Dama mun san wasu daga cikin jam'iyyun nan duk ƴan kasuwa ne, bakinsu ɗaya da gwamnati, ni dai ban ga wani ɗan kudu da zai iya shiga takarar da zai iya kayar da Bola Ahmed Tinubu ba'' in ji shi
'Abin da kawai ake nema shi ne haɗin kai'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shi kuwa ɓangaren Peter Obi ya ce ƙarfin magoya baya ne ya kai ga matakin da jam'iyyarsa ta NDC ta ɗauka kuma matakin na kan bisa tsarin neman haɗin kai.
Ibrahim Hassan Abdulkarim wani na hannun daman Peter Obi ya shaidawa BBC cewa matakin ya burgesu:
''Mun ga yadda aka sami haɗin kan matasa, wanda dama tafiya ce ta matasa, kuma shi ne mataki na farko wanda za mu warware wa ƴan siyasar ci da adini da ci da ƙabilanci zani a kasuwa''
''A fahimta a gane cewa kansu suke yi wa, sai zaɓe ya zo sai su ce Kudu ko Arewa amma a ƙarshe dai duk kansu su ke yi ma'', in ji shi.
Ya kuma musanta zargin da ake yi mu su a kan cewa su na ɓata aikin ƴan hammaya
''Ana cire ɗan takara wanda yake ci a yanzu da mutane da suke da magoya baya kuma abinda ake nema shi ne haɗin kai, shi Atiku idan ya zama shugaban ƙasa a samu haɗin kan arewa da kudu a kan cewa muna son mu fitar da wannan gwamnati''
Wannan shi ya fi amfani a kan cewa sai ka yi, ko da kai ɗan arewa ne kuma su ƴan kudu su na ganin cewa su ma ƴan Najeriya ne, yin adalci zai haɗa kan ƙasar sai ta ci gaba'' in ji shi.
Ga alama dai wasu na ganin cewa matakin NDC tamkar ta yanke hukunci Peter Obi ne zai kasance ɗan takararta na shugaban ƙasa kuma masu sharhi na ganin hakan na iya tasiri ga karkata alƙiblar sauran jam'iyyun adawa wajan fitar da na su ƴan takarar shugaban kasan.








