Me ya sa ake batun Dadiyata shekaru 7 bayan ɓatansa?

Asalin hoton, Dadiyata/X
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- Lokacin karatu: Minti 5
A makon da ya gabata ne ƴan Najeriya suka maida hankalinsu kan Abubakar Idris wanda aka fi sani da Dadiyata, bayan da wani makusancin ƙaramin ministan tsaron ƙasar Bello Matawalle, mai suna Muhammad Musa Kamarawa ya bayyana cewa a gabansa wasu ƴansanda biyu suka 'kashe' ɗan gwagwarmayar.
Wannan al'amari ya tayar da hankalin ƴan Najeriya, kasancewar sun daɗe suna son jin inda aka kwana dangane da ɓatan Dadiyata.
Shekaru bakwai kenan da matashin ya yi ɓatan dabo tun bayan da wasu mutane da ake kyautata zaton jami'an tsaro ne, suka ɗauke shi a ƙofar gidansa da ke unguwar Barnawa a jihar Kaduna.
Yanzu ƴan Najeriya suna ta kiraye-kirayen cewa ya kamata hukumomi su maida hankali, da ɗaukar mataki game da kalaman na Kamarawa domin gano haƙiƙanin abin da ya samu Dadiyata.
Abin da Kamarawa ya faɗa
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, a ranar Laraba, Muhammad Musa Kamarawa wanda tsohon mataimaki na musamman ne ga ƙaramin ministan tsaron Najeriya Bello Matawalle a lokacin da yake gwamnan Zamfara, ya yi zargin cewa wasu jami'an ƴansanda biyu sun harbe Dadiyata a gabansa.
"Ƴansandan da nake zargi, CSP Hussaini Gimba da CSP Hassan Gimba, sun bincike ni kuma sun sace min kuɗaɗe na da bincika gida na ba tare da izini ba. Sun yi barazanar 'kashe' ni kamar yadda suka 'kashe' Dadiyata da wasu a gaba na a Operation Yaki a Kaduna...," kamar yadda ya wallafa a saƙon nasa.
Da yake ƙara tabbatar da maganar, a ƙarƙashin saƙon da ya wallafa bayan wani ya tambaye shi "wai dan Allah da gaske a gabanka suka kashe Dadiyata...?", sai ya rantse cewar haka aka yi.
"Wallahi tallahi Hussaini Gimba ya 'kashe' shi," in ji Kamarawa.
Bugu da ƙari, Kamarawa ya ƙara barazanar sakin wasu bidiyoyi domin tabbatar da abin da ya faɗa.
"Bidiyo na nan na murza, ba zan sake shi ba, a kan yadda ka kashe Dadiyata..." kamar yadda Kamarawa ya faɗa a wani saƙon murya.
Ministan tsaro, Matawalle ya sha barranta kansa da Musa Kamarawa.
Martanin ƴan Najeriya
Wani fitaccen lauya a jihar Kano Barista Abba Hikima, ya fara shigar da ƙorafi ga Babban Sufetan Ƴansandan Najeriya kan zargin da buƙatar a gudanar da bincike.
A ƙorafin da ya shigar kwana guda bayan zargin, Barista Hikima ya ce: "Na miƙa buƙatar neman a gaggauta yin bincike game da zargin CSP Hassan da Hussaini Gimba da 'kisan' Dadiyata."
Lauyan ya ce akwai buƙatar hukumar ta yi gaggawar yin binciken domin gano gaskiya da wanke sunanta a idon duniya idan hakan bai tabbata ba, la'akari da girman zargin da ake yi.
Ya kuma buƙaci a ɗauki mataki kan duk wanda aka samu da hannu ba tare da la'akari da matsayinsa ba.
Martanin ƴansanda
A ranar Juma'a ne Babban Sufeton Ƴansandan Najeriya, Olatunji Disu ya ba da umarnin a yi bincike kan zargin da Musa Kamarawa, ya yi na cewa ƴansandan biyu -wa da ƙani - sun 'kashe' Dadiyata da wani mutum a Kaduna.
Da yake amincewa da karɓar ƙorafin na Barista Hikima, Babban Sufetan ya tabbatar da cewa tuni aka miƙa lamarin ga mataimakin kwamishinan ƴansanda mai kula da sashin sa ido domin ɗaukar mataki cikin gaggawa.
Cikin wata wasiƙar da babban jami'in ofishinsa, CF Lateef Adio Ahmed ya aika wa lauyan, ya tabbatar da cewa rundunar a shirye take don tabbatar da adalci.
Kwankwaso ya ɓara

Asalin hoton, DADIYATA/X
Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ya yi farin ciki da umarnin da Babban Sufeton Ƴansandan ya bayar na gudanar da bincike kan ɓacewar Dadiyata.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce yana da tabbaci kan matakin da Babban Sufetan ya ɗauka.
"Tun da aka sace shi a shekarar 2019, ni da ƴan'uwa muke ta addu'a tare da kira ga hukumomi da su gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a bacewarsa a gaban kotu," in ji Kwankwaso.
Ya bukaci ƴansanda su sa ido kan jami'an da ake zargi don hana yin katsalandan a binciken, inda ya yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da cewa an biya iyalan Dadiyata diyya kan halin da aka jefa su.
Dadiyata cikakken magoyin bayan Kwankwasiyya ne, kuma a nan ne ya fi yin suna saboda yawan kare muradun tsohon Gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso da yake yi.
Muna maraba da bincike - Amnesty
Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ita ma ta yi maraba da matakin da Babban Sufetan ya ɗauka, inda ta buƙaci a gudanar da cikakken bincike cikin gaggawa tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ƙungiyar ta ce tana fatan hukumomi su yi abin da ya kamata bayan waɗannan ƙarin bayanai da aka samu.
"Idan har an samu gamsassun hujjoji, dole a ɗauki mataki kan duk wanda ke da hannu a ciki, ko mai matsayinsa," in ji Amnesty.
Dama dai ƙungiyar Amnesty ta nemi hukumomi su yi bincike kan wasu kalamai da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi, inda ya ɓunta batun ɓatan Dadiyata.
El-Rufai ya fara kwarmata maganar
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise kwanakin baya, shi ne ya fara kwarmata batun waɗanda suka sace Dadiyata, inda ya ce shi bai san komai kan maganar ba.
El-Rufai ya ce daga bayanan da ya samu, ƴansanda ne suka tafi da shi.
Ya ƙara da cewa: "Wani ɗansanda da aka maida shi jihar Ekiti daga Kano ya shaida wa wani mutum cewa daga Kano aka turasu su sace Dadiyata, kuma yana jin ba daɗi game da hakan".
Ƴan Najeriya dai na ganin lokaci ne ya yi da abin ɓoye zai fito fili, dangane da wannan abu na take haƙƙin ɗan'adam da aka yi shekaru bakwai da suka gabata.
Ɓatan Dadiyata a watan Agustan 2019 na daga cikin batutuwan da ƴan Najeriya suka daɗe suna fatan ganin sakamakon bincike kan abin da ya faru da shi.
Dama kafin yanzu, ƴan Najeriya sun sha nuna yatsa kan El-Rufai dangane da ɓatan ɗan gwagwarmayar.
Wane ne Dadiyata?

Asalin hoton, Family
Asalin sunansa Abubakar Idris, sunan mahaifinsa Danjuma Yero, mahaifiyarsa kuma Fatima Abubakar.
Ana kiran sa Daddy a gida saboda yana da sunan kakansa na wajen mahaifiyarsa. Abokansa kuma suna kiran sa Dadiyata.
Matashi ne wanda ya yi fice a shafukan sada zumunta musamman ma a Twitter, inda yake da dubunnan mabiya.
Dadiyata malami ne a Jami'ar Tarayya ta Dutsinma da ke jihar Katsina kafin a sace shi.
Abubakar mutum ne mai yawan tsokaci a shafukan sada zumunta, inda a wasu lokuta yakan soki ayyukan wasu shugabannin siyasa da masu mulki.
Dadiyata na da mata ɗaya da 'ya'ya mata biyu.










