Abu 4 da za su fi ɗaukar hankali a ziyarar Trump zuwa China

- Marubuci, Anthony Zurcher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, North America correspondent
- Marubuci, Laura Bicker
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, China correspondent
- Lokacin karatu: Minti 5
An tsaurara tsaro a dandalin Tiananmen da ke tsakiyar birnin Beijing yayin da ake sa ran ziyarar Shugaban Amurka Donald Trump zuwa China, karon farko cikin shekaru.
An fara shirya wannan babban taron ne a ɓoye, kodayake daga baya China ta nuna shirya wa ganawar.
Gawanar za ta ƙunshi tattaunawa da liyafar cin abinci da ziyarar wuraren bautar China na tarihi, domin gudanar da addu'o'i.
Duka shugabannin biyu, Trump da Xi na fatan ziyarar za ta yauƙaƙa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.
Ita ce ganawarsu ta farko cikin shekaru maso yawa, tsakanin shugabanin da ke yi wa juna kallon hadirin kaji.

Asalin hoton, Getty Images
A baya Donald Trump bai ɗauki inganta dangantakar Amurka da China da wani muhimmanci ba.
Abin da ke gabansa shi ne yaƙin Iran, ayyukan soji a ƙasashen Yamma da kuma matsalolin cikin gida.
Amma kuma duka wannan ya sauya a makon nan.
Makomar kasuwancin duniya, ƙaruwar zaman ɗarɗar a Taiwan da kuma gasar bunƙasa fasahohi na daga cikin abubuwan da za su ɗauki hankali a lokacin ziyarar.
Ziyarar za ta ƙara inganta makomar haɗin kai - ko inganta fasaha - tsakanin ƙasashen biyu.
Matsayin Iran
China na ƙoƙarin zama mai shiga tsakani domin kawo ƙarshen yaƙin da a yanzu yake cikin wata na uku, inda ta bi sahun Pakistan kan wannan matsayi.
A watan Maris jami'ai daga Beijing da na Islamabad sun gabatar da wasu shawarwari biyar da nufin cimma yarjeniyar dakatar da yaƙin da kuma sake buɗe mashigar Hormuz.
Kuma a asirce jami'an Iran sun ci gaba da tattaunawa da takwarorinsu na China domin cimma yarjejeniyar.
Tattalin arzikin China na fama da matsalar bunƙasa, inda alƙaluman rashin ayyuka suka ƙaru.
Ƙaruwar farashin man fetur ya ɗan haifar da tashin farashin kaya da ake samarwa daga ɗanyen man fetur, da fannin tufafi da ma na robobi.
A wasu kamfanonin an samu ƙaruwar farashi da kashi 20 cikin 100.

Asalin hoton, Reuters
Yaƙin Iran ya tsaya wa China a wuya kasancewa daga ƙasar take samun mafi yawan man da take saye daga waje.
Sai dai, idan China ta zaɓi shiga yaƙin domin taya Amurka, dole ta buƙaci samun wata riba daga Washington.
Ziyarar da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya kai Beijing a makon da ya gabata na nuna irin tasirin da China ke da shi a Gabas da Tsakiya.
Amurka ta bibiyi ziyarar da kyau, ''Ina fatan China za ta faɗa masa abin da ya dace a faɗa masa,'' a cewar sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio.

Asalin hoton, VCG via Getty Images
Amurka ta yi ƙoƙarin shawo kan China kada ta hana sabon yunƙurin kwamitin tsaro na MDD na yin Allah wadai da hare-haren Iran kan jiragen ruwa a mashigar Hormuz bayan da Beijing ɗin da Rasha suka hau kujerar na-ƙi kan shawarar.
"Ina tunanin idan muna son dawo da Iran kan teburin tattaunawa, ta dole, yana da kyau Amurka ta amince China na da rawar da za ta taka,'' a cewar Ali Wyne, babban mai bincike da bayar da shawara a cibiyar nazarin rikice-rikice ta duniya.
A nasa ɓangare, Trump ya nuna bai damu da alaƙar China da Tehran ba.
Yayin da a baya-bayan nan Amurka ta ƙaƙaba wa wata matatar man fetur ɗin China takunkumin sayen mai daga Iran.
Makomar Taiwan
Gwamnatin Trump ta riƙa aika saƙonni masu cin karo da juna game da Taiwan.
A watan Disamban bara ta ayyana yarjejeniyar tallafin makamai na dala biliyan 11 ga Taiwan, wani abu da bai yi wa China daɗi ba.
Ba a jima ba kuma Trump ɗin ya nuna rashin damuwar Amurka na kare Taiwan, wadda China ke ɗauka a matsayin wani yanki nata.
"Yana ɗaukar ta a matsayin wani yankin China, don haka ya rage nasa kan abin da zai yi da ita", kamar yadda Trump ya wallafa a shafinsa na X.
A shekarar da ta gabata Trump ya saka harajin kashi 15% ga Taiwan, sannan ya zarge ta da sace wa Amurka fasahar ƙera ƙananan na'urori.
A makon da ya gabata, Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce Taiwan na daga cikin abubuwan da ziyarar Trump ɗin za ta tattauna.

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images
Batun kasuwanci
Kusan shekarar 2025 ta ƙare ne ana cacar-baki kasuwanci tsakanin Amurka da China, wani abu da ke iya girgiza tattalin arzikin duniya.
Trump ya riƙa ƙarawa da rage haraji kan China, wadda ita ce babbar abokiyar hulɗar kasuwancin Amurka, akwai ma lokutan da ya ƙara shi zuwa fiye da kashi 100.
China ta mayar da martani wajen rage fitar da ma'adanan ƙarƙashin ƙasa zuwa Amurka, sannan ta rage sayen kayan gona daga Amurka, wani abu da ya shafi manoma a manyan jihohin da suka zaɓi Trump.
An ɗan samu sassauncin batun ne bayan da Trump da Xi suka gana a shekarar da ta gabata a Koriya ta Kudu.
Don haka wannan ziyara za ta bai wa shugabannin biyu damar sake ingantan tattaunawa da cimma matsaya game da batun.
Shugaba Trump zai yi ƙoƙarin ganin China ta ƙara yawan kayan gonar da take saya daga ƙasarsa, haka ita ma China a nata ɓangare za ta so ganin Trump ya haƙura da aniyarsa ta sake ƙaƙaba mata haraji.
Fasahar AI
China na ƙoƙarin ganin ta shiga gaba ta fuskar fasahar ƙirƙirarriyar basira (AI) a duniya.
Ta riƙa zuba jari a fannin, musamman batun ƙera butum-butumi masu aiki irin na ɗan'adam.
Wannan na daga cikin abin da Xi ya bayyana da "sababbin dakarun aiki" waɗanda yake fatan za su inganta tattalin arzikin ƙasar.
Sai dai masu tsare-tsare na Amurka na ganin China ta saci fasahar Amurka ne wajen bunƙasa ci gabanta na cikin gida.
Hakan ya sa aka taƙaita fitar da wasu ƙananan fasahohin zuwa ƙetare, duk kuwa da adawa da hakan da wasu kamfanonin Amurka ke yi.

Asalin hoton, Reuters
Amurka za ta iya samun fasahar AI ta China da ba kasafai ake fitar da ita zuwa ketare ba, don haka ne ma ake yi mata laƙabi da mashigar Hormuz ɗin China, saboda a kowane lokaci za ta iya dakatar da fasahar.
China ta ƙware wajen ƙera butum-butumin da ke amfani da fasahar AI wajen gudanar da ayyukan da bil'adama kawai ke yin irin su.

Asalin hoton, VCG via Getty Images
Kuma ƙera irin waɗannan na buƙatar wasu kayayyaki ko na'urorin da Amurka kawai ke ƙera su.
Don haka ake ganin ganawar shugabannin biyu za ta taimaka wajen warware taƙaddamar ƙasashen game da fasahar da AI.

Asalin hoton, AFP via Getty Images










