Ko ana kama ƴan bindiga masu neman kuɗin fansa ta waya a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Najeriya na fama da matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, wanda ya haɗa da rikicin Boko Haram da na ƴan bindiga masu kisa da kuma satar mutane domin karɓar kuɗin fansa.
Ko a baya-bayan nan wasu ƴan bindiga sun sace wani tsohon babban jami'in sojan Najeriya, kuma rahotannin kafofin yada labarai na cikin gida sun bayyana cewa waɗanda suka sace shi sun gabatar da buƙatunsu ta hanyar wayar tarho.
Sai dai wani abu da ya daɗe yana rikitar da al'umma shi ne yadda irin wadannan ƴan bindiga ke shafe watanni suna waya da ƴan'uwan waɗanda suka sace domin sasantawa kan kudin fansa da za a biya.
Haka nan wani abu da ya yawaita a baya-bayan nan shi ne yadda wasu da ake zargin ƴan fashin daji ne ke yin bidiyonsu a daji suna yaɗawa a shafukan sada zumunta na tiktok, ko ma "bayyana kai-tsaye a bidiyoyi na tiktok" domin kare kansu.
"Babu shakka ƴan bindiga na amfani da yanar gizo wajen nuna bajinta da ayyukan da suke yi," in ji masanin tsaro a yankin Sahel kuma shugaban kamfanin Beacon Consulting, Kabiru Adamu.
Amma me ya sa ba a yawan jin labarin cewa an kama irin wadannan ƴan bidiga masu magana da ƴan'uwan wadanda suka sace ko kuma suke bayyana a bidiyoyin tiktok?
Kafofin yaɗa labarai na cikin gida sun ruwaito tsohon babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Tukur Burutai na cewa "ƙasar na da ƙwarewar da za ta iya bibiyar ƴan bindiga".
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"A wannan zamani yanar gizo da kafafaen sada zumunta kafafe ne na tattara bayanai (intelligence) a bayyane (OSINT) ko kuma 'Open Source Intelligence', kuma ya kamata a ce kowane ɓangare tsaro na amfani da shi".
Masanin ya bayyana cewa ƙasashen duniya da dama kamar Amurka da sauran ƙasashen Turai, sun riga sun fitar da tsarin tattara bayanai ta wannan fage na intanet.
Sai dai ya ce a ƙasashe irin su Najeriya akwai rashin yarda daga hukumomin yaƙi da tsaro wajen amfani da tsarin duk da cewa duniya ta rungume shi.
Amma ya ce a baya-bayan nan Najeriya ta fara ɗaukar matakan bin wannan tsari "sai dai ba su fara amfani da shi tare da saka shi cikin tsarin yadda ya kamata ba".
Ya bayyana cewa a misali, "akwai ƙarancin bayani kan ko an taɓa amfani da wannan tsarin tattara bayanai wajen kama masu laifi, amma kuma akwai shaidun da ke nuna cewa an yi amfani da bayanan yanar gizo wajen kama mutane da suka bayyana ra'ayoyin da suka saɓa wa hukumomi."
Shin gwamnati na sauraron bayanan mutane?
Ɓangare mai muhimmanci, ko kuma a ce mataki na farko wajen amfani da wannan tsari na kama masu laifi ta hanyar fasahar sadarwa shi ne tattara bayanai.
Kabiru Adamu ya ce "babu shakka gwamnati na da na'urori na bibiyar bayanai a wasu sassa daban-daban nata."
"Idan aka yi amfani da tsarin tattara bayanai ta hanyar na'ura, da taswira , sai kuma wasu dabaru waɗanda ba zan so na faɗe su ba saboda dalilai na tsaro, ana iya gano inda wanda ya yi amfani da wata kafa ta yada labarai yake," kamar yadda masanin ya bayyana.
Me ya sa ba a cika kamo ƴan fashin daji ba ta hanyar waya?
Ma'aikatar sadarwa: "Ina ganin babban abin da ke kawo cikas ga amfani da wannan tsari shi ne rashin kyakkyawan amfani da ma'aikatar sadarwa da ƙirƙire-kirkire, wato 'ministry of communication, innovation and digital economy' a cikin harkar tsaro tsundum.
Masanin ya ce wajibi ne Najeriya ta shigar da ayyukan ma'aikatar cikin tsarin yaƙi da tsaro na ƙasar.
Ma'aikata ce ta gwamnati wadda aka ɗora wa alhakin bunƙasa ɓangaren sadarwa musamman na zamani da kuma tafiyar da shi a faɗin ƙasar.
Rashin kayan aiki: Ya bayyana cewa ana buƙatar kayan aiki da za su bai wa jami'an tsaro damar tashi cikin sauri domin zuwa inda mai laifi yake idan an gano shi.
Rashin mallakar hanyoyin intanet: Masanin ya bayyana cewa ƙasashe ba su ne ke da ikon bayar da umarni ko sarrafa kamfanonin sada zumunta da na intanet ba. Ya ce wannan ne muhawarar da ake yi kan wane ne ke da alhakin abin da ke faruwa a shafukan internet, wato 'Digital accountability'.
Ya ce ba Najeriya kawai ba, yawancin ƙasashen Afirka na da rauni wajen yin tasiri kan ayyukan shafukan sada zumunta.
Sai dai ya ce akwai lokacin da Najeriya ta yi yunƙurin magance hakan ta hanyar tursasa wa shafin tuwita kan yadda yake gudanar da ayyukansa a ƙasar, amma masanin ya ce lamarin bai yi nasara sosai ba.
Rashin mayar da hankalin gwamnati: "A fahimtarmu abin da ya fi famun ƴan siyasa shi ne idan yara sun zage su ko sun taɓa su, ana amfani da irin wadannan dabaru wajen kamo su, amma babu irin wannan ƙoƙari a ɓangaren tsaro," a cewar Adamu







