Tsohon ɗan wasan Liverpool da Newcastle Keegan ya rasu

Asalin hoton, BBC Sport
Tsohon ɗan wasan Ingila kuma koci Kevin Keegan ya rasu yana da shekara 75.
Rasuwar tasa na zuwa ne bayan sanar da kamuwa da ya yi da ciwon Kansa da ta kai mataki na huɗu.
Daya daga cikin 'yan wasan Ingila da suka fi samun kyautuka a duniya, Keegan ya buga kwallo a Scunthorpe United, Liverpool, Hamburg, Southampton da kuma Newcastle lokacin da yake kan ganiyarsa.
Daga baya ya zama kocin Newcastle da Fulham da Ingila da kuma Manchester City.
A watan Yuni ne Keegan ya bayyana cewa yana fama da kansa a mataki na huɗu, wanda shi ne mataki mafi haɗari da ke nuna kansar ta bazu zuwa wasu sauran sassan jikinsa.



























