Me ya sa ake nuna wa tawagar ƙwallon ƙafar Argentina tsana?

Asalin hoton, Getty Images
Ko shakka babu kwarewarka a irin wasan da kake bugawa da abokan hamayya kan iya janyo maka ƙaruwar masu fatan ganin faɗuwarka.
Wani hali da ake ganin ƙasar Argentina da ta ci kofin duniya sau uku ta tsinci kanta ciki.
Makiya wani lokacin ba dole sai na kusa ba na nesa ma ana tattaro su a zo da su ba tare da lura ba.
Kuma lokacin da tawaga ta ƙasaita take iya doke kowa kamar yadda Argentina ta yi a Kofin Duniya na 2026, hakan ka iya tara mata maƙi masu yawa suma.
Kan haka BBC ta tattauna da masana harkokin kwallon ƙafa domin jin ina wannan adawa da ake nunawa Argentina ta samo asali, yanzu ne aka fara mata ko kuma dama ta gaje su ne tun daga lokacin magabata irinsu Maradona.
Hanyar Argentina zuwa wasan ƙarshe
Fifa ce ke tsara yadda jadawalin wasannin gasar duniya ke gudana, bayan an kammala karkaɗe wajen raba rukuni.
Abin da ya fara jan hanakalin masu bibiyar wasan kwallon ƙafa shi ne yadda aka raba jadawalin gasar ta yadda Messi ba zai haɗu da ko ɗaya daga cikin ƙasashe 10 na jadawalin Fifa ba.
Sai a wasan kusa da na ƙarshe ne suka fafata da Ingila suka doke ta da ci biyu da ɗaya.

Asalin hoton, FIFA
Mafi yawan ƙungiyoyi masu ƙarfi da ke jadawalin Fifa sai aka tara su a wuri guda irinsu: Portugal, Jamus, Faransa, Sifaniya da dai sauransu.
Wannan ya janyo fusata daga masu adawa da Argentina tare da zargin cewa Fifa ta ta yi hakan ne da sani don ta taimakawa ƙasar.
Takun da Messi ya yi a wasan Aljeriya

Asalin hoton, Getty Images
Tun a wasan farko da Argentina ta buga na Gasar Kofin Duniya mutane suka suka tare da nuna cewa Fifa na ɗauk kai ga ƙasar da kuma 'yan wasanta.
Kyaftin ɗin ƙasar Lionel Messi ya taka ɗan wasan Algeria a wasan da ya ci kwallo uku rigis, irin takun da ake korar duk wanda ya yi, amma shi ko katin gargaɗi ba a bashi ba.
Wannan ya janyo surutu daga masu sharhi da masu bibiyar wasanni a faɗin duniya.
Duk da cewa an buga wasan ne cikin dare amma saboda Messi da kuma rashin nisar da gasar ta yi ana ɗaukinta miliyoyin mutane ne a faɗin duniya suka kalli wasan.
Alƙalin wasa bai je ya duba na'urar da ke taimaka masa ba, haka masu kula da ita ba su kira shi domin dubawa ba.
A gasar, irin ƙetar da Messi ya yi ba a bashi komai ba, irinta ɗan wasan gaban Amurka Folarin Balogun ya yi aka ba shi jan kati kai tsaye.

Asalin hoton, Getty Images
Ce-ce-ku-cen wasan Masar

Asalin hoton, Getty Images
Wasan da masar ta fafata da Argentina na daga cikin wasannin da suka bar baya da ƙura.
Saboda idan mai karatu bai manta ba, sai da masar ta ci 2-0, amma aka farke aka ƙara mata cikin ƙanƙanin lokaci.
Masar ta ci kwallo ta uku ta hannun Zico a wata kora mai kyau da suka samu amma daga ƙarshe aka kashe kwallon, da zargin an taka Martinez kafin a kwace kwallon a ci Argentina.
Masana harkokin alƙalanci wasa a duniya sun samu rabuwar kai, wasu da dama na cewa ba a yi komai ba, wasu kuma na cewa an taka Martinez gabanin ɗaukar kwallon da aka ci.
Sai dai an yi irinsa a wasan Ingila da Argentina, Messi ya taka Spance kafin a ci kwallo ta biyu da fitar da Ingila da ita.
Dabi'un rikici

Asalin hoton, Getty Images
Messi da sauran 'yan wasan Argentina sun riƙa nuna baƙin ɗabi'u da ba a saba gani ba a harkokin kwallon ƙafa, doke-doke, yawan faɗa da rashin hakuri.
A wasan da Argentina ta doke Switzerland an ga Messi na nuna yatsa ga alƙalin wasa Joao Pinheiro ɗan ƙasar Portugal yana yi masa gargaɗin ya girmama shi.
Jiridu da yawa sun rawaito cewa laɓɓan Messi na gayawa alƙalin wasan ne cewa "ya kamata kana girmama ni, na cancanci girmamawa" sai dai BBC ba ta tabbatar da sahihancin kalaman ba.
Romero na daga cikin 'yan wasan da suka riƙa buga wasa tamkar yaƙi a gasar, ko kuma idan sun yi nasara kan wata ƙasa su je su yi ta ihu gaban abokan wasan nasu domin cusa musu damuwa.
Dan wasan da ke taka leda a Ingla ya yi irin wannan murnar ne a gaban mai tsarin ragar Ingilan, sai dai bai ce masa komai ba.
Tutar rikici Falklands na 1982

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ban da wasan ƙarshe na Kofin Duniya babu wani wasa da Argetina ta yi da babbar tawaga sai wasan Ingila, kuma shi ma kamar sauran wasanni ya bar baya da rikici.
Wasa ne wanda a tarihi yake da daɗaɗɗiyar gaba, kuma ake sabunta ta duk lokacin da za a yi shi.
A shekarun 1980 an yi yaƙin kwana 74 kan rukunin tsuburan Falklands, tsakanin Argentina da Burtaniya.
Tsibirin da ke kusa da Argentina duka ɓangarori biyun sun yi iƙirarin mallakarsa, abin da yakai su ga yaki da kashe sojojinsu.
Dab da za a fara wasan, mataimakiyar shugaban ƙasar Argentina ta wallafa wani saƙo a shafinta na Intanet, inda ta yi magana kan tsibirin.
Bayan Aregntina ta yi nasara 'yan wasanta sun ta ɗaga tutar wadda fassarar ke nufin "tsiburin Falklands na Argentina ne". Duk da cewa sun kwana da sanin hakan ba daidai ba ne amma sun yi.
Rahotanni sun ce Fifa za ta ɗauki mataki kan wannan abun da suka yi, ta hanyar hukunta su.
Ko a 2014, Fifa sai da ta ci tarar Hukumar Kwallon Ƙafa ta Argentina fan dubu ashirin 20,0000 bayan ta ɗaga tuta makamanciyar wannan a wani wasan sa da zumunta da suka yi da Slovenia.
Wasan ƙarshe na Kofin Duniya

Asalin hoton, Getty Images
Amma abubuwan suka faru a wasan ƙarshe na gasar kofin duniya ka iya haifarwa da ƙungiya bakin jini da tarin maƙiyan da ba a yi zato ba in ji Mu'azu Maikanti, masani kan dokokin kwallon ƙafa kuma mai sharhi kan wasanni.
Yan wasan Aregentina Parades da Molina da Almada da kuma mai taimakawa koci Roberto Ayala duka an gansu da hannu cikin rikicin lokacin da Spain ke murnar kammala gasar da ta ci 1-0.
An ga Parades ya shaƙi wuyan Eric ɗan wasan Spain da kuma kayar da Gavi yana yunkurin taushe shi yayin da shi ma Almada ya taimaka masa.
Parades bayan ya kayar da ɗan wasan na Barcelona ya nemi ya dake shi a fuska.
Tuni Fifa ta kafa kwamitin bincike kan lamarin, tare da alƙawarin tara mai tsoka kan duk wanda aka kama da laifi.
"Wannan ba ɗabi'ar kirki ba ce, kuma mai yinta ba zai gaza samun ɗumbun maƙiya ba. Sun ci wasu da yawa a baya suka zo wasan ƙarshe, to mene ne illa idan su ma an cinye su? Kamar yadda Maikanti ya yi bayani
'Messi ba shi da mu'amala mai kyau da mutane'

Asalin hoton, Getty Images
Bashir Gentile da ya kalli gasar Kofin Duniya ta 1998 a Faransa yace "ba a san Argentina da wannan ta'ada ba ta neman tashin hankali a wasa, amma sabon salon da ta ara ta yafa zai kaita ya baro.
"Babban ɗan wasan Argentina Messi ba shi da mu'amala mai kyau da magoya bayansa da sauran 'yan wasa da ake hamayya," in ji Bashir Gentile.
Yace mutum ne mai 'jiji da kai' babu wanda yake kusantar shi kamar yadda ake kusantar wasu 'yan wasan da suka yi shuhura a duniya.
Kuma daga nahiyarsu ta Kudancin Amurka an cinye kowa sai su kaɗai sun fuskanci wannan adawar ta cikin gida itama.
Gentile ya ce an cire Brazil an cire Columbia da Uruguay su kadai ne suka yi saura daga nahiyar, don haka acewarsa za su fuskanci adawar cikin gida.
'Yawan cin kofina a duniya'

Asalin hoton, Getty Images
Wani mai sharhin Mubarak Sadiq Abubakar cewa ya yi babu mamaki idan Argentina ta tara maƙiya, saboda abubuwan da ta cimma ba za su bar mutum ya zauna ba tare da magauta ba.
"Argentina ta fi kowacce ƙasa cin kofina a duniya, ta ci kofina 23 jimmila, wadda ke kusa da ita Brazil ce da kofina 20," in ji Mubarak.
Gabarsa da Cristiano Ronaldo tana cikin abubuwan da suka kara masa bakin jini duk abin da zai yi a wajen abokan gabarsa ba zai zama abin yabo ba, duk kuma abin da ya yi na ɓaci zai zama abin zambo a gare shi.
Ka zalika salon wasansu da suke bugawa da ƙarfi da sa jiki yana daga cikin abin da yake sa wasu na jin hausahin su.
'Goyawa Argentina baya da Netanhayu ya yi'
Bakin masanan biyu ya zo ɗaya wajen yarda da cewa baya ga adawar kwallon ƙafa akwai kuma siyasar duniya da ta shafe su.
"Rikicin da Firaministan Isra'ila ke ciki ne ke neman shafarsu, ganin cewa yana faɗa da ƙasashe da dama kuma ya fito ƙarara ya nuna goyon bayansa ga Argentina, don haka sai mutane suke jin haushin ƙasar," in ji Gentile.
Shi kuwa Mubarak Sadiq cewa ya yi "A wasan ƙarshe ko wa ya san Spain ba ta tare da Firaiministan, wannan ya sa mutane suka nuna goyon bayansu ga Spain kai tsaye da adawarsu ga Argentina".












