Ƴansanda na neman matashin da ya kutsa taron masu neman jinsi a Jamus

Asalin hoton, Getty Images
'Yan sanda a birnin Berlin na Jamus sun shafe dare suna neman direban wata mota da ta kutsa cikin taron mutane a ɗaya daga cikin manyan tarukan masu neman jinsi daya a Turai, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mace daya da jikkata mutum 16.
Wakilin BBC ya ce 'yansanda na amafani da jirgin sama mai saukar ungulu da fitilu masu haske a neman wanda ake zargin a cikin duhun wannan waje na tsakiyar Berlin.
Hukumomi sun ce babban wanda ake zargin matashi ne mai shekara 21 mai suna Abdul B, kuma yana da alaka da masu tsattsauran ra'ayi na ikirarin jihadi.
'Yan sanda sun kuma ce an caka wa wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa wuƙa bayan aƙalla mutum ɗaya daga cikin maharan ya fito daga cikin motar kafin ya tsere daga wurin.
Dubban mutane ne suka halarci taron na shekara-shekara na masu rajin kare haƙƙin masu neman jinsi daya, a babban birnin na Jamus, gangamin da ake wa lakabi da Christopher Street Day.
















