Manchester United na shirin raba gari da Rashford, Madrid na nazarin komawa ga Mourinho

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ba ta da shirin mayar da ɗan wasan gaban Ingila Marcus Rashford, mai shekara 28, cikin tawagar ƴan wasanta na farko a kakar wasa mai zuwa idan ya dawo daga zaman aro da ya ke yi a Barcelona. (Sun)
A halin yanzu, Rashford ya kuduri aniyar ci gaba da taka leda a kulob ɗin na Sifaniya inda zai ci gaba da wasa a ƙarƙashin horaswar Hansi Flick, duk da rashin tabbas kan makomarsa na dogon zango a United. (TeamTalk)
Real Madrid na tunanin dawo da tsohon kociyan ƙungiyar Jose Mourinho, amma ƙungiyarsa ta Benfica ta na son ya ci gaba da zama na aƙalla kaka ɗaya. (AS)
Arsenal da Barcelona na zawarcin ɗan wasan tsakiya na Chelsea Enzo Fernandez, mai shekara 25, duk da cewa suna fuskantar hamayya daga Manchester City kan ɗan wasan na Argentina. (Teamtalk)
Newcastle za ta sanya sayen sabon mai tsaron gida a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da za ta sa a gaba a bana, inda ta ke sanya ido kan golan Manchester City da Ingila James Trafford da kuma Bart Verbruggen na Brighton da Netherlands. (Telegraph)
Arsenal na shirin sayar da manyan ƴan wasa a kasuwar musayar ƴan wasa ta bana duk da cewa ta samu sama da fam miliyan 120 a kuɗaɗen kyaututtukan Uefa sakamakon nasarar da ta yi na kai wa wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai. (Sky Sports)
Brentford na ƙoƙarin ɗauko ɗan wasan bayan Austria Jannik Schuster, mai shekara 19 daga Red Bull Salzburg a kan kuɗi fam miliyan 17. (Athletic)
Tottenham na zawarcin ɗan wasan Brighton Jan Paul van Hecke, mai shekara 25, duk da cewa Chelsea da Liverpool su ma suna harin ɗan wasan na Netherlands. (TeamTalk)










