Yadda sojojin Najeriya suka ceto kusan mutum 400 daga hannun Boko Haram

Dakarun Sojin Najeriya

Asalin hoton, NIGERIAN ARMY

Bayanan hoto, Dakarun Sojin Najeriya
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Bayanai na ci gaba da fitowa, kan yadda dakarun rundunar hadin gwiwa ta yaki da masu tayar da kayar baya a Arewa maso Gabashin Najeriya, wato Operation Hadin Kai, suka ceto mutum 360 da aka yi garkuwa da su daga wani babban sansanin 'yan tada kayar baya da ke boye a cikin tsaunukan Mandara da ke kudancin jihar Borno.

Hukumomin soji sun bayyana wannan aiki a matsayin daya daga cikin manyan nasarorin ceton mutanen da aka yi garkuwa da su a yankin Arewa maso Gabas cikin 'yan shekarun nan.

Mutanen da aka ceto sun hada da maza da mata da yara, wadanda ake zargin mayakan kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jihad, wani bangare na kungiyar Boko Haram, suka yi garkuwa da su.

A cewar rundunar sojin, an sace mutanen ne daga yankuna daban-daban musamman a yankin Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza, inda aka rika tsare su cikin mawuyacin hali a cikin sansanin mayakan da ke cikin tsaunukan.

Tsaunukan Mandara da suka yi iyaka da Najeriya da Kamaru sun dade suna zama mafakar 'yan tada kayar baya saboda wahalar shiga yankin da kuma yanayin sarkakiyar wuraren.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Laftanar Kanar Haruna Mohammed Sani ya fitar ranar Lahadi, rundunar sojin ta ce nasarar ta nuna yadda ayyukan tattara bayanan sirri ke kara taimakawa wajen yaki da masu tayar da kayar baya.

Ya ce an kaddamar da aikin ceton ne bayan shafe makonni ana tattara bayanan sirri, da gudanar da bincike a boye da kuma tsara yadda za a gudanar da farmakin.

Rundunar ta ce an fara aikin ne bayan hukumomin tsaro sun samu sahihan bayanai kan wurin da aka tsare mutanen da kuma hanyoyin kaiwa ga sansanin mayakan da kuma yadda ake shigarsa.

Dakarun sojin Najeriya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dakarun sojin Najeriya
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sanarwar ta bayyana cewa jami'an rundunar sun yi amfani da bayanan sirrin da suka samu, da kuma na su hanyoyin na sa ido da bincike, ciki har da amfani da jiragen sama marasa matuka da kuma jami'an leken asiri a wurare masu nisa.

Ta ce ta hanyar ci gaba da sanya ido a yankin ne kwamandojin rundunar suka samu cikakken bayani kan yanayin wurin, da matsugunan mayakan, da tsarinsu na kariya da kuma halin da wadanda aka yi garkuwa da su din ke ciki.

Sanarwar ta ce wannan tsari na tattara bayanan sirri ya ba rundunar damar gano wuraren da mayakan suka fi rauni tare da rage hadarin da za a iya jefa wadanda aka yi garkuwa da su din yayin aikin ceto.

A cewarta, bayan tabbatar da bayanan da aka samu ne, dakarun runduna ta musamman ta sojin Najeriyar suka kaddamar da farmaki ta bangarori daban-daban domin killace sansanin da hana mayakan samun taimako ko kuma tserewa.

''A cikin duhun dare, dakarunmu suka kutsa cikin yankin yayin da wasu sojojin suka toshe hanyoyin shiga da fita da ke kewaye da tsaunukan'' inji sanarwar.

Hukumomin sojin sun ce farmakin ya zo wa mayakan ba zato ba tsammani.

Sanarwar ta ce saboda saurin farmakin da kuma yadda aka tsara shi, mayaka da dama sun gudu daga matsugunansu zuwa wasu tsaunukan da ke kusa, yayin da wasu suka mika wuya ga sojojin.

Sai dai duk da nasarar aikin, rundunar ta ce jarirai biyu sun rasu yayin da ake kwashe wadanda aka ceto.

A cewar sanarwar, jariran sun mutu ne sakamakon gajiya da kuma mawuyacin halin da suka shiga a lokacin da suke tsare a hannun mayakan, da kuma wahalar da ke tattare da ficewa daga yankin mai duwatsu.

Sauran mutanen da aka ceto kuwa an kwashe su cikin koshin lafiya, kuma yanzu haka suna samun kulawar likitoci, taimakon jin kai da kuma tallafin lafiyar kwakwalwa.

Kwamishinan watsa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Borno, Muhammad Tar, ya tabbatar wa BBC labarin ceton mutanen.

Ya kuma ce za a gudanar da bincike da tantance wadanda aka ceto domin tabbatar da halin da suke ciki kafin daga bisani a mayar da su ga iyalansu.

A cikin watannin baya-bayan nan, rundunar ta Operation Hadin Kai, ta kara kaimi wajen kai hare-hare kan sansanonin mayakan Boko Haram, da hanyoyin samar musu da kayan aiki da kuma hanyoyin jigilar kayayyaki a jihohin Borno, da Yobe da Adamawa.

Rundunar ta ce ceton mutum 360 da aka yi garkuwa da su ya nuna yadda hadin kai tsakanin hukumomin tsaro ke kara karfi, da kuma kudurin rundunar sojin Najeriya na kare rayuka da dukiyoyin al'umma tare da tabbatar da zaman lafiya a yankunan da rikici ya shafa.

Ta kuma tabbatar wa 'yan Najeriya cewa ana ci gaba da gudanar da wasu ayyuka domin bibiyar mayakan da suka tsere, da rusa sauran cibiyoyin da ke tallafa musu da kuma hana sake faruwar irin wadannan hare-hare a yankin Arewa maso Gabas.