Alƙawura 5 da Tinubu ya yi wa an Najeriya, shin ya cika?

Tinubu

Asalin hoton, PRESIDENCY NG

Lokacin karatu: Minti 7

A yanzu da aka fara nisa wajen shirye-shiryen babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027, ƴan Najeriya da dama sun fara tambayar shin me jiya ta yi domin ganin shirin da za su yi domin gobe.

Tuni dai Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya mallaka fom na sake takarar shugabancin ƙasar domin mulki a wa'adi biyu.

A watan Janairu ne dai za a sake fafata zaɓen shugaban ƙasa, inda Bola Tinubu ke neman sake samun nasara kan jam'iyyun da suke faɗi tashin ganin sun hana shi komawa mulki bayan wa'adinsa na farko.

Wannan ya sa BBC ta waiwayi wasu muhimman alƙawura da shugaban ya yi a farkon mulkinsa, da kuma yin tankaɗe da rairaya kan ko ya samu nasarar sauke nauyin da ya ɗauka.

Wutar lantarki

A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafofin sadarwa na zamani a shekarar 2023, Bola Tinubu ya bayyana cewa duk yadda zai yi, sai ya yi domin tabbatar da cewa wutar lantarki ta wadata a ƙasar.

Ya bayyana haka ne a wajen wani taron da ƴan kasuwa kafin zaɓen, inda ya ce, "Idan har ban cika wannan alƙawarin ba, idan na dawo neman wa'adi na biyu, kada ku zaɓe ni, sai dai idan na kawo muku hujjoji gamsassu na dalilan da suka hana ni cika wannan alƙawarin," in ji Tinubu a bidiyon.

A watannin baya ne dai kakakin jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya yi tariyar saƙon na Tinubu, inda ya yi tambayar ina wutar take?

Bolaji ya bayyana a jawabin cewa tun bayan da Tinubu ya hau mulki, babban layin lantarkin ƙasar ya katse sau aƙalla 12, sannan duk da haka kuɗin lantarki ya ƙaru da kusan kashi 240.

Sabon ministan makamashi na Najeriya, Joseph Olasunkanmi Tegbe ya bayyana a lokacin da ake tantance shi cewa gyara ɓangaren makamashi na buƙatar, sannan ya ƙara da cewa zai yi bakin ƙoƙarinsa.

Sai dai tun kafin nan, a ranar 6 ga watan Afrilun 2026, Bola Tinubu ya amince da biyan basussukan da ɓangaren makamashi ke bi domin inganta ayyukansu da samar da wadatacciyar wutar lantarki.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin Bayo Onanuga ya fitar, ya ce gwamnatin ta amince da biyan naira tiriliyan 3.3 domin bashin da ya taru tsakanin Fabrailun 2015 zuwa Maris na 2025, inda ya ce za a biya kuɗin a hankali a hankali ne.

Sanarwar ta ce biyan bashin ne zai sa kamfanonin lantarki su inganta ayyukansu, wanda hakn zai sa a samu wutar lantarki ta wadata a ƙasar.

Tsaro

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kusan za a iya cewa babbar matsalar da Tinubu ya gada ita ce ta rashin tsaro a faɗin ƙasar, musamman harkokin ƴanbindiga a arewa maso yamma.

Sai dai har yanzu wasu ɓangarorin ƙasar na cigaba da fama da matsalolin tsaro, inda lamarin ya faɗaɗa zuwa arewa ta tsakiya. Yanzu haka ƙasar na fama da matsalolin tsaro kamar haka:

  • Masu iƙirarin jihadi
  • Ƴanfashin daji/Masu garkuwa da mutane
  • Rikicin ƙabilanci
  • Masu fafutikar ɓallewa daga Najeriya
  • Masu fasa bututu don satar man fetur

Wani abun da ke ƙara ɗaga hankalin ƴan ƙasar shi ne sabon salon da mahara suka ɗauka a ƙasar na kai hari kan sansanonin sojoji da kwantar ɓauna, da kuma amfani da jirage marasa matuƙa, lamarin da masana suka bayyana da matsala babba.

An shiga tashin hankali a ƙasar a lokacin da a cikin kusan mako biyu aka yi garkuwa da ɗalibai da masu ibada, inda aka sace ɗalibai a jihar Kwara da Kebbi da Neja, sannan aka yi garkuwa da wasu mutane a jihohin daban.

Lamarin ne ya kai har majalisar Amurka ta sa baki, lamarin da ya kai har Amurka ta kai hari a ƙasar.

Sai dai gwamnatin Tinubu ta sha nanata cewa tana ƙoƙari sosai wajen daƙile matsalar.

A ranar Laraba 26 ga watan Nuwamba ne shugaban ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a faɗin ƙasar, inda ya bayar da umarnin a ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Daga cikin muhimman matakan da ya bayar da umarni a ɗauka, akwai:

  • Ƴansandan jihohi: Shugaban ya umarci majalisar dokoki su yi gyara a kundin tsarin mulkin ƙasar domin ba jihohin da ke son kafa ƴansanda damar aiwatarwa.
  • Ɗaukar ƙarin ƴansanda 20,000: Ya ce a ɗauki sababbin ƴansanda 20,000, ƙari a kan guda 30,000 da ya fara amincewa a ɗauka.
  • Amfani da sansanonin NYSC: Tinubu ya ce a yi amfani da sansanonin horar da masu yi wa ƙasa hidima wajen horar da sababbin ƴansandan da za a ɗauka.
  • Tsaron gandun daji: Haka kuma shugaban ƙasar ya bayar umarni ga rundunar tsaron farin kaya ta DSS da ta ɗauki ƙarin jami'an tsaron gandun daji domin su shiga dazukan ƙasar su fatattaki ƴanbindiga.
  • Ƴansanda masu gadin manyan mutane: Shugaban ya ce ƴansandan da aka cire daga manyan mutane suna buƙatar horo na musamman, don haka ya ce a tsara yadda za a ba su horo na musamman kafin a tura su wajen aiki.
  • Tallafi ga dakarun tsaron jihohi: Haka kuma ya bayyana cewa zai yi iya yinsa wajen taimaka wa dakarun jihohi da wasu jihohin suka kafa domin su yi aiki mai kyau.

Tuni dai an ɗauki sababbin ƴansanda, sannan an ɗauki masu tsaron gandun daji da wasu matakan da aka ɗabbaƙa, duk da cewa har yanzu ɓangarorin ƙasar na cigaba da fama da matsalar tsaro.

Inganta tattalin arziki

Daga matsalar tsaro, babbar matsala da za a iya cewa ta fi dugumzuma ƴan Najeriya ita ce taɓarɓarewar tattalin arziki.

Tun a ranar rantsar da Bola Ahmed Tinubu ne shugaban ya bayyana cewa, "zamanin tallafi ya wuce" a jawabinsa na kama aiki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Tun daga ranar ƴan Najeriya suka tsinci kansu a wani sabon babin rayuwa da wataƙila ba su taɓa tsammani ba.

Tinubu ya ce sun bi shawarar gwamnatin da ta gabace ne wajen cire tallafin man fetir wanda yake amfanar masu arziƙi fiye da talakawa.

"Ba za a iya ci gaba da biyan kuɗi tsububu ba a matsayin tallafi a daidai lokacin da lalitar gwamnati ke ci gaba da tsiyayewa. Za mu karkatar da kuɗaɗen zuwa wasu hanyoyin mafiya amfani kamar gine-ginen gwamnati da Ilimi da fannin lafiya da kuma samar da ayyukan yi domin inganta rayuwar miliyoyin ƴan ƙasar."

Jim kaɗan bayan jawabin nasa sai aka fara samun dogayen layukan mai a manyan biranen ƙasar kamar Legas da Abuja da Kano, wanda tun daga lokacin tattalin arzikin mutane ya fara taɓarɓarewa.

Yanzu haka dai farashin man fetur ya haura naira 1,300, wanda hakan ya janyo tashin gwauron zabin farashin kayan masarufi a ƙasar.

Haka kuma ƴan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da matsin tattalin arzikin da ake fuskanta, duk da cire tallafin da ma ciyo basussukan da shugaban ya yi.

Inganta ɓangaren ilimi

Daga muhimman alƙawuran da shugaban ya ɗauka akwai inganta ɓangaren ilimi tun daga firamare zuwa matakin jami'a.

Ko a watan nan na Afrilu, shugaban ya amince da kuɗi domin fara ba malaman jami'o'in Najeriya bashin kuɗin, wanda za su biya a hankali.

Tun kafin nan, tun farkon hawan shugaban mulki, ya assasa shirin ba ɗaliban manyan makarantun ƙasar lamunin kuɗin domin su samu sauƙin karatu.

Sai dai har yanzu malaman jami'o'i da na ƙananan makarantu suna ƙorafi, inda har wasu suka yi watsi da shirin na bashin kuɗin, suna masu cewa suna bin gwamnatin bashi kuɗaɗe, a biya su zai fi a ba su bashi.

Noma da wadatar da ƙasa

Wani abu da Bola Tinubu ya riƙa nanatawa shi ne inganta ɓangaren noma ta yadda za a riƙa nomawa da sana'anta abincin da Najeriya ke buƙata domin wadatar da ƙasar ta daina shigar da abinci.

Sai dai har yanzu manoman ƙasar na cigaba da kokawa, musamman kan tsadar farashin takin zamani da sauran kayan noman zamani.

A ɓangaren masu gyarawa da sana'anta abinci kuwa, matsalar lantarki na cikin ƙalubalen da suke fuskanta, inda dole wasu suka koma amfani da iskar rana wajen samar da makamashi.

Ya cika alƙawari?

Dr Murtala Adoge Mohammad, babban jami'in gudanarwa ne cibiyar System Strategy and Policy Lab da ke Abuja, ya ce Shugaban Najeriya Bola Tinubu bai fahimci wasu matsalolin ba ne kafin ya ɗauki alƙawura.

A cewarsa, da Tinubu ya fahimci irin matsalar da ke ƙunshe a ɓangaren makamashi, da ba zai yi alƙawarin cewa idan bai samar da wutar lantarki ba, kada a zaɓe shi idan yana sake neman zaɓe.

"Misali ka ga a ƙididdigar Unicef, ana haihuwar tsakanin yara miliyan 6 zuwa 7 ne a Najeriya duk shekara. A gefe guda kuma wutar da muke samarwa raguwa take yi. Shi ne za ka ga unguwar da ke da mutum dubu 5 da taransifoma 1, yanzu ta zama mutum 10, kuma wannan taransifomar ɗaya ɗin ce," in ji shi.

Sai dai Dr Adoge ya ce wani ƙoƙari da Tinubu ya yi shi ne yadda ya yi dokar amince jihohi su samar da wutar lantarkinsu.

A ɓangaren, masanin na dokoki da tsare-tsare ya ce nan ma shugaban bai fahimci asalin matsalar ba sosai, domin a cewarsa, da a ce ya yi bincike kafin ya fara mulki, da an magance wasu matsalolin.

Ya yi misali da cire tallafin man fetur, wanda a cewarsa ya sa aka ƙara wa gwamnoni kuɗi.

"A wannan kuɗin ne ya kamata a ce gwamnatin tarayya ta buƙaci gwamnonin su ware wani kaso domin samar wa matasa da ayyukan yi. Da an yi haka, da an samu sauƙi sosai," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa gwamnoni ma ya su taimaka wajen magance matsalar.

A ɓangaren tattalin arziki, Dr Adoge ya ce shugaban ya yi garajen cire tallafin man fetur.

Sai dai ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin na daidaita dala, inda ya ce matakan gwamnatin sun taimaka wajen daidaita darajar naira a kan dala.