Alƙawura biyu da Tinubu ya yi wa al'ummar ƙasar Saint Lucia

Saint Lucia

Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

Lokacin karatu: Minti 2

A ranar Lahadi 29 ga watan Yunin 2025 ne shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara birnin Vieux Fort na ƙasar Saint Lucia a ƙoƙarinsa na ziyarar ƙasashe biyu na farko a yankin Karebiyan da kudancin Amurka.

A yayin ziyarar, shugaba Tinubu ya yi jawabi ga majalisar dattawan Saint Lucia a ranar Litinin 30 ga watan Yuni.

Da yake jawabi a zauren majalisar dokokin ƙasar a gaban firaiminista, Philip J. Pierre, Tinubu ya zayyana wasu tsare-tsare da ya ce Najeriya na son aiwatarwa ga ƙasashe mambobin ƙungiyar ƙasashen yankin Karebiya ko kuma (OECS).

Tinubu ya bayyana cewa tsare-tsaren za su haɓaka alaƙar ƙasashen da Najeriya.

Ga jerin alƙawura biyu da Tinubu ya ɗauka a yayin ziyarar.

Ba da ilimi kyauta ga ɗaliban Karebiyan

Bola Tinubu ya goyi bayan ƙaddamar da tsarin ilimi kyauta ga ɗaliban ƙungiyar ƙasashen Gabashin Karebiya domin yin karatu kyauta a jami'o'in Najeriya.

Rahotanni sun ce ana sa ran tsarin zai fara aiki a zangon karatu mai zuwa.

Tinubu ya ce tsarin na ɗaya daga cikin tsare-tsaren da za su ƙara danƙon zumunci tsakanin Najeriya da ƙasashen na Gabashin Karebiya.

Ɗage biza ga al'ummar Saint Lucia

Shugaba Bola Tinubu ya sanar da shirinsa na ɗage biza ga mutanen yankin na Gabashin Karebiya masu son shiga Najeriya.

Sai dai shi ma Tinubu ya nemi ƙasashen da su ɗage wa ƴan Najeriya bizar shiga ƙasashen nasu.

Ya bayyana irin wannan alaƙa da yadda za a samar da mahaɗa domin fahimtar juna.

Wace ƙasa ce Saint Lucia?

Saint Lucia

Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

Saint Lucia ƙaramar ƙasa ce da ke da yawan al'umma 185,886.

Ƙasar na ɗaya daga cikin ƙasashen da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka na shekaru kafin ta samu ƴancin kai a 1979.

Saint Lucia ba ƙasa ce da ake ayyanawa da addini ba, kasancewar kaso 60 na ƴan ƙasar ba su da addini.

Kaso mafi yawa na al'ummar ƙasar Musulmi ne da Kirista.

Al'ummar ƙasar na magana da harshen Turanci da Faransanci.

Ƙasar ba ta kasance mai yawan arziƙi ba. Tana da yawan duwatsu da tsaunuka da ke jan hankalin masu yawan buɗe ido.

Saint Lucia, wadda kuɗinta a hukumance shi ne dalar gabashin Karebiya.

Asusun Lamuni na Duniya, IMF ya ce ƙasar na samun haɓaka.