Abu 5 da kake buƙata don zama ɗansanda a Najeriya

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Hukumar kula da aikin ɗansanda ta Najeriya ta saki jerin sunayen mutanen da suka samu nasara a ɗaukar kuratan ƴansanda 50,000 a bana, bayan dacewa da sharuɗɗan da aka gindaya.

Kuma abu na gaba bayan sakin jerin sunayen, duk waɗanda sunayen nasu suka fito za su hallara a kwalejojin horar da jami'an ƴansanda a faɗin ƙasar domin samun horo.

To sai dai ba a nan gizo yake saƙa ba kasancewar ƴansandan za su gudanar da tantancewa da kuma gwaje-gwaje a kan masu neman zama ɗan sadan da zarar sun isa kwalejin horarwar kuma nan take ake sallamar wadanda suka gaza tsallake gwajin da tantancewar.

"..Ga duk waɗanda suka gaza tsallake gwaje-gwajen lafiya da jami'an lafiya na ƴansanda za su gudanar a kwalejin horarwa to za a ayyana su a matsayin wadanda ba za su iya aikin ba kuma za a buƙace su su bar kwalejin," in wata sanarwa a shafin hukumar kula da ƴansanda.

Hakan ne ya sa BBC ta yi duba dangane da abubuwan da ake sa ran mutum ya kasance yana da su ta fuskar ingantacciyar lafiya domin hayewa daga tantancewar.

Kamar sauran ayyuka musamman na jami'an tsaro, shi ma aikin ƴansanda na buƙatar a gudanar da gwaje-gwajen lafiya kan masu son shiga aiki domin tantance abubuwa biyar da dole ake buƙata domin yin aikin kamar yadda ya dace. Abubuwan kuwa su ne:

..

Asalin hoton, FCT POLICE COMMAND

1 - Tantance shekaru da takardun karatu

Hukumar da ke kula da ƴansanda dai ta wallafa cewa dole ne matashi ko matashiya su kasance sun dace da abubuwan da ta sharɗanta kamar haka:

  • Shekarun haihuwa su kasance tsakanin 18 zuwa 25
  • Mallakar aƙalla kiredit 5 a takardar kammala sakandire kuma dole akwai Turanci da Lissafi.

2 - Tantancewa ta zahiri

Wannan kusan shi ne gwajin na farko da ake fara yi wa duk wadanda suka shiga kwalejin horas da ɗan sanda, inda ake fara yin duban tsanaki ga zahirin jikin mutum domin tabbatar da babu nakasa a sassan jikinsa.

Wannan kuwa ya hada da tsawo da faɗin ƙirjin mutum.

  • Tsawo: Dole ne na miji ya kai tsawon mita 1.67 wato kwatankwacin ƙafa 5.5, inda ita kuma mace ya zama wajibi ta kai mita 1.64 wato kwatankwacin ƙafa 5.4.
  • Faɗin ƙirji: Ga namiji, dole ne faɗin ƙirjinsa ya zama aƙalla santimita 86 kwatantancin inci 34.

3 - Gwajin lafiya na farko

A nan kuma za a yi gwaje-gwaje da suka haɗa:

  • Hawa da saukar jini
  • Gwajin lafiyar idanu domin tantance mutum yana da cikakkiyar lafiyar ido
  • Gwajin lafiyar kunnuwa domin tabbatar da mutum yana ji sosai

4 - Gwaje-gwaje a ɗakunan gwaji

Bayan mutum ya kammala waɗancan gwaje-gwaje kuma ya haye, abu na gaba shi ne ana gudanar da ƙarin gwaje-gwaje a ɗakin gwaji domin tabbatar da lafiyar wasu abubuwa kamar haka:

  • Gwajin jini domin tabbatar da lafiyar jiki
  • Gwajin fitsari
  • Gwajin shan ƙwaya
  • Gwajin cuta mai karya garkuwar jiki

5 - Gwajin ƙwaƙwalwa

Bayan duk mai son shiga aikin ɗansanda ya wuce wadancan gwaje-gwaje, wani gwaji da shi ma yake taka gagarumar rawa wajen daƙile mafarkin mutane da dama na shiga aikin ɗansanda shi ne gwajin ƙwaƙwalwa da halayyar mutum" ko kuma "tantance yanayin tunani da ɗabi'a da ya ƙunshi abubuwa kamar haka:

  • Lafiyar tunani da ƙwaƙwalwa
  • Natsuwa da iya sarrafa fushi
  • Iya yanke shawara a lokutan matsin lamba
  • Halayen zamantakewa da mu'amala da jama'a
  • Matsalolin tunani da za su iya shafar aikinsa
..

Asalin hoton, FCT POLICE COMMAND

Abubuwan da ya kamata ku tafi da su kwaleji

Shafin na hukumar kula da ƴansanda ya bayyana wasu abubuwa guda biyar da ya kamata wanda sunansa ya fito a jerin sunayen ya riƙe domin zuwa kwalejin haraswa.

Abubuwan kuwa kun sun hada da taakrdu da kayan sakawa kamar haka:

  • Takardar gayyata zuwa kwalejin horaswa (Call-up slip)
  • Takardar ɗan ƙasa (NIN)
  • Lambar bankin ta BVN
  • Takardun kammala makaranta da sauran takardu da suka hada da na haihuwa.
  • Fararen gajerun wanduna da farar T-shirt da farin takalmi sau ciki (white canvas)