Faɗan daba uku da suka janyo asarar rayuka a Kano

Lokacin karatu: Minti 4

Ga al'ummar Kano, gangamin siyasa na neman zama tamkar zaman makoki, sakamakon hare-hare ƴan daba ko dai ga mutanen gari ko kuma tsakanin yaran ƴan siyasa.

Faɗan daba dai a birnin na Kano ba wani sabon abu ba ne amma kuma rikicin ya fi ƙara rincaɓewa da ɗaukar salo a lokutan gangamin siyasa irin wanda ke faruwa a yanzu haka.

Wannan ya sa ƙungiyar kare ƴancin bil'adama ta Amnesty International ta yi alawadai da hare-haren daba da ke janyo asarar rayukan al'ummar birnin Kano, inda ƙungiyar ta yi kira da a binciki abin da ya faru.

Wata ƙididdiga daga sassan gaggawa na asibitoci a jihar Kano ta nuna cewa a watanni shidan farkon shekarar 2025, ta nuna yadda ayyukan daba da ƙwacen waya suka jikkata mutum fiye da 1000.

BBC ta duba lokuta guda uku da ayyukan daba mai alaƙa da siyasa suka kassara al'umma har abin ya kai ga rasa gaɓɓai da ma rayukan jama'a a birnin.

Faɗan daba bayan rantsar da Murtala Garo

Wannan shi ne faɗan daba na baya-bayan nan sannan shi ne wanda ya fi tayar wa al'ummar Kano hankali.

Bayanai da BBC ta tattaro daga Kano sun nuna cewa al'amarin ya faru ne a ranar Talata jim kaɗan bayan kammala rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Kano, Murtala Sule Garo, da aka yi a gidan gwamnati.

Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna wasu mutane da aka kashe kwance cikin jini sannan har da wanda aka yanke wa hannu.

Wani wanda ya shaida yadda al'amarin ya faru ya shaida wa BBC cewa tawagar Murtala Garo sun fito daga gidan gwamnati inda suka yi taho-mu-gama da wata tawagar ta wani ɗan siyasa daban abin da ya janyo mummunar arangama.

"Abin ya faru ne a daidai filin sukuwa wato Race Course inda wasu matasa masu ɗauke da makamai suka hau wasu matasa da sara da suka abin da ya janyo ajalin matasan da dama."

Bayanai sun tabbatar wa da BBC cewa bayan nan kuma masu ɗauke da makaman sun sake komawa wurin da daddare inda suka sake ƙaddamar da hare-hare a kan jama'a.

Ƙungiyar Amnesty International ta ce an kashe mutum biyar sakamakon hare-haren.

Faɗan daba a lokacin ƙaddamar da A.A Zaura

A makon da ya gabata ne kuma aka samu wani harin ƴan daba a kan masu sana'ar waya da ke unguwar Farm Centre a Kano.

Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa al'amarin ya faru ne lokacin da wani ɗan siyasa a Kano, Abdulkarim Zaura da neman takarar sanatan Kano ta tsakiyayake fita daga otal ɗin Bristol da ke yankin na Farm Centre.

Wasu sun alaƙanta faruwar al'amarin da mayar da martani da ƴan tawagar ɗan siyasar suka mayar ga masu jifan su da duwatsu da ke cikin kasuwar.

Sai dai bayanan na nuna cewa wasu matasa ne da suka ɓoye a kewayen kasuwar suka shiga sara da suka kan masu sayar da waya.

"Sun so su ɓata mana suna saboda an san shi Zaura ba ma ya yawo da ƴan daba. Ko da muka zo kasuwar Farm Centre kawai sai muka ji ruwan duwatsu kafin mu an kara sai ƴan daba suka yi kanmu. Amma ƴan sandanmu sun samu damar tarwatsa su. Daga nan ne kuma suka shiga cikin kasuwa suna sara na kan-mai-uwa-da-wabi," in ji wani magoyin bayan A.A Zaura.

Babu rahoton rasa rayuka amma bayanai sun nuna cewa an samu jikkata da dama sakamakon harin.

Faɗan daba lokacin karɓar Shekarau a APC

Sakamakon faɗan daba tsakanin ƙungiyoyin daba a lokacin taron jam'iyyar APC a Kano a watan Afrilu, lokacin karɓar Sanata Malam Ibrahim Shekarau, an samu jikkatar mutane.

Bayanan da BBC ta samu sun tabbatar da sare hannun wani ɗan daba guda ɗaya da ƴan uwansa ƴan daba suka yi bayan wata arangama da ta faru tsakaninsu.

A watan Afrilu ne tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga jam'iyyar hamayya ta PDP inda ya koma jam'iyya mai mulki ta APC.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar APC mai mulki ke ta faɗin tashin zawarcin fitattun ƴan siyasa a faɗin jihar Kano.

Me hukumomi suka ce?

Har kawo yanzu babu wani ɓangare na gwamnati walau dai gwamnatin jihar Kano kuma rundunar ƴansandan jihar, da ya ce uffan dangane da halin da ake ciki musamman abin da ya shafi harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyar ranar Talata.

Sai dai ƙungiyar Amnestiy International ta nemi gwamnatin jihar Kano da ta ƙaddamar da bincike na gaskiya domin gano haƙiƙanin abin da ya faru da kuma waɗanda ke ɗaukar nauyin ƴan dabar.

Duk da cewa Amnesty ta ce wasu ƴan siyasa ne na jam'iyyar APC ke ɗaukar nauyin ayyukan daba amma ta ce ita da kanta a yanzu haka tana bincike domin gano sunayen ƴan siyasar da ke daukar nauyin ayyukan daba.