Yaya rundunar 'yan sandan jihohi za ta yi aiki a Najeriya idan Tinubu ya amince da ita?

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Majalisar Dattawan Najeriya ta kammala aiki a kan dokar gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar karo na shida ta 2026, wadda za ta tanadi kafa rundunar 'yan sandan jihohi.

Majalisar ta ce ta kammala shirya kudirin dokar domin miƙa shi ga shugaban ƙasa don neman amincewarsa.

Majalisar Dattawan ta amince da umartar magatakardar Majalisar Dokokin Tarayya da ya miƙa wa shugaban ƙasa, wanda kuma shi ne babban kwamandan rundunar sojin ƙasar, kudirin dokar mai taken: "Dokar gyaran kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya ta 1999, domin tanadin kafa rundunonin 'yan sandan jihohi da wasu batutuwa masu alaƙa da hakan (gyara ta shida) ta 2026", domin neman amincewarsa, kamar yadda dokar tabbatar da sahihancin dokoki ta 2004 ta tanada.

Matakin ya nuna cewa kudirin kafa rundunar 'yan sandan jihohin ya samu gagarumin ci gaba a Majalisar Dattawan.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da matsalolin tsaro ke ci gaba da addabar sassan Najeriya, ciki har da ayyukan 'yan bindiga, da sace mutane da dama da kuma rikice-rikice, waɗanda hukumomin tsaro na tarayya ke fuskantar ƙalubalen shawo kansu.

An sha bayyana damuwa kan ƙarancin jami'an 'yan sanda a Najeriya, inda masu sa ido kan harkokin tsaro ke cewa rundunar na fama da rashin isassun kayan aiki, ƙarancin horo da kuma fuskantar barazanar cin hanci da rashawa, a ƙasar da ke da mutane sama da miliyan 200.

Yaya aka kai ga wannan mataki na kudirin dokar kafa rundunar 'yan sandan jihohi?

Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun fara aikin amincewa da kudirin dokar ne a ranar 24 ga Yuni da kuma 23 ga Yuli, 2026, inda mafi rinjayen kashi biyu bisa uku na mambobinsu suka kada ƙuri'ar goyon baya ga kudirin.

Samun goyon bayan kashi biyu bisa uku na Majalisar Dokokin Tarayya na nufin an cika sharadin da kundin tsarin mulkin ƙasar ya gindaya domin amincewa da kudirin.

Bayan haka, Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya ta miƙa kudirin ga majalisun dokokin jihohi 36 domin neman amincewarsu, kamar yadda doka ta tanada.

A wannan mataki, ana buƙatar aƙalla kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohin su amince da kudirin, kamar yadda sashe na 9(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada, kafin a iya kammala amincewa da shi.

A watan Nuwamban 2026, Majalisar Dattawa ta bai wa wasu majalisun dokokin jihohi shida wa'adin wasu kwanaki domin kammala matsayarsu kan kudirin kafa rundunar 'yan sandan jihohi.

Hakan ya biyo bayan sanarwar da shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya yi cewa majalisun dokokin jihohi 30 sun riga sun amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulkin domin kafa rundunar 'yan sandan jihohi.

Sai dai Sanata Bamidele ya bayyana cewa adadin jihohin da suka amince ya riga ya zarce mafi ƙarancin kashi biyu bisa uku, wato jihohi 24, da kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada domin amincewa da kudirin.

A ranar 15 ga Nuwamban 2026, lokacin da wa'adin da Majalisar Dattawa ta bai wa majalisun dokokin jihohin ya cika, dukkan jihohi 36 sun bayyana matsayarsu kan kudirin.

Wannan ne ya buɗe hanyar miƙa kudirin ga shugaban ƙasa domin neman amincewarsa.

Wasu ƙasashen da ke da tsarin rundunar 'yan sandan jihohi kamar yadda ake son yi a Najeriya

Amurka (US): A Amurka, an raba tsarin aikin 'yan sanda tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya, inda kowannensu ke gudanar da ayyukansa bisa dokoki da ikon da aka ba shi, maimakon samun rundunar 'yan sanda guda ɗaya da ke kula da dukkan ƙasar.

Gwamnatocin jihohi suna da babban ikon tabbatar da tsaron jama'a da aiwatar da dokokin jihohinsu, yayin da hukumomin gwamnatin tarayya ke aiwatar da wasu takamaiman dokokin ƙasa a duk faɗin Amurka.

Kowace jiha a Amurka tana da tata rundunar 'yan sandan, wadda aka fi sani da State Police ko Highway Patrol. Rundunonin suna da alhakin aiwatar da dokokin laifuffuka da na zirga-zirgar ababen hawa na jihohinsu.

Ostiraliya: A Ostiraliya, kowace jiha da yanki suna da nasu rundunonin 'yan sanda, kamar rundunar 'yan sandan jihar New South Wales, wadda ke kula da ayyukan yaƙi da laifuffuka na yau da kullum da kuma dokokin zirga-zirgar ababen hawa.

Ita kuwa rundunar 'yan sandan gwamnatin tarayya ta Ostiraliya (AFP) tana da alhakin aiwatar da dokokin tarayya, yaƙi da ta'addanci da kuma gudanar da ayyukan 'yan sanda a babban birnin ƙasar, Canberra, da ke yankin Australian Capital Territory.

Kanada: A Kanada, an raba alhakin gudanar da ayyukan 'yan sanda tsakanin gwamnatin tarayya, da gwamnatocin larduna da ƙananan hukumomi.

Lardunan Ontario da Quebec suna da nasu rundunonin 'yan sanda, yayin da rundunar 'yan sandan gwamnatin tarayya ta Royal Canadian Mounted Police (RCMP) ke aiwatar da dokokin tarayya a duk faɗin ƙasar. Haka kuma, tana gudanar da ayyukan 'yan sanda na larduna da ƙananan hukumomi a mafi yawan sauran lardunan ƙasar.

Idan Najeriya ta amince da kudirin dokar kafa rundunar 'yan sandan jihohi, hakan na nufin za ta shiga cikin jerin ƙasashen da ke amfani da irin wannan tsarin raba ikon gudanar da ayyukan 'yan sanda tsakanin matakan gwamnati daban-daban.

Me zai biyo baya idan Tinubu ya sanya hannu kan kudirin ?

Yanzu da Majalisar Dattawa ta miƙa kudirin dokar kafa rundunar 'yan sandan jihohi ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin neman amincewarsa, tambayar da ake yi ita ce me zai biyo baya?

Dokokin da ke tsara yadda ake kafa doka a Najeriya sun tanadi wa'adin kwanakin da shugaban ƙasa zai ɗauka kafin ya amince da kudirin ko kuma ya ƙi sanya hannu a kansa.

Dokar ta tanadi cewa shugaban ƙasa yana da kwanaki 30 da zai sanya hannu kan kudirin ko kuma ya ƙi amincewa da shi.

Idan shugaban ƙasa ya sanya hannu kan kudirin, zai zama doka ta Majalisar Dokokin Tarayya.

Amma idan ya ƙi amincewa da shi, zai mayar da kudirin ga majalisar dokokin tare da bayyana dalilan ƙin amincewarsa.

Idan kuma shugaban ƙasa bai ɗauki wani mataki kan kudirin ba cikin kwanaki 30, a lokacin da Majalisar Dokokin Tarayya ke ci gaba da zama, kudirin zai iya zama doka kai tsaye.

A yayin da shugaban ƙasa ya ƙi sanya hannu kan kudirin, kundin tsarin mulkin ƙasar ya bai wa Majalisar Dokokin Tarayya damar soke wannan mataki ta hanyar samun goyon bayan kashi biyu bisa uku na mambobin kowace majalisa.

A irin wannan yanayi, kowace majalisa za ta sake nazarin kudirin, sannan idan aƙalla kashi biyu bisa uku na mambobinta suka kada ƙuri'ar goyon bayan amincewa da shi duk da ƙin amincewar shugaban ƙasa, kudirin zai zama doka ba tare da buƙatar sa hannunsa ba.

Bayan samun amincewar shugaban ƙasa ko kuma Majalisar Dokokin Tarayya ta soke ƙin amincewarsa, kudirin zai zama doka, sannan a wallafa shi a matsayin dokar Majalisar Dokokin Tarayya (Act of the National Assembly).

Za a wallafa dokar a cikin kundin sanarwar gwamnati (Government Gazette), kuma za ta fara aiki daga ranar da aka ayyana a cikinta.

Sharuɗɗan kafa rundunar 'yan sandan jihohi da kuma shirye-shiryen da jihohi suka yi na kafa ta.

Kudirin dokar da ke gaban Majalisar Dokokin Tarayya na da manufar ƙarfafa tsarin samar da tsaro a Najeriya ta hanyar raba ikon gudanar da ayyukan 'yan sanda tsakanin matakan gwamnati.

Kudirin na neman yin gyara ga sashe na 197, 214 da 215 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, domin sake fayyace iko, gudanarwa da kuma tsarin kula da rundunar 'yan sandan Najeriya.

Idan Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan kudirin, zai kawo ƙarshen tsarin da ke bai wa shugaban ƙasa da Sufeto-Janar na 'yan sanda cikakken ikon kula da rundunar 'yan sanda, ta hanyar samar da damar kafa rundunonin 'yan sandan jihohi.

Haka kuma, zai bai wa gwamnatocin jihohi cikakken iko kan hukumomin tsaron da ke ƙarƙashinsu, musamman rundunar 'yan sanda.

Kudirin ya tanadi kafa rundunar 'yan sandan tarayya da kuma rundunonin 'yan sandan jihohi, tare da fayyace cewa rundunar 'yan sandan tarayya ba za ta tsoma baki cikin ayyukan rundunar 'yan sandan jiha ba bayan kafa ta.

A wani ɓangare na kudirin, sashe na 13 ya yi tanadin sauya tsarin naɗa Sufeto-Janar na 'yan sanda da kwamishinonin 'yan sandan jihohi, ta hanyar bai wa majalisun dokoki, na tarayya da na jihohi, ikon tantancewa da amincewa da naɗin waɗannan jami'ai.

Dangane da kuɗaɗen gudanarwa kuwa, kudirin gyaran kundin tsarin mulkin da ya shafi kafa rundunar 'yan sandan jihohi na 2023 ya kuma yi tanadin hanyoyin samun kuɗaɗen gudanar da rundunonin.

Kudirin ya bai wa gwamnatin tarayya damar tallafa wa rundunonin 'yan sandan jihohi, tare da amincewar Majalisar Dokokin Tarayya.

Idan kudirin ya samu amincewar shugaban ƙasa, hakan na nufin jihohi za su samu ƙarin iko wajen gudanar da ayyukan 'yan sanda da tabbatar da tsaro a yankunansu.