Ta yaya mace za ta iya neman saki a addinin Musulunci?

.
Bayanan hoto, Khul'i wata hanya ce ta raba aure wadda mace take bi ta hanyar neman rabuwa da mijinta
    • Marubuci, Imam Saleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC World News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

A addinin Musulunci, ba namiji kaɗai ne yake da damar neman a raba aure ba. Mace ma tana da wannan dama, idan ta ga cewa ba za ta iya ci gaba da rayuwar aure da mijinta ba, ko kuma tana fargabar kasa sauke haƙƙoƙin aure da Allah Ya ɗora mata.

Wannan hanya ita ce Khul'i.

Khul'i wata hanya ce ta raba aure wadda mace take bi ta hanyar neman rabuwa da mijinta, tare da yarjejeniya kan abin da za ta mayar masa a matsayin fansar sakin. A lokuta da dama, wannan fansa tana iya kasancewa sadakin da mijin ya ba ta a lokacin aure.

Sai dai mene ne ainihin Khul'i? A wanne yanayi ne mace za ta iya neman Khul'i? Shin wajibi ne ta mayar da sadakin da aka ba ta? Kuma mene ne bambancin Khul'i da sakin da namiji yake yi?

Mene ne Khul'i a addinin Musulunci?

A cewar fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Halliru Maraya, kalmar Khul'i ta samo asali ne daga Larabci, tana nufin cire wani abu ko tuɓe shi. A fannin fikihun Musulunci kuwa, tana nufin raba auren da mace ta nemi a yi, bisa tsarin fansa ko yarjejeniyar kuɓutar da kanta daga auren.

A cewarsa babban dalilin da ya halatta wannan hanya yana cikin Alƙur'ani, Suratul Baƙara, aya ta 229, inda Allah Ya bayyana cewa babu laifi ga ma'aurata idan suka ga ba za su iya kiyaye dokokin Allah ba, mace ta fanshi kanta domin a raba auren.

Wannan aya ta kafa muhimmin tushe na shari'ar Khul'i, wato cewa mace ba dole ba ne ta ci gaba da zaman aure idan ta fahimci cewa ba za ta iya gudanar da haƙƙoƙin aure yadda ya kamata ba.

Ta yaya mace za ta nemi Khul'i?

Malamin ya lasafto wasu hanyoyi guda huɗu da ya ya kamata mace ta bi domin neman irin wannan rabuwa.

1. Bayyana buƙatarta ga mijinta

A cewarsa abu na farko shi ne ta sanar da mijinta cewa tana son a raba aurensu ta hanyar Khul'i. Ya kamata ta bayyana dalilin da ya sa take ganin ba za ta iya ci gaba da zama da shi ba.

''Ba lallai ne sai ta jira mijinta ya furta kalmar saki ba kafin ta fara neman hanyar warware matsalar aurenta''

2. Ƙoƙarin sulhu

Ya ƙara da cewa Musulunci yana ƙarfafa ma'aurata su nemi sulhu kafin raba aure, idan hakan yana yiwuwa.

Amma idan sulhun ya ci tura, hakan ba yana nufin dole mace ta ci gaba da zama a auren da ba ta iya jurewa ba, in ji shi.

3. Tattaunawa kan sadaki ko fansa

A mafi yawan tsarin Khul'i, a cewar Sheikh Halliru Maraya, ana tattaunawa kan abin da matar za ta mayar wa mijinta domin a raba auren.

4. Tabbatar da rabuwar auren

Idan ma'auratan sun cimma yarjejeniya, sai a aiwatar da rabuwar auren bisa tsarin shari'a da ya dace, kamar yadda ya shaida wa BBC.

Shin dole ne mace ta mayar da sadakinta kafin a ba ta Khul'i?

Fitaccen malamin addinin Musulunci ya ce a tsarin Khul'i, mace na iya zama wajibi ta mayar wa mijinta sadakin da ya ba ta, ko kuma abin da suka amince da shi a matsayin fansar rabuwar auren, domin shi ma ya samu damar sake gina rayuwar aurensa.

Sai dai ya bayyana cewa idan dalilin neman rabuwar auren shi ne musgunawa, cin zarafi ko zalunci da matar ke fuskanta a gidan aurenta, to lamarin ya bambanta. A irin wannan yanayi, alƙali zai binciki korafin domin tantance halin da matar take ciki da kuma irin hukuncin da ya dace.

Malamin ya jaddada cewa Alƙur'ani ya yi gargaɗi a Suratun Nisa'i, aya ta 19, kan hana maza tsangwamar matansu da nufin ƙwace wani ɓangare na abin da suka ba su.

Wannan ya nuna cewa akwai bambanci tsakanin macen da ta nemi Khul'i saboda ba ta son ci gaba da zaman aure, da wadda ta nemi rabuwa sakamakon cin zarafi ko zaluncin da take fuskanta daga mijinta.

Me zai faru idan miji ya ƙi amincewa da Khul'i?

A wajen wasu malaman fikihu, Khul'i yarjejeniya ce tsakanin miji da mata, don haka ana buƙatar amincewar miji.

Amma idan miji ya ƙi sakin matarsa, duk da cewa zaman auren ya zama abin cutarwa ko ba zai yiwu a ci gaba da shi ba, akwai wata hanyar da ake kira Faskh al-Nikah, wato warware auren ta hanyar hukuncin alƙali bisa dalilan da shari'a ta amince da su.

Dalilan da za su iya kaiwa ga hakan sun haɗa da:

  • Cutarwa da miji yake yi wa matarsa.
  • Rashin ciyarwa ko kula da iyali, gwargwadon hukuncin shari'a.
  • Barin mace cikin halin ƙunci ba tare da cika haƙƙoƙinta ba.
  • Wasu manyan matsalolin aure da suka sa zaman ba zai yiwu ba.

A cewar malamin a irin wannan yanayi, ya kamata mace ta nemi taimakon malamin da ya ƙware a fikihu ko kotun shari'a da ke da hurumin sauraron irin wannan ƙara.

Ya ce ya kamata a lura cewa Khul'i da Faskh ba abu ɗaya ba ne, kuma hukuncinsu kan sadaki da sauran haƙƙoƙin aure na iya bambanta.