Birnin da gwamnati ta hana amfani da tsabar kuɗi a Pakistan

Islamabad
    • Marubuci, Umair Mahmood
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Urdu
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Gwamnatin Pakistan ta sanar da wani shiri na mayar da birnin Islamabad ya zama babban birni na farko a duniya da ba a amfani da tsabar kuɗi wajen hada-hadar kasuwanci, sannan kuma birni na farko a ƙasar da zai koma tsarin biyan kuɗi ta hanyar zamani zalla.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin cikin gida ta fitar a ranar Juma'a, 13 ga watan Nuwamba, ta ce wa'adin kammala shirin mayar da Islamabad birni mai amfani da tsarin biyan kuɗi ta hanyar zamani kawai shi ne ranar 31 ga watan Disamba.

Ma'ana, gwamnatin na son tabbatar da cewa dukkan cibiyoyin kasuwanci da 'yan kasuwa sun shiga tsarin biyan kuɗi ta hanyar zamani kafin wannan wa'adi.

A cewar ma'aikatar harkokin cikin gida, an gudanar da wani muhimmin taro kan shirin 'Cashless Islamabad', wanda ministan harkokin cikin gida na ƙasa, Talal Chaudhry, ya jagoranta.

Taron ya samu halartar shugaban hukumar raya babban birnin ƙasar (CDA), Sohail Ashraf, da wakilan ɓangaren bankuna, tare da wasu manyan jami'an gwamnati.

Taron ya tattauna shawarwari da matakai daban-daban da za su taimaka wajen mayar da Islamabad birni mai amfani da tsarin biyan kuɗi na zamani zalla.

Talal Chaudhry ya ce tuntuɓar dukkan masu ruwa da tsaki da haɗin kansu na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da nasarar shirin.

Ya ce: "Ministan harkokin cikin gida na tarayya, Mohsin Naqvi, ya yi wa Firaminista alƙawarin cewa za a mayar da Islamabad birni na farko a Pakistan da ba a amfani da tsabar kuɗi, sannan kuma babban birni na farko a duniya da zai koma wannan tsarin."

A cewarsa, daga ranar 30 ga watan Nuwamba, ba za a ƙara karɓar tsabar kuɗi a dukkan ma'aikatun gwamnati da ke yankin babban birnin Islamabad (ICT) da kuma hukumar raya babban birnin (CDA) ba.

Talal Chaudhry ya ce manufar ita ce tabbatar da cewa dukkan 'yan kasuwa da ke Islamabad sun shiga tsarin hada-hadar kuɗi ta hanyar zamani kafin ranar 31 ga watan Disamba.

A cewarsa, bunƙasa amfani da tsarin biyan kuɗi na zamani zai ƙara tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkokin kuɗi, da inganta sa ido kan tsarin karɓar haraji, tare da inganta yadda ake gudanar da ayyukan saye da sayarwa.

Ministan harkokin cikin gidan ya ce ya zuwa yanzu, an kama 'yan kasuwa 26,000 saboda amfani da tsarin biyan kuɗi na zamani a Islamabad.

Gwamnatin ta ce manufar mayar da Islamabad birni mai amfani da tsarin biyan kuɗi na zamani kawai ita ce sauƙaƙa wa al'umma yin hada-hadar kuɗi ta hanyar zamani, ba wai tilasta musu daina amfani da tsabar kuɗi ba.

Yadda za a mayar da Islamabad birnin da ba a kashe tsabar kuɗi

Contactless
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Da yake magana da BBC Urdu, Ministan Cikin Gida na Ƙasa Talal Chaudhry ya ce gwamnati na son samar da yanayin da zai ba kowane ɗan kasuwa damar karɓar kuɗin ciniki ta hanyar intanet ko na'urar zamani kafin ranar 31 ga Disamba, ko da kuwa ƙaramin shago ne ko babba.

Ya ce a ƙarƙashin wannan shiri, za a bai wa dukkan 'yan kasuwa a Islamabad damar karɓar kuɗin kaya ta hanyar zamani, idan kwastoma ya zaɓi yin hakan.

Da yake ƙarin bayani kan shirin, Talal Chaudhry ya ce za a samar da hanyoyin biyan kuɗi na zamani a dukkan matakai, tun daga masu ƙananan sana'o'i har zuwa manyan kamfanoni. Ya ce za a kuma bai wa 'yan kasuwa asusun ajiya da lambobin QR kyauta domin sauƙaƙa musu karɓar kuɗi ta wannan hanya.

Ministan ya ce gwamnati na kuma aiki kan samar da na'urorin sanarwa ta murya a shaguna da cibiyoyin kasuwanci daban-daban, waɗanda za su rika sanar da mai sayarwa nan take idan an tura masa kuɗi.

A cewarsa, wannan mataki zai ƙara wa masu saye da masu sayarwa kwarin gwiwa wajen amfani da tsarin.

Da aka tambaye shi ko ana iya samun turjiya daga masu motocin dakon kaya da ƙananan 'yan kasuwa, Talal Chaudhry ya ce a yayin shawarwari da binciken da aka gudanar a sassa daban-daban, an gano cewa da dama daga cikin ƙananan 'yan kasuwa sun riga sun saba da karɓa da tura kuɗi ta wayoyin hannu.

Sai dai ya ce gwamnati na son faɗaɗa wannan hanya ta hanyar ƙara wayar da kan jama'a da sauƙaƙa tsarin amfani da ita.

Ya ƙara da cewa za a riƙa nuna wa jama'a a fili a cibiyoyin kasuwanci na Islamabad cewa akwai damar biyan kuɗi ta hanyar zamani.

Shin jama'a da ƙananan 'yan kasuwa sun shirya?

Islamabad

Ajmal Baloch, shugaban ƙungiyar masu sana'o'i da masana'antu ta Pakistan (All Pakistan Chamber of Commerce and Industry), ya ce har yanzu akwai mutane da dama a ƙasar waɗanda ba su da wayoyin zamani, asusun banki ko damar amfani da hanyoyin biyan kuɗi ta fasahar zamani.

Da yake magana da BBC Urdu, ya ce idan ƙananan 'yan kasuwa da masu sayar da kaya a kan titi ba su samu damar shiga wannan tsarin ba, hakan na iya shafar masu ƙaramin ƙarfi kai tsaye, domin za su iya tilastuwa zuwa manyan cibiyoyin kasuwanci da ke nesa domin sayen kayan masarufi na yau da kullum.

A cewar Ajmal Baloch, waɗannan matsaloli ba su shafi 'yan kasuwa kaɗai ba, har ma da talakawa masu saye, musamman waɗanda ba su saba sosai da harkokin banki ta intanet da biyan kuɗi ta wannan hanya ba.

Shugaban ƙungiyar ya ce har yanzu mutane da dama a Pakistan ba su da cikakkiyar fahimta kan yadda ake gudanar da mu'amalar kuɗi ta hanyar zamani. Ya ce matsaloli irin su tura kuɗi zuwa asusun banki ko lambar waya da ba daidai ba yayin aika kuɗi, na faruwa akai-akai.

Ya ce: "Idan aka aiwatar da irin wannan sauyi gaba ɗaya lokaci guda, 'yan ƙasa da dama za su fuskanci matsaloli."

Ajmal Baloch ya ce wannan ƙalubale na iya fi shafar ƙananan 'yan kasuwa da masu sayar da kaya a kan titi fiye da sauran 'yan kasuwa, saboda da yawa daga cikinsu ba su da asusun banki na yau da kullum.

Ya ƙara da cewa yayin da amfani da kuɗaɗen zamani ke ƙaruwa, akwai kuma haɗarin zamba. A cewarsa, mutanen da ba su yi karatu sosai ba ko kuma ba su saba da fasahar zamani ba, sukan faɗa tarkon masu damfara, inda a wasu lokutan ake cire kuɗi daga asusunsu.

Ya ce dole ne gwamnati ta fara samun amincewar dukkan masu ruwa da tsaki, musamman ƙananan 'yan kasuwa, masu talla a kan titi da sauran masu saye, kafin aiwatar da shirin. Ya kuma ce ya kamata a koma tsarin da ba a amfani da kuɗin hannu a hankali, tare da tabbatar da wayar da kan jama'a da kuma shigar da su cikin sabon tsarin.

Ya ce: "Wannan na iya zama kyakkyawan mataki, amma a ƙasa mai fama da talauci kamar Pakistan, zai dace a kawo irin waɗannan sauye-sauye sannu a hankali."

Baya ga batun samun damar harkokin kuɗi da damuwar 'yan kasuwa, masana na kuma mai da hankali kan wani fanni, wato tsaron bayanan sirri da mu'amalolin intanet.

Tangarɗar fasaha da wannan tsarin zai iya fuskanta

A cewar wani mashawarcin harkokin tsaron intanet, Mirza Burhan Baig, babban haɗarin tsarin biyan kuɗi ba tare da amfani da kuɗin hannu ba shi ne abin da ake kira single point of failure. Ma'ana, idan tsarin banki, sadarwar wayar hannu ko wata babbar manhajar biyan kuɗi ta samu matsala ko ta daina aiki saboda wani dalili, hakan na iya kawo cikas ga harkokin kuɗin da 'yan ƙasa ke gudanarwa a kullum.

Da yake magana da BBC Urdu, ya ce a wasu lokuta ana katse hanyoyin sadarwar wayar hannu a Pakistan saboda dalilan tsaro ko na gudanarwa. Don haka, idan aka takaita dukkan hanyoyin biyan kuɗi zuwa na zamani, hakan na iya jefa 'yan ƙasa cikin wahala wajen saye da sayarwa da sauran mu'amalolin kuɗi.

A cewar Burhan Baig, a tsarin tattalin arzikin da ba a amfani da kuɗin hannu, haɗarin laifuffukan intanet kamar satar bayanan mutum, ƙirƙirar lambobin QR na bogi da kuma ƙwace iko da asusun bankin wani na ƙaruwa.

Ya ce idan mai damfara ya yi nasarar samun damar shiga asusun wani ta hanyar samo bayanan sirrinsa na shiga asusun, zai iya amfani da tsarin kuɗin ta hanyar da ba ta dace ba. A irin wannan yanayi, mai asusun na gaskiya zai iya ɗaukar lokaci mai tsawo kafin ya sake samun damar amfani da asusunsa.

Mirza Burhan Baig ya ce manyan ayyukan fasahar zamani da gwamnati ko kamfanoni masu zaman kansu ke gudanarwa sukan dogara da kamfanonin manhajoji daban-daban, haɗin gwiwar fasaha da kuma ayyukan wasu kamfanoni na waje. A cewarsa, idan aka samu wata matsalar tsaro a ɗaya daga cikin waɗannan sassa ko manhajoji, hakan na iya shafar tsarin gaba ɗaya.

Ya ƙara da cewa 'yan ƙasa na iya fuskantar matsalar kuɗi nan take idan wayoyinsu suka ɓace ko aka sace su, ko kuma aka dakatar da asusun bankinsu na ɗan lokaci, musamman idan ba su da wata hanyar biyan kuɗi ta daban.

Masanin tsaron intanet ɗin ya ce nasarar tsarin biyan kuɗi ba tare da kuɗin hannu ba ba ta dogara da fasaha kaɗai ba, har ma da wayar da kan jama'a.

Ya ce har yanzu mutane da dama a Pakistan ba su da cikakkiyar fahimta kan kuɗaɗen zamani, tura kuɗi ta intanet da kuma biyan kuɗi ta wayoyin hannu. Saboda haka, ya kamata a fara aiwatar da irin wannan sauyi a hankali, tare da gudanar da manyan shirye-shiryen wayar da kan jama'a.

A cewar Mirza Burhan Baig, ƙasashe da dama a duniya sun koma tsarin biyan kuɗi ba tare da amfani da kuɗin hannu ba sannu a hankali, inda aka fara gwada tsarin a wasu ƙayyadaddun yankuna. Ya ce irin wannan mataki na tafiya a hankali na iya fi yin tasiri a Pakistan.