Me ya haifar da takun-saƙa tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu?

Femi Fani-Kayode da Cyril Ramaphosa
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

An samu takun-saka a dangantakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu, bayan sabon jakadan Najeriya a ƙasar, Femi Fani-Kayode, ya zargi gwamnatin Afirka ta Kudu da rashin yaɗa jawabinsa yadda ya kamata.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a, 13 ga watan Nuwamban 2026, lokacin da Femi Fani-Kayode ya miƙa takardar shaidar jakadancinsa ga Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, a wani biki na fara aikinsa a matsayin wakilin Najeriya a ƙasar.

A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Fani-Kayode ya yi zargin cewa jawabinsa ne kaɗai ba a yaɗa shi kai tsaye ta kafar watsa shirye-shiryen da ke ɗaukar taron ba, a lokacin da ya gabatar da shi.

Takun-sakan diflomasiyyar ya samo asali ne bayan Fani-Kayode ya nuna rashin jin daɗinsa kan zargin cire jawabinsa daga cikin shirye-shiryen da ake yaɗawa kai tsaye yayin bikin miƙa takardun shaidar jakadanci ga Shugaba Cyril Ramaphosa.

Ya zargi gidan talabijin na Afirka ta Kudu da dakatar da yaɗa shirin kai tsaye a daidai lokacin da jakadan Najeriya ya hau dandamali domin gabatar da jawabinsa.

Fani-Kayode ya dage cewa shi kaɗai ne cikin jakadu 15 da aka ba damar yin jawabi a wajen taron wanda aka dakatar da yaɗa jawabinsa kai tsaye.

A cikin wata sanarwa, ofishin jakadancin Najeriya a Afirka ta Kudu ya yi Allah wadai da abin da aka yi wa Fani-Kayode, yana mai cewa hakan cin mutunci ne ga jakadan da kuma daukacin al'ummar Najeriya.

Fani-Kayode ya ce ya tattauna da Shugaba Ramaphosa, wanda ya sanar da shi cewa zai sa baki domin shawo kan lamarin.

Fani-Kayode ya kuma ce wannan ne dalilin da ya sa bai amince da buƙatar yin hira da shi da gidan rediyo da talabijin na SABC ya gabatar masa ba.

Sai dai a martaninsa, mai magana da yawun gwamnatin Afirka ta Kudu, Vincent Magwenya, ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa Shugaba Ramaphosa ba shi da hannu a lamarin ba.

An ruwaito shi yana cewa gidan talabijin na SABC ya yaɗa taron kai tsaye, kuma tawagar shugaban ƙasar ba ta da ta cewa kan yadda gidan talabijin ɗin ke gudanar da harkokin editocinsa.

Ya ce: "Shugaba Ramaphosa bai taɓa tsoma baki a harkokin SABC ba, domin hukuma ce mai cin gashin kanta."

Magwenya ya bayyana zarge-zargen da Fani-Kayode ke yi kan wata ƙaramar matsalar da suka samu da kafar yaɗa labarai a matsayin abin da ya saɓa hankali.

Femi Fani-Kayode da Cyril Ramaphosa

Ana kallon naɗin Fani-Kayode a matsayin wani mataki na ƙarfafa zaman lafiya da kyautata dangantaka tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu, musamman a daidai lokacin da ake samun hare-haren ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu, waɗanda ake kai wa baƙin haure daga ƙasashen Afirka daban-daban da ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.

Wannan ne ya sa Najeriya ta fara shirin mayar da 'yan ƙasarta da ke zaune a Afirka ta Kudu, waɗanda suka bayyana aniyarsu ta komawa gida.

Haka kuma, Ghana da wasu ƙasashe sun fara mayar da 'yan ƙasarsu da ke zaune a Afirka ta Kudu zuwa gida.

Abin da Najeriya ta ce

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ofishin jakadancin Najeriya a Afirka ta Kudu ya yi Allah wadai da kalaman mai magana da yawun gwamnatin ƙasar, Vincent Magwenya, kan sabon jakadan Najeriya, Femi Fani-Kayode, yana mai zarginsa da ƙoƙarin haddasa rashin jituwa tsakanin ƙasashen biyu.

A cikin wata sanarwa, ofishin jakadancin ya ce a lokacin da Magwenya ke matsayin mai magana da yawun shugaban Afirka ta Kudu, ya riƙa sukar shugabannin Najeriya da Ghana kan zargin yaɗa bayanan da ba daidai ba game da hare-haren ƙyamar baƙi da suka ɓarke a Afirka ta Kudu.

Ya kuma zargi Magwenya da ci gaba da ɓata wa Najeriya suna, ta hanyar kiran wakilinta, Fani-Kayode, maƙaryaci.

Ofishin jakadancin ya bayyana abin da aka yi wa Fani-Kayode a wajen bikin miƙa takardun shaidar jakadanci a matsayin cin mutunci ga jakadan da kuma daukacin al'ummar Najeriya.

A nasa ɓangaren, Magwenya ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa Shugaba Cyril Ramaphosa bai taɓa tsoma baki a harkokin gidan talabijin na SABC ba, domin hukuma ce mai cin gashin kanta.

Kafar yaɗa labaran SABC ta yi ƙarin haske

Gidan rediyo da talabijin na Afirka ta Kudu (SABC) ya mayar da martani kan cece-kucen da ya biyo bayan yadda aka yaɗa bikin miƙa takardun shaidar jakadanci, inda ake zargin an cire sabon jakadan Najeriya a ƙasar, Femi Fani-Kayode, daga cikin shirye-shiryen da aka yaɗa kai tsaye.

A cikin sanarwar da ta fitar, SABC ta ce ta haska isowar Fani-Kayode a lokacin da take yaɗa wani ɓangare na taron kai tsaye a tashar SABC News da ke tashar DStv mai lamba 404.

Ta kuma ce ta wallafa wani faifan bidiyo a tashar labaranta da kuma shafinta na X, wanda ke nuna jakadan Najeriya yana tattaunawa da Shugaba Cyril Ramaphosa.

Sanarwar ta ce: "Na biyu, SABC News ta ɗauki rahoton bikin. An yaɗa shi kai tsaye a tashar SABC News LIVE da ke kan SABC+, sannan an nuna isowar babban kwamishinan Najeriya yayin da ake yaɗa wani ɓangare na taron kai tsaye a tashar SABC News (DStv mai lamba 404). Haka kuma, mun wallafa wani faifan bidiyo a shafinmu na X na hukuma, wanda ke nuna babban kwamishinan yana magana da Shugaba Cyril Ramaphosa."

Sai dai kafar yaɗa labaran ba ta yi bayanin dalilin da ya sa aka dakatar da yaɗa taron kai tsaye a lokacin da ake gudanar da bikin ba.

Maimakon haka, ta ce ta nemi yin hira da Fani-Kayode ne bayan ya kai ƙorafinsa ga Shugaba Ramaphosa, amma ya ƙi amincewa da buƙatar.

A cikin sanarwar, SABC ta ce: "Mun lura da kalaman da babban jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, Femi Fani-Kayode, ya wallafa a kafafen sada zumunta kan yadda aka ɗauki rahoton bikin miƙa takardun shaidar jakadanci a gidan baƙi na shugaban ƙasa na Sefako Makgatho da ke Pretoria a ranar Juma'a.

"Ba mu ji daɗin yadda jakadan ya ƙi amincewa da buƙatar yin hira da SABC News, bisa rahoton cewa bai ji daɗin yadda aka yaɗa bikin kai tsaye ba. Muna mutunta matakin nasa, kuma a shirye muke mu ci gaba da hulɗa da shi da ofishin jakadancin Najeriya."

Kafar yaɗa labaran ta kuma ce akwai wasu muhimman batutuwa biyu da take son fayyacewa.

Ta ce: "Na farko, SABC kafar yaɗa labarai ce ta al'umma, ba gidan talabijin na gwamnati ba. Aikin da aka ɗora mata shi ne yi wa al'umma hidima ta hanyar aikin jarida mai cin gashin kansa, marar nuna son kai kuma abin dogaro. Shirye-shiryen fadar shugaban ƙasa na yaɗa taron kai tsaye da kuma yadda sashen labarai na SABC abubuwa ne guda biyu masu zaman kansu."

Ta ƙara da cewa SABC na nan daram wajen kiyaye ƙa'idojin adalci, rashin nuna son kai da kuma 'yancin kai na editoci a yadda take gudanar da aikinta, tare da kuma ƙarfafa kyakkyawar dangantakar da ta daɗe tana tsakanin ta da Najeriya.