Shin da gaske gwamnan Kano ya rabu da matarsa Zainab Kwankwaso?

Asalin hoton, Isah Muhammad/FB
Wasu kalaman da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi, sun haifar da cece-ku-ce game da aurensa a yayin wani taro da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar ranar Litinin.
Yayin da yake jawabi a lokacin wani taro na ƴan fansho ranar, gwamnan ya bayyana cikin raha a bainar jama'a da kuma kalamai na gugar zana, sai dai wasu na alaƙanta kalaman nasa da rikicin da ake raɗe-raɗi tsakaninsa da mai ɗakinsa Zainab Musa Kwankwaso.
Ko da yake bai fito fili ya fayyace cewa ga inda kalaman nasa suka dosa ba, amma ana ganin yana martani ne kan tirka-tirkar auren nasu, inda a cikin jawabin nasa ya ce: "wanda ya gane, ya gane".
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da jaridar Daily Nigerian da wasu kafafen yada labarai suka ruwaito a ƙarshen mako cewa Zainab ta shigar da ƙarar neman a raba aurensu a wata kotu da ke Abuja.
Lamarin ya ɗauki hankali matuƙa, sakamakon doguwar alaƙar siyasa da ke tsakanin Gwamna Yusuf da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, wanda mutane ke kallonsa a matsayin wanda ya taimaka masa wajen gina siyasarsa.
Duk da cewa iyalan Kwankwaso da ofishin gwamnan ba su yarda su yi bayani kan ma'anar kalaman gwamnan ba, amma hakan ya ƙara ruruta wutar jita-jitar da ake yi na cewa auren ya mutu.
A cikin bidiyon da mai taimaka masa ya wallafa a shafukan sada zumunta, an ji Abba yana cewa: "Idan farar takarda ce suke buƙata, to mun riga mun ba su ita, kowa ya huta, an gama magana."
Wannan magana ce mutane da dama ke ganin yana nufin "takardar sakin aure" ce.
A al'adar aure da kuma tasirin Musulunci a rayuwar Bahaushe, idan aka ce 'an bai wa matar aure takarda', ana nufin 'an sake ta', wato auren ya mutu.
A lokacin taron gwamnan ya ƙara da cewa: "Kuma za mu ba kwamishinan yaɗa labarai umarni da ya fitar da sanarwa tare da yaɗa ta a shafukan sada zumunta, domin waɗanda ke son cike gurbin da aka bari su gabatar da takardun nema. Wanda ya gane, ya gane."
Masu fassara na ganin cewa Abba na mayar da martani ne ga matarsa, Zainab Musa Kwankwaso, wadda suka shafe shekara 20 da aure, kuma yana shirin ƙara aure.

Asalin hoton, Isah Muhammad Salisu/FB
Wace ce Zainab Musa Kwankwaso?
Bayanai sun ce Zainab Musa Kwankwaso tamkar ƴa ce ga tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata, Rabiu Musa Kwankwaso.
Asalin sunata shi ne Zainab Dahiru Musa, sai dai mahaifinta, wanda yaya ne ga tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso, ya daɗe da rasuwa.
A sanadiyyar haka ne Zainab ta taso a gidan Rabiu Musa Kwankwaso har zuwa lokacin da ya aurar da ita.
Ta auri gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a shekarar 2006, kuma aurensu ya shafe shekara 20 inda suke da ƴaƴa shida.
Ana ganin cewa saɓani ya shiga cikin aurensu ne bayan doguwar taƙaddamar siyasa tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da tsohon jagoransa a siyasa, wanda kuma shi ne ke zaman uba ga matarsa, Rabiu Musa Kwankwaso.
A cewar rahoton jaridar Daily Nigerian, a tsakiyar watan Nuwamban 2026, Zainab ta shigar da ƙarar neman raba aurensu a wata kotu da ke Abuja, inda kotu ta miƙa wa Gwamna Abba sammaci.
Abin da mutane ke cewa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mutane da dama sun yi ta Allah-wadai da sukar matakin gwamnan na fitowa a bainar jam'a yana kalamai da suka shafi al'amarin aurensa da mai ɗakinsa.
Wani mai suna Al'ameen a shafin X ya ce: "Ban ji daɗin yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da sakin matarsa, Hajiya Zainab Musa Kwankwaso, a bainar jama'a a yau ba, amma kuma ba zan ɗora masa dukkan laifin ba.
Tsohuwar matarsa ya kamata ta fi kowa sanin cewa bai kamata ta ruguza auren shekara 20 da 'ya'ya shida saboda siyasa ba. Ni ma ina ɗora wa Kwankwaso alhakin yawancin abin da ya faru.
Bai kamata mutum ya yi amfani da aure a matsayin hanyar mayar da wani tamkar fursuna ko tilasta masa zama ɗan amshin shatarsa a siyasa ba.
Babu shakka Kwankwaso na cikin waɗanda ke da hannu a matsalar. Ba yadda Ganduje da Abba za su juya masa baya ba idan yana mutunta kansa kuma ya fahimci cewa taimaka wa ɗan siyasa ba yana nufin za ka riƙa juya gwamnonin da aka zaɓa yadda kake so ba. Ba za ka sa ran gwamna mai ci ya miƙa maka 'yancinsa da ikon siyasa ba."
Ibrahim Macduff ya ce: "Shin kuna sa ran za ta ci gaba da zama a gidan aurenta alhali mijinta yana shirin cutar da mahaifinta? Ina ta jin mutane na cewa ba 'yar Kwankwaso ba ce ta cikinsa. Wannan lamari ya tabbatar da cewa Kwankwaso ya raine ta kamar sauran 'ya'yansa."
Wani mai suna Sarkin Yaki Na Baba Buhari ya ce: "Ban ji daɗin shigar da al'amuran iyali cikin siyasa da kuma fito da su fili ba. Shekara 20 ba wasa ba ne. Me ya sa za a kai wannan al'amari kotu har a fito da shi fili? Wannan alama ce ta ƙoƙarin ɓata masa suna a siyasa, kuma a nan ne ta yi kuskure."
Shi ma wani mai suna Nosyz Man ya ce: "Kun san irin zafin da mace ke ji idan mijinta ya ci amanar mahaifinta? Mahaifinta ya amince da auren ne saboda irin ƙaunar da yake yi wa Abba, amma duk da irin abubuwan da ya yi masa, Abba ya ci amanarsa. Kwankwaso zai samu ƙarin goyon bayan masu jefa ƙuri'a saboda wannan lamari."



























