Inter Miami na son Guardiola, Silva zai koma Barcelona

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Akwai rashin tabbass game da makomar Marc Cucurella a Chelsea bayan da kungiyoyi da dama suka tuntubi wakilan dan wasan kan barin Stamford Bridge. An ce Atletico Madrid da Barcelona da kuma Real Madrid na daga cikin wadanda ke zawarcin dan wasan na Sifaniya mai shekara 27.(The Athletic - subscription required), external

Liverpool na zawarcin dan wasan RB Leipzig Yan Diomande amma har yanzu ba su cimma matsaya ta baki ba kan cinikin dan wasan na Ivory Coast mai shekara 19. (Sky Sports), external

Newcastle ta bayyana dan wasan bayan Atalanta na Italiya Marco Palestra, mai shekara 21, a matsayin babban dan wasan da take son ta saya a bazara amma za ta iya fuskantar hamayya daga Manchester City da Arsenal da Inter Milan. (Mail), external

Daya daga cikin mutanen da suka mallaki Inter Miami, David Beckham na son ya dauki Pep Guardiola aiki a matsayin sabon kocin kungiyar ta Major League Soccer bayan ya bar Manchester City, sai dai dan kasar Sifaniya zai yi watsi da duk wani tayi na komawa filin wasa nan take.(Mirror), external

Dan wasan Portugal Bernardo Silva na shirin rattaba hannu kan kwantiragin shekara biyu da Barcelona bayan ya bar Manchester City kuma dan wasan mai shekara 31 yana son a kammala cinikin a hukumance kafin karshen mako.(AS - in Spanish), external

Watakila dan wasan Ingila Marcus Rashford, mai shekara 28, ya koma Manchester United a shirye-shiryen kakar wasa ta bana, yayin da komawarsa Barcelona, ​​inda ta kasance aro a kakar wasan da ta gabata, ta gamu da cikas.(Times - subscription required), external

Manchester United na son ta cefanar da Rashford domin taimaka wa sabon kocin kungiyar Michael Carrick' samun kudin musayar 'yan wasa kuma Arsenal da Chelsea da Newcastle da Tottenham na bibiyar halin da ake ciki . Kungiyar dai ba ta son ta sayar da dan wasan ga daya daga cikin manyan abokan hammayarta. (Mirror), external

Nottingham Forest za ta tattauna da dan wasan tsakiya Ibrahim Sangare, mai shekara 28, kan sabon kwantaragi yayin da Manchester United da Besiktas ke zawarcin dan kasar ta Ivory Coast.(Football Insider), external

Dan wasan kasar Ivory Coast Evann Guessand, mai shekara 24, na nazari kan kungiyar da zai koma bayan karewar wa'adin aronsa daga Aston Villa zuwa Crystal Palace don mayar da cinikin na dindindin .(Evening Standard), external

Aston Villa na son ta bar dan wasan Sifaniya Andres Garcia, mai shekara 23, barin kungiyar a matsayin aro a lokacin bazara, inda Valencia da Elche na cikin cikin kungiyoyin da ke zawarcinsa. (Tribuna Deportiva - in Spanish), external

Tottenham ta bayyana dan wasan Eintracht Frankfurt Jean-Matteo Bahoya a matsayin dan wasan da take son ta saya, amma kungiyar ta Bundesliga ba za ta bar dan Faransa mai shekara 21 ya tafi a farashi mai rahusa ba.(Teamtalk), external