Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan sojojin Najeriya biyu da ƴanbidiga suka sace
Sace babban jami'in sojin Najeriya da ya yi murabus, tare da maidakinsa a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya, ya ƙara jefa fargaba a zuciyar ƴan Najeriya dangane da tsaro.
Ƴan Najeriyar dai na cewa idan har ƴanbindiga na da ƙwarin gwiwar da za su iya yin garkuwa da tshon soja to hakan na nufin babu wanda ya tsira.
An dai yi garkuwa da Manjo Janar Rabeh Abubakar, wanda ya taba zama mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa ta Najeriya tsakanin 2015 zuwa 2017, tare da mai ɗakinsa.
Wannan ya sa BBC ta yi duba dangane da manyan sojojin Najeriyar da ƴan bindiga suka taɓa sacewa.
Manjo Janar Rabe Abubakar
A ranar Asabar ɗin ƙarshen mako ne ƴan bindiga suka yi garkuwa da Manjo Janar Rabeh Abubakar, wanda ya taba zama mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa ta Najeriya tsakanin 2015 zuwa 2017, tare da mai ɗakinsa.
Masu garkuwar dai sun yi awon gaba da mutanen guda biyu ne daga cikin matar da suke a lokacin da suke kan hanyarsu ta shiga Katsina daga Kaduna a ranar Asabar ɗin.
Hukumomin sun ce yanzu haka suna bakin kokarinsu wajen ganin yadda za su amso sojan, wanda dan asalin jihar ta Katsina ne amma ya fi yawan zama a birnin Kaduna, kamar yadda mai magana da yawun rundunar sojin Nakeriya Janar Michael Onoja ya sanar.
A baya dai irin wannan yunƙuri na ceto soja daga hannun ƴan bindiga ya ɗauki kwanaki 56, kafin ceto Birgediya Janar Maharazu Tsiga.
Birgediya Janar Maharazu Tsiga
A watan Fabrairun 2025 ne wasu ƴan bindiga suka yi garkuwa da Birgediya Janar, Maharazu Tsiga mai ritaya, a garinsa Tsiga da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bakori da ke jihar Katsina.
Tsiga wanda ya shugabancin hukumar yi wa ƙasa hidima ta Najeriya, NYSC, an yi garkuwa da shi tare da wasu mutum 9.
Bayan kimanin kwana 56 ne kuma sojojin Najeriya suka ce sun ceto tsohon janar ɗin sojan daga hannun masu garkuwar.
Bayan ceto shi ne kuma aka miƙa su ga ofishin Nuhu Ribadu - mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro a Abuja - tare da wasu mutum 18.
Da yake magana bayan isar su ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, tsohon janar ɗin ya bayyana irin wahalhalun da suka sha, ciki har da yadda namun daji ke yawo a kusa da su.
Me sace manyan sojoji ke nufi?
Dakta Bulama Bukarti, mai sharhi kan harkokin tsaro a nahiyar Afirka ya shaida wa BBC cewa sace manyan sojojin da ƴan bindiga suke yi wata ƴar manuniya ce ga girman matsalar da Najeriya ke fuskanta.
"Wannan wata sabuwar alama ce da ke nuna cewa rashin tsaron Najeriya fa bai bar kowa ba kuma alamu na nuna nan gaba Allah kaɗai ya san mutanen da za ta shafa waɗanda ake ganin shafaffu da mai ne a baya," in ji Bulama.
"idan ba mu manta ba shi fa wannan wanda aka kama shi ne tsohon kakakin sojoji wanda kuka sha yin hira da shi a kan matakan tsaro da ake ɗauka, to idan mutum irin wannan za a sace to me ya ragewa sauran talakawa."
Bulama ya kuma ƙara da cewa abu na biyu da wannan al'amari yake nufi shi ne irin bayanan sirrin da ƴan bindiga ke da shi dangane da al'umma.
"Idan ba suna da masu ba su bayanan sirri ba yaya za a yi ace sun san janar na soji na kan hanya har ma su tare shi?"