Abun kunya ne yadda ake ta kashe jama'a a mulkin Abba - Gwarzo

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar hamayya ta NDC, kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Aminu Abdussalam Gwarzo, ya caccaki gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, da ya zarga da yin sakaci, wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'ar jihar.

Yayin wata hira da BBC Hausa, Kwamared Aminu Abdussalam, ya ce abun kaico ne yadda tsaron Kano ya tabarbare fiye da kowacce lokaci a tarihin baya-bayan nan.

A cewarsa ''A karamar hukumar Tsanyawa an kashe gwamman mutane. an kwashe dukiyoyinsu, abubuwan da suka rika faruwa a karamar hukumar Shanono, abubuwan da suke faruwa yanzu a karamar hukumar Gwarzo, an zo daya biyu uku an kwashe dukiyoyin mutane, an kashe wasu, an sace wasu, har yanzu akwai wadanda suna can sama da wata shida a tsare'' inji shi.

''Hatta a kananan hukumomin cikin birni mutanen da aka kashe cikin sati uku zuwa yanzu Allah ne kadai ya san adadinsu, kisa murus, ina zaman lafiyar? ina maganar in an hadu da gwamnatin tarayya Kano za ta samu zaman lafiya?''

Ya kara da cewa ''Ko a ranar da aka rantsar da mataimakin gwamna mutum biyar aka kashe, an ga iyayensu suna ta kuka a talabiin, ga gawarwaki nan muna gani da idonmu, wasu ma sun ce daga baya mutum daya ya sake mutuwa ana cewa mutum shida ne suka mutu, ina tsaron? ina APCn? ina gwamnatin tarayyar?'' inji shi.

Tun da aka fara 'Kano First' matsalar tsaron Kano ta tabarbare

A cewar tsohon mataimakin gwaman na Kano matsalar tsaron da jihar ke fama da ita ta sake tabarbarewa ne tun bayan da gwamnati ta fito da wani ''Izgilanci wai shi Kano First, wanda take ne na 'yan mulkin mallaka, take ne na Amerika. America First da kake ji ai manufar ita ce fifita wasu mutane a kan wasu 'yan America, ba a maganar bakin haure ba a maganar bakake ko 'yan Indiya da dai sauran baki, don haka wannan kwaikwayo da ake so a yi sai a duba shi kansa Trump da ya kawo shi me ya cimma?''

''Idan ka dawo nan Kano sai ka tambaya me taken yake nufi, wai sai a ce da kai ga Shekarau, ga Ganduje, ga Abba, saboda haka Kano ta hadu, suna APC, saboda haka za a samu tsaro, amma a zahiri tunda aka kafa Kano Firt tsaron Kano ya tabarbare'' a cewarsa.

Ya ce gwamnan da kansa ya shaida wa al'ummar jihar cewa Kano First ce za ta kawowa jihar Zaman lafiya, sai dai abun ya zama yaudara.

Ya ce ko shi kansa Trump da ya kawo wannan take bai iya taka wata rawa ta fuskar taimakon kasarsa ba, wadanda basu yi hakan ba sun fishi taka rawa wajen taimakon Amerika.