Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya Wannan 30/05/2026

Wannan shafi ne da kawo muku muhimman bayanan dangane da wainar da ake toyawa a Najeriya da sassan duniya na ranar Asabar 30 ga watan Mayun 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Ƴanbindiga sun sace tsohon mai magana da yawun soji a Katsina

    Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi garkuwa da tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, tare da matarsa a Jihar Katsina.

    Wani rahoto da jaridar Daily Post ta wallafa ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar a yankin Matazu yayin da tsohon jami'in sojan da matarsa ke tafiya zuwa birnin Katsina.

    Maharan sun tare motarsu tare da tafiya da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

    Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa direban motar ya samu raunin harbin bindiga lokacin harin, amma ya yi nasarar tserewa.

    Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina da kuma rundunar sojoji ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

  2. Ƴanbindiga sun sace tsohon mai magana da yawun soji a Katsina

    Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi garkuwa da tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, tare da matarsa a Jihar Katsina.

    Wani rahoto da jaridar Daily Post ta wallafa ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar a yankin Matazu yayin da tsohon jami'in sojan da matarsa ke tafiya zuwa birnin Katsina.

    Maharan sun tare motarsu tare da tafiya da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

    Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa direban motar ya samu raunin harbin bindiga lokacin harin, amma ya yi nasarar tserewa.

    Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina da kuma rundunar sojoji ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

  3. 'Iran ta yi asarar kusan dala biliyan 4 a cibiyar gas ta South Pars'

    Wani ɗan majalisar dokokin Iran, Jafar Pourkabagani, ya bayyana cewa an yi asarar da ta kai kusan dala biliyan 4 a filin gas na South Pars sakamakon yaƙin da aka yi.

    Ya ce wannan ƙiyasi ya fito ne daga haɗin gwiwar ƙwararru da masana daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha, inda suka kuma ƙiyasta cewa ragin aikin da aka samu na haifar da asarar kusan dala miliyan 2 a kowace rana.

    Rahotanni sun nuna cewa a lokacin rikicin, Amurka da Isra’ila sun kai hare-hare kan wuraren South Pars, wanda shi ne mafi girman filin gas a duniya da ke cikin Tekun Fasha.

    Filin na da matuƙar muhimmanci ga samar da makamashi, yayin da Iran ke raba shi da Qatar wadda ke da ɓangaren arewa na filin.

    South Pars mallakin Iran ne, yayin da Qatar ke sarrafa ɓangaren arewacin shi, kuma ita ce ƙasar da ta fi fitar da iskar gas a yankin, inda take samar da kusan kashi 20 cikin 100 na iskar gas ɗin da ake amfani da shi a duniya.

    Wannan ya sa duk wani tasiri a yankin ke iya shafar kasuwar makamashi ta duniya baki ɗaya.

    A gefe guda, wakilin yankunan Bushehr, Genaveh da Daylam ya ce an kai hari sau uku a Cibiyar Kula da Yanayi ta Bushehr, inda aka lalata wasu sassa.

    Ya kuma bayyana cewa filin jirgin saman Bushehr yana da cikakken kayan aiki, amma sake buɗe shi zai dogara ne da samun izinin tsaro daga gwamnati kafin a dawo da zirga-zirgar jirage.

  4. Gwamnonin Najeriya na duba yiwuwar mayar da mafi karancin albashi N100,000

    Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana cewa gwamnoni na nazarin yiwuwar ɗaga mafi ƙarancin albashin ƙasa zuwa Naira 100,000, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.

    AbdulRazaq ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce hauhawar farashi, tsadar rayuwa da matsin tattalin arziƙi da ma'aikata ke fuskanta ne suka sa ake duba batun.

    Ya ce gwamnatocin jihohi na tattaunawa da gwamnatin tarayya da kuma ƙungiyoyin ƙwadago domin cimma matsaya kan sabon tsarin albashi da zai inganta rayuwar ma'aikata tare da tabbatar da cewa jihohi za su iya ɗaukar nauyin biyan albashin.

    A cewarsa, manufar ita ce ƙara ƙarfin sayen kayan masarufi na ma'aikata tare da bai wa gwamnatoci damar ci gaba da aiwatar da ayyukan raya ƙasa da hidimomin jama'a.

    A halin yanzu, mafi ƙarancin albashi a Najeriya na tsaye ne a kan naira 70,000 a wata, yayin da wasu jihohi ke biyan fiye da hakan.

  5. 'Iran ta daina kallon yarjejeniyar nukiliyarta da Amurka a matsayin mafita'

    Tsohon mai ba da shawara ga tsohon shugaban Amurka, Barack Obama, wato Vali Nasr, ya bayyana cewa Iran ta daina kallon yarjejeniyar nukiliyarta da Amurka a matsayin mafita ga matsalolinta na tattalin arziƙi da tsaro.

    A wata maƙala da ya wallafa a jaridar Financial Times, Nasr ya ce Tehran na kallon wasu sassaucin ra'ayi da Amurka ke nunawa a tattaunawar da shakku, har ta kai ga ganin kamar ba za su zama gaskiya ba.

    Nasr ya tunatar da cewa Iran tana da mummunar ƙwarewa daga yarjejeniyar nukiliya ta baya, inda shugaban Amurka Donald Trump ya janye ƙasarsa daga yarjejeniyar JCPOA. Ya kuma ce a lokacin tattaunawar da aka yi da Iran, gwamnatin Trump ta kai hare-hare sau biyu kan ƙasar, lamarin da ya ƙara rage amincewar Tehran ga duk wata sabuwar yarjejeniya.

    Maƙalar da aka yi wa taken "Dalilin da ya sa Iran ta damu kan ko yarjejeniyar yau za ta zama yaƙin gobe" inda ya ce "Iran ta daina kallon yarjejeniyar nukuliyarta a matsayin mafitar matsalolinta ba"

    Vali Nasr ya kuma bayyana cewa matsin lambar da Amurka ke yi na dakatar da Iran daga tace sinadarin uranium yana ƙara tabbatar wa Tehran cewa manufar Washington ita ce raunana ƙarfin kariyar Iran ta hanyar diflomasiyya kafin komawa ga amfani da ƙarfi.

    Ya ce duk da cewa Amurka da Iran na iya cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen wannan rikici, samun wata yarjejeniya mai ɗorewa kan makomar Mashigar Hormuz da shirin nukiliyar Iran zai kasance babban ƙalubale.

    A halin yanzu, ƙasashen biyu na ci gaba da tattaunawa inda Iran ke neman zaman lafiya mai ɗorewa, yayin da Amurka ke cewa manufarta ita ce tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba.

  6. Sojojin Najeriya sun ceto mutum 31 da aka sace a Zamfara

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 31 da aka yi garkuwa da su tare da kashe 'ƴan ta'adda'biyar a wasu hare-haren da suka kai a jihohin Zamfara da Katsina.

    Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar 29 ga Mayun 2026.

    A cewar sanarwar, a Jihar Zamfara dakarun sun ceto mutanen ne a yankin Bagega zuwa Kawaye da ke ƙaramar hukumar Anka bayan wani samame ta sama da rundunar ta kai kan maɓoyar 'yan ta'adda da ke yammacin dajin Bagega.

    Mutanen da aka ceto sun fito ne daga ƙananan hukumomin Maga, Gummi, Zuru, Wasugu, Bukuyyum da Anka da ke jihohin Zamfara da Sokoto, bayan sun shafe makonni da dama a hannun masu garkuwa da mutane.

    Rundunar ta ce an ba su kulawar lafiya kafin a mayar da su ga iyalansu.

    Haka kuma, a wani samame ta daban a yankunan Maradun da Gidan Dan Jaja na Zamfara, sojojin sun yi artabu da 'yan ta'adda inda suka kashe biyu daga cikinsu tare da lalata sansanoninsu.

    Rundunar ta kuma ƙwato wasu bindigogi da aka ƙera a gida da kuma babura hudu da ake zargin masu laifin na amfani da su wajen gudanar da hare-hare.

    A Jihar Katsina kuwa, dakarun sun tare wasu 'yan ta'adda a yankunan Ruwan Godiya da titin Sayaya da ke ƙaramar hukumar Matazu yayin da suke kan hanyarsu ta kai hari.

    Bayan musayar wuta mai zafi, sojojin sun kashe 'yan ta'adda uku tare da kwato babura da wasu harsasai.

  7. Majalisar dokokin Iran na shirin amincewa da ƙudirin kula da mashigar Hormuz

    Wani mamba a kwamitin shugabancin Majalisar Dokokin Iran, Alireza Salimi, ya bayyana cewa majalisar na shirin amincewa da wani ƙudiri da zai bai wa Iran cikakken iko da kula da Mashigar Hormuz.

    Ya ce an gudanar da cikakken nazari kan ƙudirin tare da samun ra'ayoyi daga hukumomi daban-daban da suka haɗa da ɓangarorin tattalin arziki da sufuri da tsaro.

    A wata hira da kamfanin dillancin labarai na ISNA, Salimi ya ce nan ba da jimawa ba za a amince da ƙudirin tare da mayar da shi doka.

    Sai dai har yanzu ba a bayyana yawan 'yan majalisar da suka sanya hannu kan ƙudirin ba, ko kuma ranar da za a tattauna shi a majalisar.

    Tun bayan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran, zaman Majalisar Dokokin Iran ya tsaya a hedkwatarta ta dindindin.

    A halin yanzu kuma, zirga-zirgar jiragen ruwa ta ragu sosai a Mashigar Hormuz, wanda ke tsakanin ruwan Iran da Oman.

    Salimi ya kuma ce ɓangaren Oman ya nuna amincewa ta farko kan shirin.

    Ya ƙara da cewa Mashigar Hormuz ya fi wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran muhimmanci da daraja fiye da makaman nukiliya masu yawa, yana mai jaddada cewa batun kula da mashigar ba abu ne da Iran za ta tattauna ko ta yi sulhu a kansa ba.

    A gefe guda kuma, Amurka ta buƙaci a ci gaba da buɗe mashigar ga zirga-zirgar jiragen ruwa na kasa da kasaa

  8. PDP ta tsayar da Goodluck Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa

    Jam’iyyar PDP tsagin Kabiru Tanimu Turaki ta tsayar da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.

    Jam’iyyar ce ta sanar da hakan bayan ta wallafa takardar shaidar tsayawa takarar Goodluck Jonathan a babban zaɓen ƙasar na 2027.

    Farida Umar, Mataimakiyar sakataren yaɗa labaran jam'iyyar PDP ɓangaren Turaki ta ƙasa ta kuma shaida wa BBC batun tsayar da Jonathan a matsayin wanda zai kara da shugaba Tinubu a zaɓen 2027.

    Lamarin ya biyo bayan canjin wurin gudanar da taronta na ƙasa da jam’iyyar ta shirya a Abuja a yau Asabar, 30 ga watan Mayu, bayan da ‘yan sanda suka hana mambobinta shiga A Class Hotel, wurin da aka fara tanada domin gudanar da taron.

    Daga bisani jam’iyyar ta sauya wurin taron cikin gaggawa, inda aka kammala shi cikin ƙanƙanin lokaci.

    A wajen taron, an gabatar da matakin tsayar da Jonathan, wanda aka ce ya samu goyon bayan manyan jiga-jigan ɓangaren Turaki na jam’iyyar.

    Rahotanni sun ce an mika takardar shaidar tsayawa takara ga Fred Agbedi, wanda ya karɓa a madadin tsohon shugaban ƙasar, yayin da manyan mambobi irin su Prof. Jerry Gana, Tanimu Turaki da Adolphus Wabara suka halarci taron. Jam’iyyar ta ce duk da taƙaddama da cikas, za ta ci gaba da shirinta na siyasa domin tunkarar zaɓen 2027.

    Tun dai lokacin da jam'iyyar ta bayyana cewa ta tattance Jonthan har zuwa lokacin da ta tabbatar da cewa shi ta tsayar a matsayin ɗan takararta ba, ba a ji ta bakin tsohon shugaban ƙasar ba akan ko ya yarda zai sake tsayawa takara a shekarar 2027 ko a'a

    Jonathan dai yayi shugabancin ƙasar daga shekarar 2010 zuwa 2015.

    Shine shugaban ƙasar da aka taɓa kayarwa a kan mulki kuma ya amince da kayarwar da aka yi masa.

  9. Trump ya sake “cin amanar diflomasiyya” karo na uku - Iran

    Mohsen Rezaei, tsohon kwamandan dakarun juyin juya hali na Iran, ya zargi Donald Trump da “cin amanar diflomasiyya” sau uku, yana mai cewa ci gaba da takunkumin toshe hanyoyin jiragen ruwa kan Iran da kuma gabatar da “matsananciyar bukata” a tattaunawar sulhu suna lalata duk wani yunƙuri na zaman lafiya.

    Bayan rahotannin kafafen yaɗa labarai na Iran da ke cewa Mojtaba Khamenei ya karbi jagorancin ƙasar daga mahaifinsa a matsayin sabon shugaban addinin ƙasar na uku, an ce ya naɗa Rezaei a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin soja.

    A wani rubutu da ya wallafa a dandalin X, Rezaei ya ce Trump ya sake nuna cewa ba mai sha’awar zama mai sasanci ba ne, yana bin wasu manufofi daban da tattaunawar sulhu.

    Rahotanni daga ɓangaren Iran da Amurka sun sha zargin Washington da kaddamar da hare-haren soja a lokacin da ake tattaunawa da Iran, musamman a farkon Yakin Kwanaki 12 da kuma a wasu sabbin rikice-rikice, inda suke cewa hakan na nuna “cin amanar diflomasiyya.”

  10. 'Harin Iran a Kuwait ya jikkata sojojin Amurka da dama'

    Rahotanni daga kafar labarai ta Bloomberg sun ce Iran ta kai hari da makami mai linzami kan wani sansanin sojin sama a Kuwait cikin awanni 24 da suka gabata, lamarin da ya jikkata sojojin Amurka da dama.

    Rahoton ya ce wani jami’i da ba a bayyana sunansa ba ne ya bayyana hakan inda ya ce an kuma lalata jiragen leƙen asiri guda biyu na MQ9 Reaper a harin.

    An ce an samu nasarar dakile makami mai linzami nau'in Fateh-110, amma tarkace daga harin sun faɗa cikin sansanin sojin Ali Salem, inda suka haddasa lalacewa.

    Majiyoyin tsaro sun kuma bayyana cewa wannan hari na zuwa ne a lokacin da ake samun tashin hankali a yankin Tekun Farisa, inda Amurka da Kuwait suka riga suka tabbatar da wani hari makamancin haka a kwanakin baya, ko da yake lokutan rahotannin ba su yi daidai ba.

    A baya, hedikwatar rundunar sojin Amurka ta ce an harba makami mai linzami daga Iran zuwa Kuwait a ranar 27 ga Mayu, wanda aka dakile cikin nasara.

    A gefe guda, rundunar juyin juya halin Iran ta kai hari ne a matsayin martani ga hare-haren Amurka a kusa da Bandar Abbas, inda ta ce ta nufi sansanin da ake zargin ya zama tushen farmakin.

    Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ke ganawa da mashawartansa kan batun Iran, yayin da Fadar White House ta ce duk wata yarjejeniya da Iran dole ta "amince da sharruddan Amurka".

  11. Iran ta ce sake buɗe intanet ga jama'a mataki ne na kare haƙƙoƙinsu

    Mai magana da yawun gwamnatin Iran, Fatemeh Mohajerani, ta bayyana cewa matakin da gwamnati ta ɗauka na sake buɗe intanet na duniya ga jama'a ba kawai cire wata takunkumin fasaha ba ne, illa wani mataki ne na tabbatar da haƙƙoƙin al'umma.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar, Mohajerani ta ce katse intanet din da aka yi a watannin baya ya samo asali ne daga barazanar tsaro da hare-haren abokan gaba da kuma yanayin da ya biyo bayan hakan.

    Ta ƙara da cewa kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadi cewa babu wani yanayi na musamman da zai zama dindindin.

    Bayan shafe watanni ana fama da katsewar intanet a Iran sakamakon yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila, an fara mayar da wasu ayyukan intanet a ƙasar kwanaki biyu da suka gabata.

    Tun da farko, gwamnatin Shugaba Masoud Pezeshkian ta yi kira sau da dama da a dawo da intanet, tana mai gargadin cewa katsewar na haifar da illa ga harkokin ilimi, tattalin arziki da kuma kasuwanci a ƙasar.

  12. Shugaban Amurka na cikin ƙoshin lafiya - Likitan Trump

    Likitan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa shugaban na cikin ƙoshin lafiya kuma yana da cikakken ƙarfin da zai ci gaba da gudanar da ayyukansa na shugabancin ƙasa.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Fadar White House ta fitar a ranar Juma'a.

    Dokta Sean Barbabella ya ce gwaje-gwajen lafiya da aka yi wa Trump a wannan makon sun nuna cewa har yanzu yana da ɗan kumburi kaɗan a ƙafafunsa da kuma wasu ƙananan tabo a hannuwansa, amma ba su da wata illa ga lafiyarsa.

    A cewar likitan, zuciyar Trump, huhunsa, tsarin jijiyoyinsa da kuma sauran sassan jikinsa suna aiki yadda ya kamata kuma cikin yanayi mai kyau.

    Ya ƙara da cewa shugaban yana da cikakken ƙarfi da lafiya domin ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayin shugaban ƙasa kuma babban kwamandan rundunar sojin Amurka.

    An gudanar da binciken lafiyar Trump na shekara-shekara ne a ranar 26 ga Mayu.

    Trump, wanda zai cika shekaru 80 a watan Yuni, shi ne mutum mafi tsufa da ya taɓa hawa kujerar shugaban ƙasar Amurka.

  13. Shugaban WHO ya kai ziyara yankin da cutar Ebola ta fi ƙamari a DR Congo

    Babban Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, na ziyarar aiki a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo domin ƙarfafa ƙoƙarin da ake yi na daƙile yaduwar cutar Ebola.

    Bayan ganawa da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa a birnin Kinshasa, ya nufi lardin Ituri da ke gabashin ƙasar, wanda shi ne cibiyar barkewar cutar a halin yanzu.

    A yayin ziyarar, Dr Tedros zai duba halin da ake ciki a yankin tare da tattauna hanyoyin ƙara ƙaimi da daidaita ayyukan yaƙi da cutar tsakanin gwamnatin Kongo da ƙungiyoyin agaji na duniya.

    Ya bayyana cewa akwai ƙalubale da dama wajen shawo kan barkewar cutar, saboda Ebola cuta ce mai wuya, kuma babu rigakafin da aka amince da shi gaba ɗaya domin dakile ta.

    Haka kuma yankin da cutar ta bulla na fama da rikice-rikice da yawan mutanen da ke gudun hijira, lamarin da ke taimakawa wajen yaɗuwar cutar.

    Hukumar WHO ta ce an samu ci gaba wajen gwajin cutar da kuma isar da kayan aikin jinya zuwa yankin.

    Haka kuma ana ci gaba da gina cibiyoyin kula da masu cutar, sai dai hukumar ta ce har yanzu akwai aiki mai yawa da ya rage kafin a samu nasarar shawo kan barkewar Ebola gaba ɗaya.

  14. Cire tallafin mai ya ceci Najeriya daga durƙushewar tattalin arziƙi - Tinubu

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce matakin da gwamnatinsa ta ɗauka na cire tallafin man fetur ya ceci Najeriya daga fadawa cikin matsananciyar matsalar tattalin arziƙi, tare da shimfiɗa tubalin farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar.

    Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin da ya karɓi bakuncin wasu gwamnoni da suka kai masa ziyarar taya murnar bikin babbar Sallah da kuma cika shekara uku da hawansa mulki.

    Ya ce duk da cewa cire tallafin ya jawo wa 'yan Najeriya ƙalubale da raɗaɗi, matakin ya zama dole domin ceto ƙasar daga durƙushewar kuɗaɗenta da kuma dawo da daidaito a tattalin arziki.

    Tinubu ya ce "tsawon shekaru Najeriya na kashe kuɗaɗe masu yawa wajen biyan tallafin man fetur wanda a cewarsa ya fi amfanar kaɗan daga cikin jama'a, yayin da muhimman fannoni kamar noma da ababen more rayuwa suka rasa jarin da suke buƙata. "

    Ya ƙara da cewa "tattalin arzikin ƙasar na nuna alamun farfaɗowa, inda noma da ayyukan gine-gine ke ci gaba da bunƙasa."

    Shugaban ya kuma yaba wa gwamnonin jihohi bisa haɗin kai da goyon bayan da suka ba gwamnatinsa wajen aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki.

    Ya ce "a yanzu jihohi ba sa fama da matsalar neman tallafi daga gwamnatin tarayya domin biyan albashi kamar yadda aka saba a baya."

    A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yaba wa jajircewar Tinubu wajen tinkarar matsalolin da ke tattare da tallafin mai, yana mai cewa shugaba ya nuna ƙarfin hali wajen ɗaukar matakan gyaran tattalin arzikin ƙasar.

  15. Har yanzu ba a kammala wata yarjejeniya ba da Amurka - Iran

    Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya bayyana cewa har yanzu ba a kammala wata yarjejeniya batsakanin Iran da Amurka ba.

    A wata hira da gidan talabijin na gwamnatin Iran, Baghaei ya ce Iran da Oman ne ke da ikon yanke hukunci kan yadda ake gudanar da harkokin mashigar Hormuz.

    Ya kuma ce a halin yanzu hankalin Iran ya karkata ne wajen kawo ƙarshen yaƙin da ake ciki, kuma babu wata tattaunawa da ake yi kan shirin nukiliyar ƙasar.

    Baghaei, wanda aka naɗa a matsayin mai magana da yawun tawagar masu tattaunawar Iran, ya ce kasashen Yamma ba za su iya yi wa Iran magana da salon umarni ba. Ya ce Iran tana yanke hukunci ne bisa muradun da haƙƙoƙin al'ummarta.

    Kalaman nasa sun zo ne bayan da Amurka ta fitar da wasu sharuɗɗan da ta ce dole Iran ta cika. Waɗannan sun haɗa da tabbatar da cewa Iran ba za ta mallaki makaman nukiliya ba, bude mashigar Hormuz ba tare da karɓar kuɗin wucewa ba da kawar da duk wasu nakiyoyi da ke cikin mashigar, da kuma cire tarin sinadarin uranium da Iran ta wadatar, tare da haɗin gwiwar Amurka da sa ido daga Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA).

  16. Assalamu alaikum

    Marabanku masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Aisha Babangida ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku ci gaba da ta tafka muhawara kan labaran da muke wallafa a shafukanmu na sada zumunta