'Harin Iran a Kuwait ya jikkata sojojin Amurka da dama'

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga kafar labarai ta Bloomberg sun ce Iran ta kai hari da makami mai linzami kan wani sansanin sojin sama a Kuwait cikin awanni 24 da suka gabata, lamarin da ya jikkata sojojin Amurka da dama.
Rahoton ya ce wani jami’i da ba a bayyana sunansa ba ne ya bayyana hakan inda ya ce an kuma lalata jiragen leƙen asiri guda biyu na MQ9 Reaper a harin.
An ce an samu nasarar dakile makami mai linzami nau'in Fateh-110, amma tarkace daga harin sun faɗa cikin sansanin sojin Ali Salem, inda suka haddasa lalacewa.
Majiyoyin tsaro sun kuma bayyana cewa wannan hari na zuwa ne a lokacin da ake samun tashin hankali a yankin Tekun Farisa, inda Amurka da Kuwait suka riga suka tabbatar da wani hari makamancin haka a kwanakin baya, ko da yake lokutan rahotannin ba su yi daidai ba.
A baya, hedikwatar rundunar sojin Amurka ta ce an harba makami mai linzami daga Iran zuwa Kuwait a ranar 27 ga Mayu, wanda aka dakile cikin nasara.
A gefe guda, rundunar juyin juya halin Iran ta kai hari ne a matsayin martani ga hare-haren Amurka a kusa da Bandar Abbas, inda ta ce ta nufi sansanin da ake zargin ya zama tushen farmakin.
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ke ganawa da mashawartansa kan batun Iran, yayin da Fadar White House ta ce duk wata yarjejeniya da Iran dole ta "amince da sharruddan Amurka".
















