Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
PSG beat Arsenal in shootout to retain Champions League
Takaitaccen Bayanin Wasa
UEFA Champions League -
Final
Paris Saint-Germain
Arsenal
After extra time
Paris Saint-Germain win 4 - 3 on penalties
Full Time Paris Saint-Germain 1 , Arsenal 1,Half Time Paris Saint-Germain 0 , Arsenal 1
Key Events
Paris Saint-Germain
- O. DembéléPenalty 65 minutes
Arsenal
- K. HavertzGoal 6 minutes
Assists
Arsenal,L. Trossard (6 minutes)
Venue:Puskás Aréna
Attendance:61,035
Taƙaitattu
- Champions League: Wa zai lashe kofin tsakanin PSG da Arsenal?
- Wannan shi ne wasa na takwas da za su kara, kowacce ta yi nasara biyu
- Champions League: Damar da PSG ke da ita a kan Arsenal
- PSG ce ke rike da kofin zakarun Turai na bara mai fatan ɗaukar biyu a jere
- Dabarun da Arsenal za ta iya amfani da su wajen lashe Champions League
- Arsenal ba ta taɓa lashe Champions League ba a tarihinta
- Ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp
- Za ku iya tafka muhara a shafnmu na sada zumunta a BBC Hausa Facebook
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu
PSG ta kara lashe Champions League karo na biyu a jere
Arsenal za ta ci gaba da jiran lashe Champions League
Labarai da dumi-dumi, Paris St German ta lashe Champions League karo na biyu a jere, Bugun fenariti 4-3 bayan tashi 1-1
, Bugun fenariti: PSG 4-3 Arsenal
Gabriel ya buga kwallo ta yi saman raga.
Akwai kuma ta Nuno Mendes (PSG) da ya barar
, Bugun fenariti: PSG 4-3 Arsenal
Lucas Beraldo ya buga ya ci
, Bugun fenariti: PSG 3-3 Arsenal
Gabriel Martinelli ya buga ta fada raga
, Bugun fenariti: PSG 3-2 Arsenal
Achraf Hakimi ya buga ya ci
, Bugun fenariti: PSG 2-2 Arsenal
Declan Rice ya buga ya ci
, Bugun fenariti: PSG 2-1 Arsenal
Eberechi Eze ya buga ta yi fadi
, Bugun fenariti: PSG 2-1 Arsenal
Desire Doue ya buga ya ci
, Bugun fenariti: PSG 1-1 Arsenal
Shima Viktor Gyokeres ya buga ya ci
, Bugun fenariti: PSG 1-0 Arsenal
Ramos na PSG zai fara buga fenariti - ya kuma buga ya ci
, Paris St-Germain 1-1 Arsenal
Sau huɗu ne ƙungiyoyin Ingila suka taɓa lashe Kofin Turai / UEFA Champions League ta hanyar bugun fenariti.
Shin za mu ƙara Arsenal a wannan jerin?
- 1983-84 - Liverpool 1-1 Roma (4-2 on pens, Rome, Italy)
- 2004-05 - Liverpool 3-3 AC Milan (3-2 on pens, Istanbul, Turkey)
- 2007-08 - Manchester United 1-1 Chelsea (6-5 on pens, Moscow, Russia)
- 2011-12 - Chelsea 1-1 Bayern Munich (4-3 on pens, Munich, Germany
An tashi wasan sai bugun fenariti, Paris St-Germain 1-1 Arsenal
An kammala minti 90 sakamakon 1-1 an kuma yi karin lokaci amma sakamakon bai canja ba.
Kenan za a yi bugun fenariti da yan wasa biyar biyar daga kowacce kungiya.
Shin waye zai lache Champions League?
, Paris St-Germain 1-1 Arsenal
Muna minti 116 duk wanda ya ci kwallon ban ji za a farke domin kowa ya gaji so yake a tashi daga wasan.
, Paris St-Germain 1-1 Arsenal
Arsenal na tsare gida watakila sun amince da Raya zai cece su a bugun fenariti kenan - komai zai iya faruwa idan ta kai ga fenariti, sai mai rabo.
Yadda ake gara wasan tsakanin kungiyoyin biyu, Paris St-Germain 1-1 Arsenal
Za a karasa minti 15, Paris St-Germain 1-1 Arsenal
Za a karasa minti 15 idan ba ci a yi bugun fenariti