, Daga Jaridu
Tottenham ta sake nuna sha'awarta a kan cinikin dan wasan gaba na gefe na Manchester United Savinho, dan Brazil mai shekara 22, a kan fam miliyan 60. (Mail), external
Liverpool ta fi son maye gurbin Mohamed Salah, da matashin dan wasan RB Leipzig, Yan Diomande, mai shekara 19, dan Ivory Coast, wanda kwantiraginsa ya tanadi damar sayar da shi a kan fam miliyan 86.
Haka kuma daga cikin zabin da Liverpool din ke dubawa akwai dan wasan Newcastle da Ingila Anthony Gordon, mai shekara 25, da kuma dan gaban Paris St-Germain da Faransa Bradley Barcola, mai shekara 23. (Telegraph)
Sai dai kuma suma zakarun gasar Jamus - Bundesliga - Bayern Munich suna son Gordon din na Newcastle, kuma Bayern za ta iya hadawa da mai tsaron ragar Jamus Alexander Nubel mai shekara 29, ta bayar a cinikin na Gordon. (Bild)
Barcelona za ta yi sabuwar tattaunawa da Manchester United kafin wasan Kofin Duniya, domin kammala cinikin Marcus Rashford, inda kungiyar ta Sifaniya tauni ta kammala yarjejeniya tsakaninta da dan gaban na Ingila mai shekara 28 (Talksport)