Zanga-zanga ta ɓarke a Oyo kan sace ɗaliban jihar
Ɗaruruwan malaman makaranta da iyaye da ƙungiyoyin matasa sun fantsama titunan jihar Oyo domin yin zanga-zanga kan abin da suka kira rashin taɓuka komai daga gwamnati don ceto ɗalibai da wasu malamansu da ƴanbindiga suka sace makwanni biyu da suka gabata.
Masu zanga-zangar ɗauke da alluna da ƙaton allo ɗauke da hotunan yara, wasu cikin tsoro wasu kuma na nuna jikinsu da tabbai.
Wasu yara ƴan shekara 12 zuwa 15 suma sun bi sahun masu zanga-zangar.
Zanga-zangar wani ɓangare ne na matakan malaman makarantun gwamnati karƙashin ƙungiyar malamai ta NUT na matsa wa gwamnati lamba ta kuɓutar da ɗalibai da malamansu da aka sace a watan da ya gabata.