KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 01/06/2026.

  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Haruna Kakangi

  1. Amurka ta kai 'hare-haren martani' kan Iran

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Amurka sun ce sun kai hare-hare kan wuraren samar da jirage marasa matuƙa na Iran a birnin Goruk da kuma tsibirin Qeshm a ƙarshen mako.

    Rundunar sojin Amurka a gabas ta tsakiya ta bayyana a shafinta na sada zumunta cewa an kai hare-haren ne a matsayin martani ga abin da ta kira “Matakan tsokana daga Iran”, waɗanda suka haɗa da harbo wani jirgin leƙen asiri marar matuƙi na Amurka, wanda take ikirarin yana shawagi ne a sararin samaniyarta.

    A matsayin martani, dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran sun ce sun kai hari kan wani sansani da sojojin Amurka ke amfani da shi, sai dai ba su bayyana sunan sansanin ba.

    Tun da fari, Kuwait ta ce ta dana garakuwar tsaron sararin samaniyarta, don harbo wani makami mai alinzamia da Iran din ta harba.

  2. Mutum huɗu sun warke daga cutar Ebola

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin lafiya a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun yi murnar warkewar mutum huɗu da suka tsira daga cutar Ebola.

    Suna daga cikin mutanen farko da aka sallama daga cibiyoyin jinya tun bayan barkewar cutar da aka samu a yanzu.

    A wani biki da aka gudanar a Bunia, wanda shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya halarta, an yaba wa mutanen da suka warke wadanda dukkaninsu ma’aikatan lafiya ne bisa jarumtar da suka nuna.

    Mutanen sun kamu da Ebolar ne yayin da suke kula da masu cutar, kuma sun ce sun ji dadi kwarai-kwarai da suka samu lafiya.

  3. Barkan mu da warhaka!

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye na ranar Litinin 1 ga watan Yuni 2026.

    Wannan shafi zai kawo muku duk muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya tsokaci kan abubuwan da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta: facebook, X, Instagram da kuma YouTube.