Yadda bidiyon ƴan agajin Izala ya tayar da ƙura a Najeriya

Kungiyar Izala ta JIBWIS da 'yan agajin Izala
    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta tun safiyar Litinin, wanda aka ga wasu matasa sanye da kayan aikin 'yan agaji da ake dangantawa da ƙungiyar Izala ta JIBWIS, ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya.

A cikin bidiyon, an ga matasan suna fareti tare da furta wasu kalamai a salon waƙa, waɗanda suka sa wasu 'yan Najeriya nuna fargabar cewa za su iya "haddasa tarzoma".

Bidiyon, wanda tsawonsa ya kai kusan minti ɗaya, wani mataimaki na musamman ga ministan Abuja kan yaɗa labarai, Lere Olayinka, ne ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X.

Kalaman da aka ji matasan suna furtawa a yayin faretin sun jawo martani daga 'yan Najeriya da dama, inda wasu suka nuna ɓacin rai tare da kiran a ɗauki mataki kan lamarin.

Sai dai wasu sun yi ƙoƙarin kare matasan, suna mai cewa an fahimci kalaman nasu ba daidai ba.

Haka kuma, an yi ta yaɗa iƙirarin cewa an ɗauki bidiyon ne tun a shekarar 2020. Sai dai har yanzu babu tabbacin lokacin da aka ɗauki bidiyon.

Wasu daga cikin waɗanda suka mayar da martani sun buƙaci hukumomi su gayyaci matasan domin gudanar da bincike, yayin da wasu suka yi kira da a ɗauki matakan da suka dace kan ƙungiyar, bisa zargin cewa kalaman na iya "nuna ƙiyayya" ga wasu.

A nata ɓangaren, ƙungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'ah Wa'iƙamatus-Sunnah (JIBWIS), wadda ake danganta matasan da ita, ta ce ta ɗauki mataki kan lamarin.

Me ƴan Najeriya ke cewa?

Bidiyon ya jawo martani daban-daban daga 'yan Najeriya, inda wasu suka yi Allah wadai da kalaman da aka ji a ciki, tare da kira ga hukumomin tsaro su gudanar da bincike kan lamarin.

Tsohon Sanatan Najeriya, Shehu Sani, ya bayyana kalaman da aka ji a bidiyon a matsayin abin Allah wadai, musamman saboda barazanar da ya ce wani matashi ya yi wa Kiristoci.

A saƙon da ya wallafaa shafinsa na Facebook, Sanata Shehu Sani ya ce ya kamata a gudanar da bincike kan matashin tare da ɗaukar matakin da ya dace a kansa.

Sai dai ya jaddada cewa ra'ayin matashin bai kamata a ɗauke shi a matsayin ra'ayin ƙungiyar 'yan agajin JIBWIS ko mambobinta ba.

Ya ce JIBWIS ƙungiya ce da ba ta taɓa goyon bayan tashin hankali ko haɗa kanta da ayyukan da ke nuna ƙiyayya ga mabiya wani addini ba, yana mai cewa ra'ayin mutum ɗaya bai kamata a ɗora wa ƙungiya ko addini baki ɗaya ba.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Shi ma Bashir Ahmad, tsohon mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, ya bayyana damuwa kan bidiyon.

A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce bidiyon, wanda ba a bayyana lokacin ɗaukar sa ba, ya nuna wasu mambobin ƙungiyar agajin JIBWIS/Izala suna rera waƙar ƙarfafa gwiwa mai ɗauke da kalaman tunzura jama'a.

Ya ce "irin waɗannan kalamai ba su da gurbi a koyarwa a addinin Musulunci..ina kira ga hukumomin tsaro su binciki bidiyon domin gano gaskiya da ɗaukar mataki..".

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Sai dai ba kowa ne ya goyi bayan kiraye-kirayen ɗaukar mataki kan ƙungiyar ba.

Wasu masu amfani da shafin X sun yi zargin cewa ana ƙoƙarin amfani da bidiyon wajen ɓata sunan Izala, suna mai cewa ƙungiyar ba ta da alaƙa da tashin hankali.

@oil_shaeikh ya ce: "Ba a taɓa sanin Izala da tashin hankali ba. Ba ƙungiya ce mai son tayar da hankali ba, kamar yadda kai da mutanen da ke tare da kai kuke ƙoƙarin nuna ta. Manufarku ba za ta yi tasiri ba."

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 3

@abbkar_ai shi ma ya ce: "An ɗauki wannan bidiyon ne a shekarar 2020. Yau shekara shida ke nan da faruwar lamarin.

"Munafukai a cikin al'ummar Musulmi da kuma waɗanda ke ɗaya ɓangaren sun tono wannan batu ne domin tayar da hankula, sukar addinin Musulunci da raba kan 'yan Najeriya, don cimma manufarsu. "In Allah ya yarda, za a kunyata ku."

Abin da ƙungiyar Izala ta ce kan bidiyon ƴan agajin

Sheikh Bala Lau
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'ah Wa'iƙamatus-Sunnah (JIBWIS), wadda aka fi sani da Izala, ta yi Allah wadai da bidiyon, tana mai cewa ba ta amince da kalaman da aka ji a ciki ba.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya buƙaci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), rundunar 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro su gudanar da bincike cikin gaggawa, domin gano waɗanda ke da hannu a lamarin tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi bisa doka.

A cikin sanarwar da ɗaya daga cikin jami'an yaɗa labaran ƙungiyar, Ibrahim Shehu Giwa, ya fitar a ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, Sheikh Bala Lau ya ce: " Muna kira ga jami'an tsaro na DSS da 'yan sanda su kama wanda ya yi bidiyon, sanye da kayan agaji, yana wasu jawabai cewa a ba su AK-47, su je Enugu ranar Lahadi, lokacin motsa jiki, domin kai hari.

Sanarwar ta ce Sheikh Bala Lau ya nesanta ƙungiyar da kalaman tunzura jama'a da aka ji a bidiyon, yana mai jaddada cewa barazana da kiran tashin hankali kan wata al'umma ba su cikin manufofi da koyarwar ƙungiyar.

Ya kuma ce kasancewar mutum sanye da kakin aikin 'yan agajin JIBWIS ko kuma bayyana tare da mambobinta ba yana tabbatar da cewa yana magana ko aiki ne da izinin ƙungiyar ba.

Shugaban ya nuna damuwa cewa akwai yiwuwar wasu mutane na ƙoƙarin amfani da lamarin domin ɓata wa ƙungiyar suna, yana mai kira ga hukumomin tsaro su binciki yanayin da aka ɗauki bidiyon, da waɗanda ke ciki, alaƙarsu da ƙungiyar da kuma manufarsu.

"Ko da yake an gan shi sanye da kakin aikin 'yan agajinmu, kuma an gan shi a cikinmu, hakan ba yana nufin cewa ba turo shi aka yi domin ya ɓata wa ƙungiyar suna ba."

Haka kuma, a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin X, an ji shugabannin ƙungiyar, ciki har da Sheikh Abdullahi Bala Lau da Sheikh Kabiru Gombe, suna magana kan lamarin tare da kira ga hukumomi su kama waɗanda ke da hannu a bidiyon.

Amnesty International ta buƙaci a yi bincike

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Amnesty International ta buƙaci hukumomin Najeriya su gudanar da bincike kan bidiyon da ke sanye da kayan 'yan agaji da ake dangantawa da ƙungiyar Izala, waɗanda aka gani suna fareti tare da rera kalaman kira ga tashin hankali.

A cikin sanarwar, Amnesty International buƙaci hukumomi su binciki waɗanda suka jagoranci faretin, su gano waje da lokacin da aka ɗauki bidiyon, tare da nazarin abubuwan da ke cikinsa da kuma manhajojin koyarwa da ake amfani da su a irin waɗannan shirye-shiryen matasa.

Ta kuma ce ya kamata a ɗauki mataki kan duk wata ƙungiya ko mutum da aka samu da hannu a irin waɗannan ayyuka.

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Amnesty International ta ƙara da cewa ya kamata a kare yaran da abin ya shafa daga cusa musu wani tsattsauran ra'ayi, tare da samar musu da tallafin da ya dace ta fuskar ilimi da lafiyar tunaninsu.

Ƙungiyar ta yi nuni da dokar kare haƙƙin yara ta Najeriya da kuma yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan haƙƙin yara, tana mai cewa yara na da haƙƙin kariya daga tashin hankali, kalaman ƙiyayya da kuma ɗaukar su ko horas da su a ayyukan da suka yi kama da na rundunonin soja.