Gine-gine 8 mafiya ƙayatarwa a duniya

Asalin hoton, Pompidou Center, Malaga/Getty Images
Tsawon lokaci mai yawa, masu zana gine-gine suna amfani da launi a matsayin wata muhimmiyar hanya wajen ƙara wa ayyukansu armashi da kuma jan hankalin mutane.
An daɗe ana amfani da launuka domin nuna farin ciki da kuma ƙawata wurare tun dubban shekaru da suka gabata.
Mutanen Neanderthal da suka rayu dubbai na shekaru da suka wuce, sun kasance suna ƙawata kogunan da suke zaune da launuka da suka samo daga ƙasa da kuma ma'adanai daban-daban.
Daga baya, tsoffin al'ummomin Masar da Girka sun gina wurare masu kayatarwa waɗanda aka yi wa ado da launuka masu haske da kyau. Haka kuma Romawa sun yi amfani da launuka iri-iri wajen kawata manyan gine-ginensu.
A dukkan zamanai na tarihi, launi ya kasance muhimmin ɓangare na ƙawata gine-gine, kuma ana iya ganinsa kusan a ko'ina.
Misali, launi ya taka muhimmiyar rawa a cikin tagogin gilashi masu launi na majami'un Tsakiyar Zamani. Haka kuma ya kasance cikin zanen rufi da bangon gine-gine da aka kawata da fitattun zane-zanen fresco na zamanin Renaissance a Italiya.
Bugu da ƙari, launi ya zama wani ginshiƙi mai muhimmanci a gine-ginen zamani masu fuska masu haske da walƙiya na ƙarni na 20 da na 21. Daga cikin misalan akwai ƙofar tagwaye ta Cibiyar Pompidou da ke birnin Malaga, wadda Daniel Buren ya tsara, kuma ya shahara saboda yadda yake amfani da launi da haske ta hanya ta musamman.
Mai zanen gine-gine Adam Nathaniel Furman da marubuciya Kate Mazade sun bayyana a cikin littafinsu mai suna Chromatic Architecture: The Craft of Colour in Design cewa launi "wani muhimmin abu ne da ke ƙawata gini, yana ƙara masa jan hankali tare da ba da farin ciki ta hanyar da babu irinta."
Waɗannan gine-gine guda takwas suna nuna a sarari yadda launi zai iya sauya kamanni da kuma yanayin da gini ke haifarwa, tare da ƙarfafa masu zana gine-gine su riƙa amfani da launuka cikin ƙarfin gwiwa a ayyukansu.
1. Wajen Ibada na Sri Ranganatha Swamy da ke jihar Tamil Nadu a Indiya

Asalin hoton, Rupesh Maurya/ Creative Commons
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wajen ibada na Sri Ranganatha Swamy da ke jihar Tamil Nadu na ɗaya daga cikin fitattun gine-ginen addinin Hindu a ƙasar Indiya.
Haɗuwar launuka masu haske kamar shuɗi, kore, rawaya, ja mai walƙiya da kuma ruwan dorawa ya sa wajen ibadar ya zama kyakkyawan misali na yadda ake amfani da launi wajen nuna al'adu, addini da kuma asalin yankin.
Saboda kamanninsa masu jan hankali, wurin ya zama ɗaya daga cikin sanannun alamomin gine-ginen Hindu a duniya.
An fara gina shi Sri Ranganatha Swamy tun kusan ƙarni na farko kafin haihuwar Annabi Isa (A.S.), kuma gwamnatoci da masarautu daban-daban sun ci gaba da faɗaɗa shi tsawon ƙarnuka har zuwa ƙarshen ƙarni na 20.
A yau, yana daga cikin mafi girman gine-ginen addini a duniya, inda yake mamaye fili mai faɗin fiye da hekta 60.
Wurin bautar yana kewaye da manyan ƙofofi 21 da ake kira gopuram, waɗanda aka kawata da ɗaruruwan mutum-mutumai masu launuka masu haske da kayatarwa. Waɗannan sassaƙaƙƙun abubuwan ado masu girma uku sun sa haikalin ya zama ɗaya daga cikin fitattun misalai na gine-ginen gargajiyar Hindu.
2. Fadar Kiɗa ta Catalonia Barcelona, Spain.

Asalin hoton, Consuelo Borroni/ Pexels
Kyakkyawan zauren kide-kide na Palau de la Música Catalana, wanda aka gina a shekarar 1908, ya zama alamar da ke nuna asali da martabar yankin Catalonia, wani yanki na ƙasar Spain mai cike da al'adu masu ɗimbin yawa da tarihin ci gaban masana'antu.
Wanda ya tsara wannan gini, Lluís Domènech i Montaner, ya haɗa salailai daban-daban na gine-gine, ciki har da Art Nouveau, Romanesque da Neo-Gothic, tare da tasirin salon Mudéjar da kuma al'adun yankin Valencia.
A cewar Geoffrey Furman, ƙwararre a tarihin gine-gine, kowane sashe na Palau de la Música yana ɗauke da alamu da siffofi da ke sa ginin ya yi kama da wani wuri na musamman mai ban sha'awa, tamkar wurin da labaran tatsuniyoyi ke faruwa.
Furman ya ce: "Dukkan duwatsun ginin, ginshiƙai, kusurwoyi da kyawawan abubuwan adonsa an kawata su da launuka da zane-zane masu jan hankali, waɗanda suke kama da masu rai kuma suna aiki tare cikin ban mamaki."
3.Ginin Guardian da ke birnin Detroit a jihar Michigan, Amurka.

Asalin hoton, Guardian Building
Wannan ginin ofisoshi, wanda aka kammala a shekarar 1929 kuma Wirt C. Rowland ya tsara shi, mazauna yankin sun ba shi laƙabin "Cathedral of Finance" (Babban Coci na Kuɗi) saboda kyawunsa, salon gine-ginensa mai kayatarwa da kuma muhimmancinsa a tarihi.
Haka nan ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin muhimman gine-ginen salon Art Deco a duniya.
Da yake magana da BBC, Kate Mazade ya ce Rowland ya yi amfani da launuka ne domin nuna ƙwarewa da fasahar ƙwararrun masu sana'a daga yankin Great Lakes na Amurka a farkon ƙarni na 20.
An rufe bangaren waje na ginin da kusan tubalan bulo ja miliyan biyu da aka yi daga yumɓun da aka gasa, masu ɗan launin ruwan lemu, waɗanda suka ba ginin wani salo na musamman da ake iya gane shi cikin sauƙi.
A cikin ginin kuwa, babban zauren yana da rufi mai ƙunshe da bakuna uku masu jere a saman juna, kuma an yi masa ado da tayal masu launuka na asali waɗanda aka shirya cikin wani tsari mai kama da bargon faci-faci.
Mazade ya ƙara da cewa: "Wannan gini ya kasance alamar manyan nasarorin kasuwanci da birnin Detroit ya samu a wancan lokaci, kuma har yanzu yana ci gaba da zama wata rayayyar tunawa da wadata da bunƙasar da aka more a lokacin."
4.Shagon De Bijenkorf da ke Eindhoven, Netherlands

Asalin hoton, Getty Images
Haka kuma, fitaccen ɗan Italiya mai fasahar gine-gine da ƙira, Gio Ponti, ya samo tunanin wannan gini ne a shekarar 1969 daga kallon filayen noma masu kore na ƙasar Holland waɗanda suka yi kama da tsarin shatale-tale, yayin da yake cikin jirgin sama.
Ba wa wani babban gini marar tagogi kamanni na musamman da jan hankali babban ƙalubale ne ga masu zanen gine-gine da yawa. Amma ga Ponti, hakan bai kasance matsala ba, domin ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagororin gine-ginen zamani tare da fitattun mutane irin su Le Corbusier da Mies van der Rohe.
A cewar Geoffrey Furman, Ponti ya mayar da ginin zuwa wani "babban hoto mai kayatarwa, mai hasken koren emerald", wanda ya sha bamban gaba ɗaya da sauran gine-ginen da ake da su a wancan lokaci.
Ta haka ne ya sauya fuskokin siminti marasa armashi da suka yi yawa a lokacin zuwa wani babban aikin fasaha na zamani mai inganci, wanda ya ba birnin sabon salo da kyan gani.
5.Gidajen Hayar Reversible Destiny Lofts, Tokyo, Japan

Asalin hoton, Reversible Destiny Foundation
Wannan rukunin gidajen haya da aka gina a shekarar 2005, an ƙirƙire shi ne domin girmama Helen Keller, marubuciya kuma mai rajin kare haƙƙin masu nakasa daga Amurka.
Littafin ya bayyana cewa gidaje tara na nau'in loft, waɗanda Shusaku Arakawa da Madeline Gins suka tsara, sun ƙunshi wani salo na musamman na zamani da ya haɗa siffofi daban-daban kamar silinda, murabba'ai masu tsawo, ƙwallaye da sauran sassa na gine-gine masu launuka masu matuƙar haske.
An haɗa waɗannan abubuwa ne domin samar da wani muhalli na rayuwa na musamman, wanda ya bambanta da na al'ada. A wajen, kusan kowane bangon gida da kowane kayan ɗaki suna cike da kuzari da armashi sakamakon amfani da launuka masu ƙarfi da iri-iri.
Mai fasaha Arakawa da mawaƙiya Gins sun yi niyyar fitar da mazauna gidajen daga yanayin jin daɗi da kwanciyar hankali na yau da kullum, tare da sa su fuskanci sabbin abubuwa ta hanyar yadda suka yi amfani da launuka da tsarin gine-ginen.
Mazade ya bayyana cewa: "Sun yi imanin cewa idan muhalli zai iya fitar da mutane daga rayuwar zaman-kansu marar motsi, ya kuma ba su sabon kuzari, hakan zai iya taimaka musu su rayu tsawon lokaci."
Saboda haka, sun haɗa benaye masu siffar raƙuman ruwa da dakuna masu kama da ƙwallaye, sannan suka kawata su da haɗaɗɗun launuka masu tayar da farin ciki da kuzari. A cewar Mazade, dukkan waɗannan tsare-tsaren an yi su ne da nufin inganta rayuwa da jin daɗin mutanen da ke zaune a wurin.
6. Tashar Kona Shara ta Maishima, Osaka, Japa

Asalin hoton, Corporación HU-NET, Osaka
Fitaccen mai fasaha kuma mai zanen gine-gine ɗan Austria, Friedensreich Hundertwasser, ya rasu a shekarar 2000, shekara guda kafin a kammala wannan gini.
Littafin ya bayyana cewa Hundertwasser ya shahara wajen adawa da salon gine-ginen zamani (modernism) wanda ke fifita gine-gine masu fuska madaidaiciya da kamanni iri ɗaya. Maimakon haka, ya yi imanin cewa gine-gine ya kamata su yi kama da halittu masu rai waɗanda ke ci gaba da girma da sauyawa, maimakon su kasance kamar injuna da aka ƙera don yin aiki guda ɗaya kawai.
A wurin Hundertwasser, wannan falsafar ta shafi kowane irin gini, tun daga gidajen zama har zuwa gine-ginen masana'antu.
Ana kwatanta Tashar Maishima da wani katafaren fada na tatsuniya, har ta kai ga cewa mutane da dama suna kuskuren ɗaukarta a matsayin wani ɓangare na filin nishaɗi da ke kusa da ita.
Layuka masu launin rawaya waɗanda ke kama da na zane da hannu suna bayyana tamkar suna gangarowa daga ƙasan ginin, yayin da doguwar hasumiyarsa mai zagaye take ɗauke da irin waɗannan layuka masu launin shunayya.
Dukkan gine-ginen da ke cikin harabar wurin, har da waɗanda aka gina da wasu sassa masu fito da ginshiƙai zuwa waje, suna kan gajerun ginshiƙai masu zagaye waɗanda aka ƙawata da tayal masu launuka iri-iri.
A cewar marubuciya Kate Mazade, kowane sashe na wannan gini alama ce ta ƙin bin ƙa'idojin gargajiya na zayyana gine-gine.
Mazade ta ce: "Masana'antar sarrafa shara mai bututun hayaƙi mai launin kore-shuɗi, bangon da aka ƙawata da siffofi masu murabba'i da layukan rawaya da ja masu haske; me zai fi wannan tawaye ga ƙa'idojin gine-gine?"
7. Maktabar Leganés, Spain

Asalin hoton, Roland Halbe
Wannan ɗakin karatu na jama'a da cibiyar adana takardun hukuma ta ƙaramar hukuma, wanda aka gina a shekarar 2019 kuma kamfanin BN Asociados Arquitectos ya tsara shi, an ƙirƙire shi ne domin ya bayyana a fili abin da yake ɗauke da shi a cikinsa.
Fuskarsa ta waje mai kama da raƙuman ruwa, wadda aka lulluɓe da manyan tayal masu launukan pastel, tana daidaita da tsarin ginin kuma tana samar da wani kallo mai kama da jerin littattafan da aka shirya a kan ɗakunan ajiya. Manufar wannan ƙira ita ce nuna yawan littattafai da nau'o'in ilimin da ke cikin ɗakin karatun.
Bugu da ƙari, ginin ya zama wata muhimmiyar alamar al'adu a yankin, kasancewarsa a wata sabuwar unguwa a Madrid wadda a baya ba ta da wani gini mai jan hankali da irin wannan matsayi.
Mazade ya bayyana cewa"Yayin da hasken rana ke sauyawa kuma yana haskaka fuskar ginin mai tayal masu siffar raƙuman ruwa, launukan pastel ɗinsa masu natsuwa da kuma kamanninsa marar walƙiya suna haifar da wani yanayi mai kama da takarda.
8. Ginin Colonnade na Croydon, London, Birtaniya

Asalin hoton, Gareth Gardner
Wannan hanyar masu tafiya a ƙasa mai tsawon mita 50 da ke Croydon a Birtaniya, an gina ta ne a shekarar 2003, kuma Adam Nathaniel Furman ne ya tsara ta. An ƙirƙire ta da nufin kawo wani zane mai jan hankali zuwa wani yanki da ba a san shi da gine-ginen da ke da siffofi na musamman ba.
Tsarin ginin ya ƙunshi manyan ginshiƙai 16 da kuma katanga biyu masu faɗi, waɗanda aka rufe gaba ɗayansu da dubban tayal masu siffar alwatika da aka ƙera da hannu.
An yi wa kowane tayal rufi na musamman mai sheƙi wanda ke mayar da haske, tare da launuka masu zurfi da armashi. Ƙasan ginin yana da wani duhun shuɗi mai kama da zurfin teku, yayin da launin ke canzawa a hankali zuwa fari mai kama da kirim a sama.
Manufar wannan aikin ita ce kawo wasu daga cikin launuka da salon ƙira da aka yi amfani da su a lokuta da wurare daban-daban na duniya zuwa tashar jirgin ƙasa ta East Croydon.
Adam Nathaniel Furman ya bayyana cewa"Waɗannan launukan suna kewaye da mutumin da ke wucewa, suna jefa shi cikin wani yanayi mai yalwar armashi da ƙwarewar gani. Suna tunatar da dubban shekaru na amfani da shuɗi da farin tayal a manyan gine-ginen duniya, tun daga tsohuwar Masar, Portugal, Turkiyya, Iran na zamanin Safawiyawa, Babila da sauran wurare masu yawa."
Ana sa ran za a wallafa littafin Chromatic Architecture: The Craft of Colour in Design, wanda Adam Nathaniel Furman da Kate Mazade suka rubuta, a ranar 1 ga Satumbar 2026.





























