Tarihi huɗu da aka kafa a zaɓen tsakiyar wa'adin Amurka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da sakamakon zaɓen ya riƙa bayyana tun a jiya, jam'iyyar hamayya ta Demokrats ta kama hanyar ƙwace rinjayen majalisar dattawa da ta wakilan ƙasar.

Jam'iyyar Republican ta Shugaba Trump ta gamu da babban koma baya inda ta sha gagarumin kaye a zaɓukan tsakiyar wa'adi a ƙasar ta Amurka.

Kafin wannan zaɓen dai jam'iyyar Republican ce ke da rinjaye a duka majalisun biyu.

Kuma tuni masu nazarin siyasar ƙasar suka yi hasashen Demokrats za ta ƙwace iko da majalisar wakilai, amma ba a yi zaton za ta ƙwace iko a majalisar dattawa ba.

To sai dai wannan zaɓen ya kuma zo da wani abin mamaki na tarihi da aka kafa a ƙasar. A jihohi huɗu, an samu wasu muhimman nasarori da ba a taɓa ganin irinsu ba a baya:

Abdul El-Sayed

Abdul El-Sayed ya kafa tarihin zama Musulmi na farko da aka zaɓa zuwa Majalisar Dattawan Amurka.

Ɗan gida masu ci rani ne daga ƙasar Masar, ɗan jam'iyyar Democrat mai shekara 42 ya lashe zaɓen kujerar Majalisar Dattawa a jihar Michigan, duk da cewa ya fuskanci kalaman ƙiyayya ga Musulunci a lokacin yakin neman zaɓensa.

El-Sayed, wanda likita ne wanda bai taɓa riƙe muƙamin siyasa ba na a tsakiyar wani yaƙin neman zabe wanda ya haifar da rarrabuwar kawuna saboda bambancin launin fata.

Al'amura sun ƙara dagulewa ne a ranar ƙarshe ta yakin neman zaɓe, bayan da abokiyar karawarsa a zaɓen fitar da gwani a jam'iyyar Democrat, Haley Stevens, wadda ya kayar da bambancin ƙuri'u kalilan, ta ayyana goyon bayanta ga dan takarar jam'iyyar Republican, Mike Rogers.

A ranar Lahadi El-Sayed ya mayar da martani game da hakan a lokacin fira da 'yan jarida da cewa: "Wannan jiha ce mai kunshe da mutane miliyan 10 wadanda suka cancanci mulki mai inganci daga gwamnati. Na fi mayar da hankali kan sauran mutane miliyan 9,999,998 wadanda ba a kansu kuke magana ba."

Wanda aka haifa a shekarar 1984 a unguwar Rochester Hills da ke gefen birnin Detroit ya taso ne a hannun mahaifinsa da matar mahaifin nasa Jacqueline Johnson, bayan da auren iyayensa ya mutu lokacin yana dan shekara uku.

Ya yi karatun likitanci a jami'ar Michigan da kuma jami'ar Columbia University, inda ya kware a harkar cutuka masu saurin yaduwa.

Nadin da aka yi masa a matsayin shugaban sashen lafiya na jihar Detroit a shekarar 2015 ya sa sunansa ya bazu a sassan Amurka.

Keisha Lance Bottoms mace baƙar fata ta farko da aka zaɓa gwamnan jiha a Amurka

'Yar takarar jam'iyyar Democrat, Keisha Lance Bottoms, ta samu nasara a zaɓen gwamnan jihar Georgia da ke Amurka, inda ta doke abokin hamayyarta na jam'iyyar Republican, Rick Jackson. Wannan nasara ta sanya ta zama mace ba'amurkiya ta farko mai baƙar fata da aka zaɓa a matsayin gwamnan wata jiha a tarihin Amurka.

Bottoms, wadda ta taɓa zama magajiyar garin Atlanta daga shekarar 2018 zuwa 2022, za ta kuma zama mace ta farko da ta taɓa riƙe kujerar gwamnan Georgia. Za ta gaji gwamna mai barin gado, Brian Kemp, wanda dokar jihar ta hana sake tsayawa takara bayan ya kammala wa'adinsa biyu.

Nasarar ta ta zo ne duk da gagarumin ƙarfin kuɗin da abokin hamayyarta, Rick Jackson, ya yi amfani da shi wajen yaƙin neman zaɓe. Jackson, hamshaƙin attajiri kuma ɗan kasuwa a fannin kiwon lafiya, ya kashe sama da dala miliyan 200 daga dukiyarsa wajen yaƙin neman zaɓen.

A lokacin yaƙin neman zaɓe, Bottoms ta mayar da hankali kan inganta tattalin arzikin jama'a, faɗaɗa damar samun inshorar lafiya, ƙara mafi ƙarancin albashi da kuma kare haƙƙin masu kaɗa ƙuri'a. Ta kuma sha suka kan manufofin gwamnatin Shugaba Donald Trump.

Wannan nasara ta kawo ƙarshen sama da shekaru 20 da jam'iyyar Republican ta shafe tana riƙe da kujerar gwamnan Georgia. Haka kuma, ta zama wani babban tarihi ga mata baƙaƙen fata a siyasar Amurka, waɗanda suka daɗe suna fafutukar samun wakilci a manyan muƙaman siyasar ƙasar.

Chris Pappas ɗan luwaɗi na farko da aka zaɓa Sanata a tarihin Amurka

Chris Pappas, ɗan takarar jam'iyyar Democrat daga jihar New Hampshire, ya kafa tarihi bayan lashe zaɓen kujerar Sanata a Majalisar Dokokin Amurka, inda ya doke ɗan takarar jam'iyyar Republican, John E. Sununu. Nasarar tasa ta sanya shi zama ɗan luwaɗi na farko da ya fito fili ya bayyana kansa a matsayin mai sha'awar jinsi ɗaya da aka zaɓa zuwa Majalisar Dattawan Amurka.

BostonGlobe.com

Pappas, mai shekaru 46, ɗan majalisar wakilai ne mai wakiltar New Hampshire tun shekarar 2019. Ya yi amfani da gogewarsa a siyasa wajen neman goyon bayan masu zaɓe, inda ya jaddada buƙatar rage tsadar rayuwa da kuma kare muradun al'ummar jihar.

Abokin hamayyarsa, John Sununu, tsohon Sanata ne da ya taɓa wakiltar jihar New Hampshire a majalisar daga shekarar 2003 zuwa 2009. Ya amince da shan kaye bayan sakamakon farko ya nuna Pappas na kan gaba.

A yayin jawabin godiya ga magoya bayansa, Pappas ya gode wa mijinsa, Vann Bentley, bisa goyon bayan da yake ba shi. Ya kuma bayyana farin cikinsa da yadda al'ummar New Hampshire suka amince da shi duk da kasancewarsa ɗan luwaɗi.

Ana kallon nasarar Pappas a matsayin wani sabon tarihi ga wakilcin al'ummar LGBTQ a manyan hukumomin siyasar Amurka, musamman kasancewar babu wani namiji da ya fito fili ya bayyana kansa a matsayin ɗan luwaɗi da aka taɓa zaɓa zuwa Majalisar Dattawan ƙasar kafin shi.

Deb Haaland Ba'amurkiya ta farko da aka zaɓa gwamna a Amurka

'Yar takarar jam'iyyar Democrat, Deb Haaland, ta lashe zaɓen gwamnan jihar New Mexico da ke Amurka, inda ta doke abokin hamayyarta na jam'iyyar Republican, Gregg Hull. Nasarar ta sanya ta zama mace ta farko 'yar asalin ƙasar Amurka da aka zaɓa a matsayin gwamnan wata jiha a tarihin ƙasar.

Haaland, mai shekaru 65, 'yar ƙabilar Laguna Pueblo ce. Ta taɓa zama 'yar majalisar wakilan Amurka, kafin tsohon shugaban ƙasar Joe Biden ya naɗa ta sakatariyar harkokin cikin gida daga shekarar 2021 zuwa 2025. Hakan ya kuma sanya ta zama Ba'amurkiya ta farko 'yar asalin ƙasar da ta riƙe muƙamin minista a gwamnatin Amurka.

A yayin yaƙin neman zaɓenta, Haaland ta mayar da hankali kan inganta rayuwar al'ummar jihar, kare muhalli da albarkatun ruwa, da kuma samar da ingantattun tsare-tsaren jin daɗin jama'a. Ta kuma yi alƙawarin inganta harkokin kiwon lafiya da kula da yara.

Ta doke Gregg Hull, tsohon magajin garin Rio Rancho, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam'iyyar Republican. Rahotannin sakamakon zaɓen farko sun nuna cewa Haaland ta samu kusan kashi 57 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da Hull ya samu kusan kashi 43 cikin 100.

Nasarar Haaland ta zama wani muhimmin tarihi ga 'yan asalin ƙasar Amurka, musamman mata, wajen samun wakilci a manyan muƙaman siyasar ƙasar. Za ta gaji gwamna Michelle Lujan Grisham, wadda wa'adin mulkinta ya zo ƙarshe.